Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Sunday, 7 February 2016

MATSAYIN SAHABBAN MANZON ALLAH (SAW) A CIKIN AL- QUR'ANI KASHI NA (4)


**ALLAH YA YI ALKAWARIN ALJANNA GA DUKKAN SAHABBAI GABA 'DAYANSU**

ALLAH YA CE:
{ لَا يَسْتَوِي مِنْكُمْ مَنْ أَنْفَقَ مِنْ قَبْلِ الْفَتْحِ وَقَاتَلَ أُولَئِكَ أَعْظَمُ دَرَجَةً مِنَ الَّذِينَ أَنْفَقُوا مِنْ بَعْدُ وَقَاتَلُوا وَكُلًّا وَعَدَ اللَّهُ الْحُسْنَى وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ } [الحديد: 10]

"WA'DANDA SUKA CIYAR DA DUKIYOYINSU DAGA CIKINKU, KUMA SUKA YI YAK'I KAFIN BU'DE GARIN MAKKA (KO NASARAR HUDAIBIYYA), WA'DANNAN SU SUKA FI GIRMAN DARAJA FIYE DA WA'DANDA SUKA CIYAR SUKA YI YAK'I DAGA BAYA, AMMA DUKKAN 'BANGARORIN GUDA BIYU (2) ALLAH YA YI MUSU ALKAWARIN ALJANNA, ALLAH MASANI NE GA ABIN DA KUKE AIKATAWA".

MAGANA A KAN WANNAR AYAR ZA TA KASANCE NE TA FISKOKI GUDA BIYU (2):
1- MA'ANAR:
الْفَتْحِ
MALAMAN TAFSIRI SUN AMBACI MA'ANONI GUDA BIYU (2):
(a) SHI NE FATHU MAKKAH, WANNAN SHI NE RA'AYIN MAFI YAWAN MALAMAI.
(b) NASARAR HUDAIBIYYA (FATHUL HUDAIBIYYA).
IBNUL JAUZIY YA CE:
قبل الفتح وفيه قولان: أحدهما: أنه فتح مكة، قاله ابن عباس، والجمهور. والثاني: أنه فتح الحديبية، قاله الشعبي.
زاد المسير في علم التفسير (4/ 233)

WANNAR MA'ANA TA BIYUN ITA IBNU JARIR (R) YA RINJAYAR, INDA YA CE:
وأولى الأقوال في ذلك بالصواب عندي أن يقال: معنى ذلك لا يستوي منكم أيها الناس من أنفق في سبيل الله من قبل فتح الحديبية للذي ذكرنا من الخبر عن رسول الله صلى الله عليه وسلم، الذي رويناه عن أبي سعيد الخدري عنه وقاتل المشركين بمن أنفق بعد ذلك، وقاتل
تفسير الطبري = جامع البيان ط هجر (22/ 395)

YA RINJAYAR DA WANNAR FASSARA CE, DA TA NUNA CEWA; MA'ANAR "FATHU" ITA CE: NASARAR HUDAIBIYYA SABODA HADISIN DA YA RUWAITO DA ISNADINSA KAMAR HAKA:
عن أبي سعيد الخدري قال: قال لنا رسول الله صلى الله عليه وسلم عام الحديبية: «يوشك أن يأتي قوم تحقرون أعمالكم مع أعمالهم» ، قلنا: من هم يا رسول الله، أقريش هم؟ قال: «لا، ولكن أهل اليمن أرق أفئدة وألين قلوبا» ، فقلنا: هم خير منا يا رسول الله؟ فقال: «لو كان لأحدهم جبل من ذهب فأنفقه ما أدرك مد أحدكم ولا نصيفه، ألا إن هذا فصل ما بيننا وبين الناس» ، {لا يستوي منكم من أنفق من قبل الفتح} الآية، إلى قوله: {والله بما تعملون خبير}".
تفسير الطبري = جامع البيان ط هجر (22/ 394)

2- MA'ANAR:
الْحُسْنَى
ITA CE ALJANNA. BABU SABANI A KAN HAKA A TSAKANIN MALAMAN TAFSIRI.
ALBAGWIY (R) YA CE:
{وكلا وعد الله الحسنى} أي كلا الفريقين وعدهم الله الجنة.
تفسير البغوي - طيبة (8/ 34)

"MA'ANA; DUKKAN 'BANGARORIN GUDA BIYU (WA'DANDA SUKA CIYAR, KUMA SUKA YI YAK'I KAFIN FATHU MAKKA (KO NASARAR HUDAIBIYYA), DA WA'DANDA SUKA YI A BAYAN HAKA) ALLAH YA YI MUSU ALKAWARIN ALJANNA".

SABODA HAKA, A BISA KOWACE MA'ANA DAGA CIKIN MA'ANONIN GUDA BIYU (2) NA FATHU; IMMA FATHU MAKKA NE, KO NASARAR HUDAIBIYYA, DUKA AYAR TANA BAYANIN CEWA; DUKKAN SAHABBAI ALLAH YA YI MUSU ALKAWARIN ALJANNA. SABODA WA'DANDA SUKA CIYAR SUKA YI YAK'I KAFIN FATHU MAKKAH (KO HUDAIBIYYA) DA BAYANSA YA HA'DA DUKKAN SAHABBAI.
WANNAN YA NUNA CEWA; A CIKIN SAHABBAI DUKA BABU 'DAN WUTA, SABODA DUK WANDA ALKAWARIN ALJANNA DAGA WAJEN ALLAH TA RIGAYA GARE SHI TO KO MOTSIN WUTAR MA BA ZAI JI BA, BARE YA SHIGETA. ALLAH YA CE:
{ إِنَّ الَّذِينَ سَبَقَتْ لَهُمْ مِنَّا الْحُسْنَى أُولَئِكَ عَنْهَا مُبْعَدُونَ لَا يَسْمَعُونَ حَسِيسَهَا وَهُمْ فِي مَا اشْتَهَتْ أَنْفُسُهُمْ خَالِدُونَ } [الأنبياء: 101 - 102]

DON HAKA SAHABBAI DUKKANSU 'YAN ALJANNA NE, KO DA NASIBAI DA RAFIDHA 'YAN SHI'A BA SA SO.

No comments:

Post a Comment