Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Sunday, 7 February 2016

MATSAYIN SAHABBAN MANZON ALLAH (SAW) A CIKIN AL- QUR'ANI KASHI NA (3)


**DUKKAN SAHABBAI ALLAH YA YARDA DA SU, KUMA YA YI MUSU TANADIN ALJANNA**

ALLAH YA CE:
{وَالسَّابِقُونَ الْأَوَّلُونَ مِنَ الْمُهَاجِرِينَ وَالْأَنْصَارِ وَالَّذِينَ اتَّبَعُوهُمْ بِإِحْسَانٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ وَأَعَدَّ لَهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي تَحْتَهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا ذَلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ } [التوبة: 100]

"WA'DANDA SUKA RIGA IMANI DA SHIGA MUSLUNCI NA FARKO, A MAHAJIRUNA DA ANSAR (MUTANEN MADINA), DA WA'DANDA SUKA BISU DA KYAUTATAWA, ALLAH YA YARDA DA SU, KUMA SUN YARDA DA SHI, KUMA YA TANADA MUSU ALJANNAI, RAFUKA SUNA GUDANA A K'ARK'ASHINSU, ZA SU DAUWAMA A CIKINSU HAR ABADA, WANNAN RABO NE MAI GIRMA".

MAGANA A KAN WANNAR AYAR ZA TA KASANCE NE TA FISKOKI GUDA HU'DU (4):
1. SU WANENE WA'DANDA SUKA RIGA IMANI DA SHIGA MUSLUNCI NA FARKO?
2. SU WANENE WA'DANDA SUKA BISU DA KYAUTATAWA?
3. ALLAH YA YARDA DA SU.
4. ALLAH YA TANADA MUSU ALJANNAI, RAFUKA SUNA GUDANA A K'ARK'ASHINSU, ZA SU DAUWAMA A CIKINSU HAR ABADA.

FISKA TA FARKO: AKWAI MAGANGANUN MALAMAN TAFSIRI GUDA SHIDA (6) A KAN MA'ANAR:
{وَالسَّابِقُونَ الْأَوَّلُونَ }

IBNUL JAUZIY (R) YA CE:
قوله تعالى: والسابقون الأولون فيهم ستة أقوال: أحدها: أنهم الذين صلوا إلى القبلتين مع رسول الله صلى الله عليه وسلم، قاله أبو موسى الأشعري، وسعيد بن المسيب، وابن سيرين، وقتادة.
والثاني: أنهم الذين بايعوا رسول الله صلى الله عليه وسلم بيعة الرضوان، وهي الحديبية، قاله الشعبي.
والثالث: أنهم أهل بدر، قاله عطاء بن أبي رباح.
والرابع: أنهم جميع أصحاب رسول الله صلى الله عليه وسلم، حصل لهم السبق بصحبته. قال محمد بن كعب القرظي: إن الله قد غفر لجميع أصحاب النبي صلى الله عليه وسلم وأوجب لهم الجنة محسنهم ومسيئهم في قوله تعالى: والسابقون الأولون.
والخامس: أنهم السابقون بالموت والشهادة، سبقوا إلى ثواب الله تعالى. ذكره الماوردي.
والسادس: أنهم الذين أسلموا قبل الهجرة، ذكره القاضي أبو يعلى.
زاد المسير في علم التفسير (2/ 291 - 292)

(1) SU NE WA'DANDA SUKA FISKANCI ALKIBLA GUDA BIYU (2).
(2) SU NE WA'DANDA SUKA YI MUBAYA'A A HUDAIBIYYA.
(3) SU NE 'YAN YAK'IN BADAR.
(4) SU NE DUKKAN SAHABBAI, SABODA SUN RIGA SAURAN AL'UMMA GABA 'DAYA YIN IMANI DA SHIGA MUSLUNCI.
(5) SU NE WA'DANDA SUKA RIGA RASUWA, SUKA SAMU SHAHADA.
(6) SU NE WA'DANDA SUKA MUSLUNTA KAFIN HIJIRA.

AL- WAHIDIY (R) YA CE:
وقد فسرت الآية على أن المراد بها جميع الصحابة الذين أدركوا رسول الله صلى الله عليه وسلم، وحصل لهم السبق بإدراكه وصحبته. وذلك ما أخبرنا أبو بكر أحمد بن محمد التميمي، أنا عبد الله بن محمد بن جعفر بن حيان، نا الوليد بن أبان، نا الفضل بن حماد، نا عبد الله بن صالح، حدثني خالد بن حميد، عن أبي صخر حميد بن زياد، قال: قلت لمحمد بن كعب القرظي يوما: ألا تخبرني عن أصحاب رسول الله صلى الله عليه وسلم فيما كان من رأيهم؟ وإنما أريد الفتن.
فقال: إن الله قد غفر لجميع أصحاب النبي صلى الله عليه وسلم، وأوجب لهم الجنة في كتابه، محسنهم، ومسيئهم.
قلت: في أي موضع أوجب لهم الجنة في كتابه؟ فقال: سبحان الله، ألا تقرأ قوله تعالى: والسابقون الأولون إلى آخر الآية، فأوجب الله لجميع أصحاب النبي صلى الله عليه وسلم الجنة والرضوان، وشرط على التابعين شرطا لم يشترطه عليهم.
قلت: وما اشترط عليهم؟ قال: اشترط عليهم أن يتبعوهم بإحسان، يقول: يقتدون بأعمالهم الحسنة ولا يقتدون بهم في غير ذلك.
قال أبو صخر: فوالله لكأني لم اقرأها قط، وما عرفت تفسيرها حتى قرأ علي محمد بن كعب.
التفسير الوسيط للواحدي (2/ 520)

"HAK'IK'A AN FASSARA AYAR DA CEWA; ABIN DA AKE NUFI DA ITA SHI NE; DUKKAN SAHABBAI WA'DANDA SUKA RISKI MANZON ALLAH (SAW), SUKA RIGA KOWA TA HANYAR HA'DUWA DA SHI, DA ZAMOWA SAHABBANASA…".

FISKA TA BIYU: HAKA AKWAI FASSARAR MALAMAI GUDA BIYU (2) A KAN FADIN ALLAH:
{ وَالَّذِينَ اتَّبَعُوهُمْ بِإِحْسَانٍ }

ABUL MUZHAFFAR AL- SAM'ANIY (R) YA CE:
وأما قوله: {والذين اتبعوهم بإحسان} فيه قولان: أحدهما: أنهم بقية المهاجرين والأنصار سوى السابقين الأولين منهم.
والقول الثاني: أنهم المؤمنون إلى قيام الساعة.
وقال عطاء: يريد: يذكرون المهاجرين والأنصار بالجنة والرحمة والدعاء لهم، ويذكرون محاسنهم.
تفسير السمعاني (2/ 342)، تفسير البغوي - طيبة (4/ 88)، التفسير الوسيط للواحدي (2/ 521)

AKWAI MAGANA GUDA BIYU (2) A MA'ANAR AYAR:
1- SU NE SAURAN SAHABBAI BAYAN NA FARKO.
2- SU NE SAURAN MUMINAI NA CIKIN WANNANR AL'UMMA HAR ZUWA TASHIN QIYAMA, WA'DANDA SUKE AMBATON SAHABBAI DA ALHERI, SUKE YI MUSU ADDU'A DA NEMAN RAHAMA.

A BISA WANNAN BAYANI DA YA GABATA, TA KOWACE FISKA KA 'DAUKI WANNAR AYAR ZA KA SAMU TANA BAYANIN MATSAYIN DUKKAN SAHABBAN ANNABI (SAW) A WAJEN ALLAH; IN KA 'DAUKI FASSARA:
{وَالسَّابِقُونَ الْأَوَّلُونَ }

DA CEWA; SU NE:
(1) WA'DANDA SUKA FISKANCI ALKIBLA GUDA BIYU (2).
(2) KO SU NE WA'DANDA SUKA YI MUBAYA'A A HUDAIBIYYA.
(3) KO SU NE 'YAN YAK'IN BADAR.
(4) KO SU NE WA'DANDA SUKA RIGA RASUWA, SUKA SAMU SHAHADA.
(5) KO SU NE WA'DANDA SUKA MUSLUNTA KAFIN HIJIRA.

TO SAI MA'ANAR:
{ وَالَّذِينَ اتَّبَعُوهُمْ بِإِحْسَانٍ }

TA ZAMA CEWA; SU NE SAURAN SAHABBAI WA'DANDA SUKA BIYO BAYAN NA FARKO.
DON HAKA SAI LAMARIN YA ZAMA CEWA; AYAR GABA 'DAYANTA TA TAK'AITA CE A KAN SAHABBAI GABA 'DAYANSU KAWAI.

IN KUMA KA 'DAUKI MA'ANAR:
{وَالسَّابِقُونَ الْأَوَّلُونَ }

A BISA FASSARA TA HUDU (4):
والرابع: أنهم جميع أصحاب رسول الله صلى الله عليه وسلم، حصل لهم السبق بصحبته. قال محمد بن كعب القرظي: إن الله قد غفر لجميع أصحاب النبي صلى الله عليه وسلم وأوجب لهم الجنة محسنهم ومسيئهم في قوله تعالى: والسابقون الأولون.

WATO SU NE DUKKAN SAHABBAI MUHAJIRAI DA ANSAR GABA 'DAYA, SABODA SUN RIGA SAURAN AL'UMMA GABA 'DAYA YIN IMANI DA SHIGA MUSLUNCI, TO SAI MA'ANAR:
{ وَالَّذِينَ اتَّبَعُوهُمْ بِإِحْسَانٍ }

TA ZAMA CEWA; SU NE SAURAN MUMINAI NA CIKIN WANNAR AL'UMMA HAR ZUWA TASHIN QIYAMA, WA'DANDA SUKE AMBATON SAHABBAI DA ALHERI, SUKE YI MUSU ADDU'A DA NEMAN RAHAMA.

IBNUL JAUZIY (R) YA CE:
قوله تعالى: والذين اتبعوهم بإحسان من قال: إن السابقين جميع الصحابة، جعل هؤلاء تابعي الصحابة، وهم الذين لم يصحبوا رسول الله صلى الله عليه وسلم.
وقد روي عن ابن عباس أنه قال: والذين اتبعوهم باحسان إلى أن تقوم الساعة.
ومن قال: هم المتقدمون من الصحابة، قال: هؤلاء تبعوهم في طريقهم، واقتدوا بهم في أفعالهم، ففضل أولئك بالسبق، وإن كانت الصحبة حاصلة للكل.
زاد المسير في علم التفسير (2/ 292)

AL- SHAUKANIY (R) YA CE:
تكون «من» في قوله من المهاجرين على هذا للتبعيض، وقيل:
إنها للبيان، فيتناول المدح جميع الصحابة، ويكون المراد بالتابعين: من بعدهم من الأمة إلى يوم القيامة.
فتح القدير للشوكاني (2/ 453)

SABODA HAKA, A BISA MA'ANA TA FARKO, DUKKAN SAHABBAI SUN SHIGA CIKIN AYAR, KUMA TA TAK'AITA A KANSU NE KAWAI.
A BISA MA'ANA TA BIYU KUMA, DUKKAN MUMINAI NA CIKIN WANNAR AL'UMMA; SAHABBAI GABA 'DAYANSU, DA NA BAYANSU WA'DANDA SUKA BISU DA KYAUTATAWA, BAN DA WA'DANDA SUKA KAUCE DAGA TAFARKIN SAHABBAI, KUMA SUKE CUTAR DA SU, SUKE KAFIRTASU, SUKE ZAGINSU, SUKE AIBANTASU, SU NE: RAFIDHA 'YAN SHI'A DA NASIBAWA DA SAURAN 'YAN BIDI'A.

SABODA HAKA, HANYAR SAMUN YARDAR ALLAH DA GIDAN ALJANNA ITA CE; BIN SAHABBAN ANNABI (SAW) DA KYAUTATAWA, DA KUMA AMBATONSU DA ALHERI, DA YI MUSU ADDU'AN SAMUN RAHAMAR ALLAH DA GAFARARSA DA YARDARSA.

FISKA TA UKU: ALLAH YA YARDA DA DUKKAN SAHABBAI, A BISA MA'ANA TA FARKO, KO KUMA YA YARDA DA DUKKAN MUMINAI NA CIKIN WANNAR AL'UMMA; SAHABBAI GABA 'DAYANSU, DA NA BAYANSU, WA'DANDA SUKA BISU DA KYAUTATAWA. ALLAH YA YARDA DA SU BA ZAI YI FUSHI DA SU BA, HAKAN YANA LAZIMTA YA YARDA DA AIYUKANSU NA ALHERI KUMA YA KAR'BESU, NA LAIFUKA KUMA YA GAFARTA MUSU.

FISKA TA HU'DU: ALLAH YA TANADI GIDAN ALJANNA MA DUKKAN SAHABBAI DA MABIYANSU DA KYAUTATAWA, ZA SU DAUWAMA A CIKINTA HAR ABADA. SABODA HAKA DUKKAN SAHABBAI 'YAN ALJANNA NE, BABU 'DAN WUTA A CIKINSU.

AHLUS SUNNA NA GASKIYA SU SUKA RABAUTA DA WANNAN RABO MAI GIRMA, SABODA SUNA BIN SAHABBAI, KUMA BA SA AMBATONSU SAI DA ALHERI, SUNA YI MUSU ADDU'AN YARDAR ALLAH DA GAFARA DA RAHAMA. A LOKACIN DA RAFIDHA 'YAN SHI'A DA NASIBAWA SUKA YI HASARAR WANNAN RABO, SABODA SUNA KAFIRTA SAHABBAI SUNA ZAGINSU SUNA TSINE MUSU, DA SAURAN 'YAN BIDI'A DA SUKA BAR TAFARKIN SUNNA, TAFARKIN SAHABBAI, SU MA SUN YI WANNAN HASARAR.

No comments:

Post a Comment