AKWAI RUWAYOYI MASU YAWA DA MALAMAN SHI'A SUKA RUWAITO A CIKIN LITTATAFANSU WA'DANDA DUK MAI KISHIN ADDININ MUSLUNCI, TARE DA SON ANNABIN RAHAMA (SAW) IN YA JISU BA ZAI JI DA'DIN IRIN WULAK'ANCI DA CIN MUTUNCI DA MALAMAN SHI'AN SUKE YI WA MATSAYIN ANNABI (SAW) BA.
DAGA CIKIN IRIN WA'DANNAN RUWAYOYI A KWAI:
" لولاك لما خلقت الأفلاك ، ولولا علي لما خلقتك ، ولولا فاطمة لما خلقتكما "
الاسرار الفاطمية - الشيخ محمد فاضل المسعودي - (1 / 153)
WAI ALLAH YA CE WA ANNABI (SAW):
"BA DON KAI BA DA BAN HALICCI TAURARI BA, KUMA BA DON ALIYU BA DA BAN HALICCEKA BA, KUMA BA DON FATIMA BA DA BAN HALICCEKU KU BIYUN BA".
KU DUBA KU GA IRIN WANNAN RENI DA CIN ZARAFI WA MATSAYIN ANNABI (SAW), -WAI- ALLAH YA HALICCI ANNABI (SAW) NE DON ALIYU (RA)??!
SA'ANNAN KUMA -WAI- YA HALICCE SHI NE SHI DA ALIYUN (RA) DUKA SABODA FATIMA (RA)?
TO TA YAYA ZAMU FAHIMCI WANNAR MAGANA, DA TA MASU CEWA; AN YI DUNIYA NE DON MANZON ALLAH (SAW), WATO MASU AQIDAR (AL- HAQIQATUL MUHAMMADIYYA), KO (AL- NURUL MUHAMMADIY), KO (AL- INSANUL KAMIL), KO (HAQIQATUL HAQA'IQ)?
TO SU WA ZA MU GASKATA A TSAKANINSU?!
MU DAI ABIN DA MUKA SANI SHI NE; ALLAH YA YI HALITTA NE DON GASKIYA, DON BAYI SU SAN SHI DA SUNAYENSA DA SIFFOFINSA NA KAMALA, DON SU BAUTA MASA SHI KA'DAI.
ALLAH YA CE:
{وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا لَاعِبِينَ (38) مَا خَلَقْنَاهُمَا إِلَّا بِالْحَقِّ وَلَكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ (39) } [الدخان: 38، 39]
"BA MU HALICCI SAMMAI DA K'ASA DA ABIN DA KE TSAKANINSU BA DON WASA, BA MU HALICCESU BA SAI DON GASKIYA, AMMA SAI DAI MAFI YAWAN MUTANE BA SU SANI BA".
KUMA ALLAH YA CE:
{ اللَّهُ الَّذِي خَلَقَ سَبْعَ سَمَاوَاتٍ وَمِنَ الْأَرْضِ مِثْلَهُنَّ يَتَنَزَّلُ الْأَمْرُ بَيْنَهُنَّ لِتَعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ وَأَنَّ اللَّهَ قَدْ أَحَاطَ بِكُلِّ شَيْءٍ عِلْمًا (12) } [الطلاق: 12]
"ALLAH WANDA YA HALICCI SAMMAI GUDA BAKWAI, K'ASA MA YA HALICCI KAMARSU, AL'AMARIN ALLAH YANA SAUK'A A TSAKANINSU, DON KU SAN CEWA: LALLAI ALLAH MAI IKO NE A KAN KOMAI, KUMA LALLAI YA KEWAYE KOMAI A ILMANCE".
KUMA YA CE:
{وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنْسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ (56) } [الذاريات: 56، 57]
"BAN HALICCI ALJANI DA MUTUM BA SAI DON SU BAUTA MINI".
WA'DANNAN AYOYI NA AL- QUR'ANI SU SUKE BAYYANA MANA MANUFAR HALITTAR HALITTA GABA 'DAYA, WATO ALLAH YA HALICCI HALITTA NE DON GASKIYA, GASKIYAR KUWA ITA CE; SANIN ALLAH DA KYAWAWAN SUNAYENSA DA MA'DAUKAKA SIFFOFINSA NA KAMALA, DON BAYINSA; MUTANE DA ALJANU SU BAUTA MASA, SU KA'DAITA SHI DA BAUTA SHI KA'DAI.
WANNAN SHI YAKE NUNA MANA KUSKUREN WA'DANDA SUKE ZATON ALLAH YA YI HALITTA NE DON WANI MUTUM, KOMAI MATSAYINSA KUWA, BABBAN KUSKURE NE KA YI ZATON AN YI HALITTA NE DON MANZON ALLAH (SAW), KO DON ALIYU (RA), KO DON FATIMA (RA), WA'DANNAN AQIDU NE DA SUKA SA'BA MA AL- QUR'ANI MAI GIRMA, LITTAFIN DA AKA SAUK'AR MANA DON MU YI AIKI DA SHI.
No comments:
Post a Comment