Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Saturday, 6 February 2016

MA'ANAR SUNNA

Sunnah dai kalmar Larabci ce, ma'anarta kuwa ita ce: hanya da tafarki mai kyau ce, ko mummuna, abin yabo ce, ko abin kushewa. Kuma wannan lafazi ya zo cikin Alqur'an da hadisi.

Kalmar Sunna lafazi ne na Shiri'ah, ma'anarta kuwa ita ce: Bin littafin Allah (SWT) da Sunnar Manzonsa (SAW) (Hadisai ingantattu) da Sahabbansa, cikin al'amuran Aqida (Imani), da na Ibadah (al'amuran addini).

IBN RAJAB ya ce: ''Sunna ita ce Tafarki abun bi, wanda ya kunshi riko da abinda Annabi (SAW) ya kasance a kai, shi da Khalifofinsa Shiryayyu, na al'amuran AQIDA da ayyuka da zantuka. Wannan ita ce cikakkiyar Sunna.''
Kuma du ya ce: ''Da yawa daga cikin Malaman baya, suna kebance sunan Sunna ga abinda ya shafi al'amuran AQIDA, don shi ne TUShEN ADDININ da duk wanda ya saba a cikinsa, to yana cikin hATSARI mai girma.''

Yaushe aka fara amfani da lafazin 'Ahlus Sunna'??
A Tafsirin fadin Allah (SWT):
''يوم تبيض وجوه وتسود وجوه''

Abdullahi Ibn Abbas (RA) ya ce: ''Fiskokin Ahlus Sunna wal Jama'a za su yi haske, fiskokin 'Yan bidi'a da Bata za su yi baki.

Imamu Malik (R) ya ce: ''Sunnah misalin jirgin Annabi Nuhu ne, wanda ya hauta ya tsira, wanda kuma ya makara ta bar shi ya halaka''

Abdullahi bn Abbas (RA) ya ce: ''Kallon mutum Ahlus Sunnah, wanda yake kira zuwa ga Sunnah, yake hani ga Bidi'a, Ibada ne''.

Shaikhul Islami ya ce: ''Lafazin 'Ahlus Sunnah' ana amfani da shi ga wanda ya tabbatar da khalifancin Khalifofi 3, don haka dukkan kungiyoyi za su shiga amma ban da RAFIDA. Ana kuma amfani da shi ga mabiya hadisi da tsantsar Sunnah, to a nan ba mai shiga sai mai tabbatar da siffofi ma Allah (T) ....

No comments:

Post a Comment