Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Monday, 8 February 2016

MATSAYIN JAGORAN SHI'A SAYYID KHAMNA'IY GAME DA BIDI'AR TATTAKI ZUWA ZARIA TA 'YAN SHI'A


FASSARAR TAMBAYA KAN HALASCI KO AKASI NA TATTAKI ZUWA ZARIYA

Daga Ofishin Jagora Sayyed Ali Khamene'i (d.z) ta shafin Whatsapp:

Ga matanin tambaya da larabci:

. السلام عليكم ورحمةالله تعالى وبركاته.بسماحتكم! نحن في نجيريا بعض اخوانناالشيعة يمشون على أقدامهم أكثر من مئةكلومترا رجالا ونساءوالاطفل كسبعةأيام متواجهون الى حسينة مدينة زاريا متمثلون بمشي المستب الى كربلاء بعنوانهم لاحياء اربعينة الامام الحسين(ع) في كل سنة والى الان حتى يتخذونه موسما.
فهل يجوزلنا في ذالك المشي الى هذه الحسينة امتثالا بكربلاء في شريعةالمقدسة? تحت مرجعية سيدالقائد?ادام الله ظله على رؤسنا

Fassara da Hausa:

"Assalamu alaykum

Bisa Alhurmarku!, Mu a Najeriya mu ke amma akwai wasu 'yan uwanmu 'Yan Shi'a da suke Tattaki da 'kafarsu fiye da Km100 Maza da Mata da 'kananan yara tafiyar kamar ta Kwanaki 7 haka suna nufin zuwa wata Hussainiya a Birnin Zariya don su misalta Tattakin Mustahabbi da a ke yi zuwa Karbala kuma sunayi ne da nufin raya Arba'indin Imamul Hussaini (a.s). Haka suke yi kowace shekara; to zuwa yanzu har sun dauke shi Mausim. (Wato aikin da ake yi na 'Ka'ida ta al'ada a zagayowan Shekara kamar Idi ko Hajji a misali). To Shin hakan ya halatta mana mu yi irin wanna Tattakin zuwa wannan Husainyyar don misalta na Karbala a Shari'a tsarkakakkiya a karkashin Fatawar Jagora Sayyidul Ka'id?

Muna Fata Allah ya Dauwamar da inuwarsa a kan Kayuwanmu Ma'ana (Allah yaja kwanansa tare damu)".

FASSARAR AMSAR JAGORA SAYYIDUL 'KA'ID AL KHAMENA'I:

السلام عليكم ورحمة الله وبركاته. لم يثبت استحباب هذا العمل

FASSARA:

"Irin wannan aikin Mustahabbancinsa bai tabbata ba".

To ga mai neman 'karin bayani zuwa Ofishin na jagora to ga Lambar WhatsApp dinda aka aiko min ta nan kuma din nayi Tambayar.+989368070097.

A WANNAN HOTO NA KASA KUWA, AYATLLAHI SAFIY NE YAKE CEWA; TATTAKIN ZUWA ZARIA BAI HALASTA BA.

No comments:

Post a Comment