Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Monday, 8 February 2016

BA NI NA KAR ZOMON BA RATAYA AKA BA NI

RAFIDHA 'YAN SHI'A BA SU DA ADALCI.
AN YI TURMUTSITSI A MINA, A LOKACIN AIKIN HAJJIN BANA, TUN A RANAR DA ABIN YA FARU, BABU WANI BINCIKE DA AKA FARA YI, AMMA SAI GOMNATIN IRAN (KASAR 'YAN SHI'A) SUKA FITO SUKA DORA LAIFIN ABIN DA YA FARU A KAN KASAR SUNNA SAUDIYYA.

TO A YAU KUMA, ALLAH YA BA NI DAMA NA KWARMATO WANI RAHOTO NA SIRRI MAI HADARI A KAN AYATULLAHI KHAMNA'IY DA GOMNATINSA TA IRAN, WANDA YAKE TABBATAR DA CEWA; GOMNATIN IRAN CE TA SHIRYA WANNAN HATSARI DA YA FARU A MINA, A MATSAYIN AIKIN TA'ADDANCI, A KARKASHIN JAGORANCIN JAGORAN SHI'A NA DUNIYA AYATULLAHI ALIY KHAMNA'IY DA KUNGIYARSA TA TSAGERUN 'YAN SHI'A, WATO KUNGIYAR "AL- HARSUL THAURIY".

TO ABIN MAMAKI, BAYAN FITOWAN WANNAN RAHOTO ME YA KAMATA 'YAN SHI'A SU YI??

NI A FAHIMTATA, KAMATA YA YI SU KOMA SU YI BINCIKE, SABODA BA DA KA MUKA FADI ABIN DA MUKA FADA BA. MUN AMBACI WANDA MAGANAR TA FITO DAGA WAJENSA, WATO SHI NE TSOHON BABBAN JAMI'IN HARKOKIN JEKADANCIN IRAN, WANDA YA YI AIKINSA NA KARSHE A OFISHIN JEKADANCIN IRAN A KASAR BELGIUM, MAI SUNA "FARZAD FARHNKIN". DON HAKA SAI 'YAN SHI'A SU JE SU BINCIKE SHI DON SU TABBATAR DA IN KARYA YA YI MUSU. AMMA MU KAM BA ZA MU KARYATA SHI BA, SABODA KUSACIN INDA YA SAMO LABARIN DA AYATULLAHI KHAMNA'IY, KUMA DON MUN TABBATAR DA CEWA; GOMNATIN AYATULLAHI KHAMNA'IY WACCE GOMNATIN IRAN TAKE KARKASHINSA ZA TA IYA YIN FIYE DA HAKA. TARIHI NE YAKE MAIMAITA KANSA.

HABA JAMA'A!!
INA ADALCI YAKE A NAN?!

AN ZO AN YADA MUKU WANI FAIFAN VIDEO DA KOWA YA GANI YA SAN SHARRI NE, SABODA RASHIN DACEWARSA DA WAJEN JIFA DA KUMA RANAR DA ABIN YA FARU, WATO RANAR JIFA NA FARKO (NA RANAR SALLAH), DA KUMA ALAMAR CEWA TSOHON VIDEO NE, AMMA ABIN MAMAKI SAI GA SHI 'YAN SHI'A DA WASU DABAN, HAR DA SHEHIN DARIKA SHEHU DAHIRU BAUCHI SUNA GINA HUKUNCI A KANSA, AMMA KUMA 'YAN SHI'A SUNA KOKARIN KARYATA WANNAN RAHOTO DA YA FITO YAKE TUHUMAR AYATULLAHI KHAMNA'IY DA GOMNATINSA TA IRAN DA KUNGIYARSA TA TA'ADDANCI DA AIKATA WANNAN DANYEN AIKI.

DON ME YA SA KUKA YARDA DA WANCAN VIDEO, AMMA BA ZA KU YARDA DA WANNAN RAHOTO BA, ALHALI RAHOTO NE DA YA FITO DAGA BABBAN JAMI'I, KUMA NA HANUN DAMAN AYATULLAHI KHAMNA'IY, WANDA DA SHI AKA YI TARON, YA BA DA LABARIN DUKKAN ABIN DA AKA SHIRYA WA ABOKINSA, KUMA AMININSA TSOHON BABBAN JAMI'IN JEKADANCI NA GOMNATIN IRAN A OFISHINTA NA JAKADANCI DA KE KASAR BELGIUM, MAI SUNA "FARZAD FARHNKI"??!

HABA INA ADALCI YAKE A NAN?!
ALHALI ALLAH YA UMURCI MUMINAI DA YIN ADALCI KO DA KUWA A KANSU NE.
ALLAH YA CE:

{يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُونُوا قَوَّامِينَ بِالْقِسْطِ شُهَدَاءَ لِلَّهِ وَلَوْ عَلَى أَنْفُسِكُمْ أَوِ الْوَالِدَيْنِ وَالْأَقْرَبِينَ } [النساء: 135]

SABODA HAKA, KAMAR YADDA KUKA GASKATA WANCAN VIDEO NA DAN SARKIN SAUDIYYA, TO DOLE NE KU GASKATA WANNAN RAHOTO DA YA TABBATAR DA LAIFI A KANKU KU 'YAN SHI'A.

SABODA HAKA, BAI KAMATA KU KARYATANI BA, DON BA NI NA KAR ZOMON BA, RATAYA AKA BA NI.

KA'IDA A WAJEN MALAMAN TANTANCE LABARI ITA CE KAMAR HAKA:

من أسند لك فقد حمَّلك
من أسند فقد برئت ذمته أو عهدته
من أسند فقد أحال ومن أحال فقد برئ

SABODA HAKA BA NI 'YAN SHI'A ZA SU KARYATA BA, BABBAN JAMI'IN TSARO NA HANUN DAMAN KHAMNA'IY ZA SU KARYATA.

KUN GA KUWA, BABU WANI MAI HANKALIN DA ZAI GASKATAKU, YA KARYATA NA HANUN DAMAN AYATULLAHI ALIY KHAMNA'IY JAGORAN THAURA, KUMA WAKILIN MAHDI WANDA YAKE MATSAYIN SHUGABAN "WILAYATUL FAQIH", KUMA SHUGABAN 'YAN SHI'A NA DUNIYA.

TO A GASKIYA INA TSORACE MAKA YA KAI 'DAN SHI'A, IN KA KARYATA WANNAN RAHOTO, TO ZA KA IYA KARYATA AYATULLAH KHAMNA'IY, IN KUWA KA KARYATA SHI TO SHI'ANCINKA YA SAMU MATSALA, DON YA SHIGA GARARI, SABODA KA YI KARAN TSAYE WA WAKILIN "SAHIBUZ ZAMAN".

SABODA HAKA, DOLE NE AL'UMMAR MUSULMIN DUNIYA SU DORA WA AYATULLAHI ALIY KHAMNA'IY DA GOMNATINSA TA IRAN, DA KUMA KUNGIYARSA TA TSAGERUN 'YAN TA'ADDA MAI SUNA "AL- HARSUL HAURIY" ALHAKIN WANCAN TA'ADDANCI DA SUKA YI A MINA, A WAJEN AIKIN HAJJIN BANA.

ALLAH YA TSAREMU DA SHARRIN MAHASSADA.

No comments:

Post a Comment