Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Monday, 8 February 2016

GASKIYAR SARKIN KANO NE, 'YAN SHI'A SUNA ZAGIN SAHABBAI

(Martani ga wanda ya rubuta Budaddiyar Wasika zuwa ga Mai Martaba Sarkin Kano Sunusi na II)

Bayan 'Yan Shi'a sun yi rigima da sojojin Nigeria a Birnin Zaria a farkon satin da ya wuce, bangarori daban – daban; daidaikun mutane, shugabanni da hukumomi sun tofa albarkacin bakinsu a kan abin da ya faru, daga cikin wadanda suka yi magana mai muhimmanci kuma mai tasiri akwai Mai Martaba Sarkin Kano Malam Sunusi Lamido Sunusi na ll, wanda ya yi Allah - wadai da Aqidar Shi'a ta Zagin Sahabbai da Matan Annabi (saw), kuma ya nuna cewa; Aqidar Musulmai a Kasar Hausa ita ce Aqidar Ahlus Sunnati wal Jama'a, sabanin munanan Aqidu da suka shigo daga baya, kamar Aqidar zagin Sahabbai da Ahlul Baiti, wato Matan Annabi (saw).

Bayan wadannan jawabai na Mai Martaba ne, sai aka samu wani ya yi rubutu mai taken "Budaddiyar Wasika Zuwa ga mai martaba sarki sunusi da al'ummar Nigeria baki daya". Inda marubucin ya yi kokarin kore cewa; 'Yan Shi'a suna zagin Sahabbai.

Amma wannan kawai wani yunkuri ne na neman karfafa guiwan masu tausaya ma su 'Yan Shi'an a kan abin da ya faru da su a Zaria, amma in ba haka ba, ai kowa ya san cewa; zagin Sahabbai a wajen 'Yan Shi'a abu ne bayyananne kamar rana a tsakiyar sama.

To shi wannan marubuci ya yi kokarin boye wannan mummunar Aqida ta 'Yan Shi'a na zagin Sahabbai ta hanyar cakuda karya da gaskiya, don ya rikitar da wadanda ba su yi zurfi a karatu ba. Saboda haka muka ga ya wajaba a kan duk wanda Allah ya ba shi ilmin warware shubuhohi da wannan bawon Allah ya kawo, da ya tashi ya yi bayanin gaskiya, da kuma martini wa karya.

Wannan martini mun kasa shi zuwa kashi biyu kamar haka:
1- Martini a Dunkule.
2- Martini a Rarrabe dalla - dalla.

KASHI NA FARKO: MARTANI A DUNKULE:
Duk wanda ya karanta wannar wasika ta wannan bawon Allah ba zai yi mamaki ba, in ya lura da wasu abubuwa kamar haka:
(1) Addinin Shi'a ya ginu ne a kan Gaba da Kiyayya da Tsana da Hasada. Don haka ya ginu a kan zagi, da suka, da tsinuwa.
Wannan ya kasance ne saboda asalin Addinin Shi'anci Bayahude Abdullahi Dan Saba'i ne ya kirkire shi, Yahudawa kuwa sun shahara da tsananin Adawa da Gaba da Kiyayya da Hasada wa Musulmai.
Allah ya ce:
{لَتَجِدَنَّ أَشَدَّ النَّاسِ عَدَاوَةً لِلَّذِينَ آمَنُوا الْيَهُودَ وَالَّذِينَ أَشْرَكُوا } [المائدة: 82]
Kuma ya ce:
{وَدَّ كَثِيرٌ مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ لَوْ يَرُدُّونَكُمْ مِنْ بَعْدِ إِيمَانِكُمْ كُفَّارًا حَسَدًا مِنْ عِنْدِ أَنْفُسِهِمْ مِنْ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمُ الْحَقُّ } [البقرة: 109]

Saboda haka ne ya sa Addinin Shi'a ya ginu a kan gaba da kiyayya da hasada wa Sahabbai Muminan farko.

(2) Addinin Shi'a ya ginu ne a kan Karya da Munafurci, wanda suke kira da sunan "Taqiyya".
Wannar Aqida ta Taqiyya ita ce ta halatta musu boye gaskiya da hakikanin halinsu. Shi ya sa a kullum 'Yan Shi'a suka cika Duniya da karyar su ba sa zagin Sahabbai, alhali kuwa Littatafansu da Makaloli da lekcoci na Malamansu, da rubuce – rubucensu a yanar gizo da kafafen sadarwa da kafofin sada zumunta duka cike suke da zagin Sahabban (ra).

(3) Tun tuni 'Yan Shi'a suka shiga harkar Tarihi suka bata shi. In ka bibiyi riwayoyi da labarai na Tarihi za ka samu silsilolinsu cike suke da 'Yan Shi'a, wadanda suka dauki yin karya a matsayin Addini da Ibada. Wannan ya sa harkar Tarihi ta cika da karerayi, da labarai raunana da aka ruwaitosu ta hanyar makaryatan maruwaita da raunanansu, wadanda mafiya yawansu 'Yan Shi'a ne.
Wannan ya sa 'Yan Shi'a suke yawaita dogaro a kan labarum Tarihi wajen zaginsu ga Sahabbai.
Alhali abu ne sananne a wajen malaman ilimin riwaya, ba dukkan abin da aka ruwaito ko aka gani a cikin littatafan Tarihi da mafi yawan Littatafan Hadisi yake gaskiya ba. Wannan ya sa Malaman Riwaya suke da ka'ida da take cewa: "Duk wanda ya ba da Labari ko Hadisi ta hanyar ambaton silsilar wadanda suka ruwaito shi to nauyi ya sauka a kansa".
Don haka ba dukkan abin da ka gani za ka dauko ka gaya wa mutane ba, sai abin da ka tabbaar da ingancinsa.

Al- Imam Ibnu Jarir Al- Dabariy ya tsayar da hujja a kan dukkan wanda zai dauko Labari a cikin Littafinsa inda ya ce:
"Duk abin da yake cikin wannan Littafi nawa na labarin da muka ambace shi daga wadanda suka gabata, na daga abin da mai karanta shi zai k'amace shi, ko mai sauraronsa zai ga muninsa saboda bai san wata fiska ta ingancin labarin ba, kuma ba shi da wata ma'ana a bisa hakika, to ya sani cewa; lallai matsalar ba daga wajenmu ta zo ba, matsalar ta zo ne ta bangaren wasu daga cikin maruwaitan labarin zuwa garemu, mu dai kawai mun kawo labarin ne a bisa yadda aka kawo mana shi zuwa garemu".
Tarikhu Al- Dabariy (1/ 8).

Saboda haka duk wani labari da za a kawo na zagi da sukan wani Sahabi ko Matar Annabi (saw) a bisa hujjar an samu ne a cikin littatafan Tarihi, to ba dalili ba ne, kuma wanda ya kawo ba shi da wani uzuri.

(4) Tarihin Sahabbai ya kasu kashi uku (3):
(a) Bayyananne, wato tarihin da yake bayanin falalarsu da adalcinsu. Saboda Ayoyin Al- Qur'ani da Hadisai mutawatirai sun zo sun tabbatar da Adalcinsu da falalarsu.
(b) Rikitacce, wato wanda ya saba ma kashi na farko, to shi wannan wajibi ne a mayar da shi zuwa ga bayyananen, don shi ne asali.
(c) Na k'arya, wannan kam wajibi ne a zuba shi a kwandon shara kai tsaye.

(5) Abin da aka ruwaito na laifuka da rigingimu na tsakanin Sahabbai ya kasu kashi uku (3):
(a) Wanda bai inganta ba ta hanyar riwaya da isnadi (silsila), wannan bai halatta a ambace shi ba, saboda zato mai karfi yana nuna karya aka yi musu, kuma yana dauke da zaginsu da aibantasu, alhali Annabi (saw) ya yi hani a kan zagin Sahabbansa.

(b) Wanda ya inganta, amma yana da fiska da za a dauke shi a bisa kyakkyawar ma'ana, to wannan wajibi ne a dauke shi a bisa kyakkyawar ma'anar, a dauke shi a matsayin ijtihadi suka yi sai suka yi kuskure.

Mai Littafin "Risala" ta Ibnu Abi Zaid Al- Qirawaniy ya ce:
"Kuma kar a ambaci daya daga cikin Sahabban Manzon Allah (saw) sai dai da mafi kyaun ambato, da kamewa daga abin da ya faru a tsakaninsu (na fitina), saboda su ne suka fi kowa cancantar a nema musu kyakkyawar mafita daga cikin mutane, kuma ayi musu zaton mafiya kyaun hanyoyi (Fahimta)".
Risala shafi na (9).

(c) Wanda kuma ya inganta, amma ba shi da yadda za a dauke shi a bisa kyakkyawar ma'ana, to irin wannan yana nan a matsayinsa na laifi nasu, amma kuma bai halatta a zargesu ko a sokesu, ko a aibantasu a kansa ba, saboda gaba dayansu a dunkule Allah ya yi musu alkawarin gafara da shiga gidan Aljanna, don haka su ba abin zargi ba ne a kan laifukan nasu.
Bayan haka kuma akwai wasu wasu abubuwa guda bakwai (7), wanda kowanne daya daga cikinsu sababi ne da zai sa Allah ya gafarta musu, ya ba su gidan Aljanna kai tsaye ba tare da azaba ko wata uquba ba:
(a) Tuba, muna kyautata zaton sun tuba a kan laifukan nasu, saboda Sahabbai mutane ne da suka fi kowa saurin tuba, kuma duk wanda ya tuba kamar wanda tun asali ba shi da zunubi ne.
(b) Istigfari, wato neman gafara, sahabbai mutane ne masu yawan istigfari.
(c) Manyan aiyukan alheri da suke da shi, wa'danda suke wanke munanan aiyukansu. Misali; sun riga sauran al'umma shiga muslunci, da yin imani da allah da manzonsa (saw), da yin jihadi, da ba da jinanensu da dukiyoyinsu saboda Allah da Addininsa da Manzonsa (saw), da fifita Allah da Manzonsa (saw) da Addininsa da Ranar lahira a kan iyayensu da 'ya'yansu da danginsu da garuruwansu da dukiyoyinsu, da taimakon Manzon Allah (saw) da kawukansu da dukiyoyinsu.
(d) Addu'an da musulmai suke yi musu a kullum, suna cewa; "Allah ya yarda da su", wacce ta kunshi rok'on Allah ya gafarta musu ya yi musu rahama, ya ba su gidan Aljanna, ya tsaresu daga fushinsa da shiga wuta.
(e) Ceton Annabi (saw) garesu.
(f) Allah zai gafarta musu a dalilin musiba da bala'i da ya samesu a halin rayuwarsu ta duniya, saboda bala'in da yake samun mumini kaffara ce gare shi.
(g) Tsantsar rahamar Allah da tausayinsa da ihsaninsa da afuwansa da gafararsa ga bayinsa, ba tare da sa hanun wanin mahluki ba.
• Saboda haka, dukkan kurakurai da laifukan sahabbai, imma duka wa'dannan abubuwa da muka ambata su lullu'besu, ko kuma wasu daga cikinsu sun riskesu.
• Saboda haka ta yaya za ka zargesu, kana zaginsu kana aibantasu alhali ba su da laifi abin zargi a wajen Allah Mai Rahama?!

(6) Menene zagi?
Shin ambaton laifi kawai shi ne zagi?

Abu ne sananne zagi shi ne; aibantawa da zargi da muzantawa. Saboda haka ruwaito Hadisi da yake dauke da laifin wani Sahabi a cikin wani Littafin Hadisi, da silsila ingantacciya ba ya zama zagi kai tsaye, har sai an dauke shi a matsayin abin aibantawa ko muzantawa ko zargi.

KASHI NA BIYU: MARTINI A RARRABE:
A wannan bangare za mu bibiyi muhimman abubuwan da mai wannar wasikar ya kawo, daya bayan daya muna mayar masa da martini, muna warware abin da ya sa'ba ma gaskiya a cikinsa.

BANGARE NA FARKO: ZAGIN SAHABBAI.

1. Mai Wasika ya nuna cewa; Malaman Sunna suna rushe Adalcin Sahabbai a cikin littattafansu, ta hanyar ruwaito Hadisai ingantattu da suke dauke da ambaton laifin wani Sahabi.

To da farko: sai mu ce; duk abin da ya inganta na laifin wani Sahabi, babu matsala a cikin ruwaito shi, inda matsalar take shi ne wajen daukar wannan Hadisi da mu'amalantar laifin Sahabin da yake cikinsa.
Su Ahlus Sunna suna daukarsa ne a matsayin Hadisi da za a ilmantu da shi a Addini, kuma suna mu'amalantar laifin wannan Sahabin ta hanyar daukarsa a bisa ma'ana mai kyau, da ba da uzuri ma Sahabin, saboda shi ba abin zargi ba ne. Saboda su Ahlus Sunna suna daukan abin da ya inganta na laifukan Sahabbai ne a bisa kyakkyawar ma'ana, wacce ba za ta kai ga aibantasu ba, kamar yadda a baya muka gabatar da maganar Mai Risala.
Amma su 'Yan Shi'a suna daukar Hadisin ne a matsayin hanyar tallata laifin Sahabin, da kuma mu'amalantarsa da aibantawa da zargi da suka. Wannan kuwa shi ne zagin Sahabbai.

Na biyu: ya kamata mai wasika ya san cewa; Don an ruwaito laifin Sahabi da silsila mai inganci ba ya kore Adalcin Sahabin, saboda abubuwa kamar haka:
a. Kasancewar sahabbai adilai ne ba ya kore faruwan kuskure ko laifi daga wajensu, saboda su ba ma'asumai ba ne.
b. Adalar sahabbai ita ce wacce idan aiyukan da'a ma Allah na mutum suka rinjayi na sabonsa to ya zama adali, haka idan aiyukansa na sabo suka rinjayi na da'a to ya zama fasiqi.
Al- Nawawiy ya ce:
"Ra'ayin mafi yawan malamai shi ne; lallai duk wanda aiyukansa na da'a ma Allah suka rinjayi sa'bonsa ya zama adali, akasinsa kuwa shi ne fasiki. Lafazin Imamu Shafi'iy a cikin "Al- Mukhtaswar" ya dace da wannan".
Raudhatu Al- Dalibeen (11/ 225).

Don haka Sahabban Annabi (saw) ba ma'asumai ba ne, suna aikata laifuka, amma aiyukansu na alheri da da'a ma Allah su suka fi rinjaye a kan na sabo, don haka suka zama adilai.

2. Mai Wasika ya nuna cewa: a cikin Littafin Bukhari –wai- Sayyidina Abubakar (ra) da Umar (ra) sun fusata Nana Fatima (ra), har ta tambayesu: Shin ba ku ji Manzon Allah (saw) yana cewa: "Allah yana fushi da fushina ba, kuma yana yarda da yarda ta ba?", sai suka ce; haka ne. Sai ta ce: To ni ma ina fushi da ku, ban yarda da ku ba, kuma idan na hadu da manzon Allah (saw) sai na kai kararku wurinsa saboda abin da kuka yi mana?!".

To wannan labari karya ne, babu wata magana da ta zo da wannan siyaki a cikin Sahihul Bukhari da Muslim. 'Yan Shi'a su ne suka hada wannan labari ta hanyar cakuda karya da gaskiya don su isa zuwa ga zargi da zagin Sayyidina Abubakar (ra) da Umar (ra).

Kawai abin da ya tabbata shi ne; Sayyidina Aliyu (ra) ya yi nufin yi ma Fatima (ra) kishiya, ya auri yar gidan Abu Jahl, to sai labari ya sami Annabi (saw) sai ya ce: bai ba da izni ba, sai dai in Sayyidina Aliyu (ra) ya saki Fatima (ra), sai ya auri yar Abu Jahl din. Sai yake cewa: "Fatima tsoka ce daga gareni, abin da zai cutar da ita zai cutar da ni, wanda ya fusatata ni ya fusata".
Bukhari da Muslim.
To sai 'Yan Shi'a suke daukar wannan hadisi suke hada shi da Hadisin Fatima (ra) na neman gadonta da ta yi a wajen Abubakar (ra), wanda ta yi fushi don bai bata ba. Sai 'Yan Shi'an suke zargi da aibanta Abubakar (ra) da Umar (ra) saboda haka, suke ce musu azzalumai mak'iya Allah.
Alhali maganan gado kuwa, Annabi (saw) ne ya hana cin gadonsa, ya ce: "Ba a gadonmu (Annabawa), dukkan abin da muka bari sadaka ne".
Bukhari da Muslim.

Saboda haka, ba don kiyayya ko zalunci Abubabar (ra) ya hana Fatima (ra) gadon da ta tambaya ba, ya hanata ne saboda bin Manzon Allah (saw). Don haka ko a wajen Allah Abubakar (ra) ba shi da laifi.

Saboda haka tambayar da mai wasika ya yi kamar haka:
"Buhari ya zagi sahabbai ke nan. Yayin da ya tabbatar da fushin Allah kan Abubakar da Umar! Kuma ga shi mafi ingancin littafi!?".

Sai mu ce; a'a, Bukhari bai zagi Sahabbai ba, don babu inda ya tabbatar da fushin Allah a kan Abubakar (ra) ko Umar (ra). Hasali ma ya kore fushin Allah ne a kansu, saboda Abubakar (ra) din, umurnin Annabi (saw) ya bi.

Saboda haka 'Yan Shi'a ne suke zagin Sahabi Abubakar (ra) da Umar (ra), suke dora masu fushin Allah a kansu ba Imamul Bukhari ba.

3. Abin da Mai wasika ya ambata daga Ibnu Taimiyya (r) akwai cakuda karya da gaskiya da yawa a ciki. Don haka wajen warware wannan kulli za mu lura da abubuwa kamar haka:
Na farko: Mai wasika ya ce:
"Ibn taimiyya yana cewa mafi yawan sahabbai sun kasance suna kin sa suna la'antarsa!".

Ibnu Taimiyya bai ce mafi yawa ba.
Kuma bai ambaci la'anta ba.

Ga nan maganarsa kamar haka:
إن كثيرا من الصحابة والتابعين كانوا يبغضونه ويسبونه ويقاتلونه
منهاج السنة النبوية (7/ 137 - 138)

"Lallai mutane da yawa daga cikin Sahabbai da Tabi'ai, sun kasance suna kinsa (Aliyu 'ra'), suna zaginsa, suna yakarsa".

Na biyu: Ibnu Taimiyya ya yi wannar Magana ce a lokacin da yake martini a kan maganar malamin Shi'a, wanda ya nuna cewa; Babu wani Sahabi da Muminai suke sonsa a zuciya sai Sayyidina Aliyu (ra) kawai, don ya nuna cewa; dukkan Sahabbai suna kin Abubakar (ra) da Umar (ra) da Usman (ra) a cikin zukatansu.
To sai Ibnu Taimiyya ya yi masa martini da wannar magana da ya fada cewa; ai kuwa an samu mutane da yawa cikin Sahabbai da Tabi'ai wadanda suke kinsa, suke zaginsa, suke yakarsa. Kuma wannan haka ne, don an samu wadanda suka ji haushin Aliyu (ra) a cikin Sahabbai a lokacin da Annabi (saw) ya aika shi tare da wasu Sahabbai zuwa Yaman don karbo Ganima, sai Aliyu (ra) ya dauki wata baiwa daga cikin ganiman, har ya sadu da ita. Sai Sahabban suka ji haushinsa, har suka kai karansa zuwa ga Annabi (saw) a kan hanyarsa ta dawowa daga aikin Hajji, a lokacin da suka tsaya a Ghadeer Khum, har Annabi (saw) ya tashi ya yi huduba, daga cikin abin da ya fada, ya tunatar da mutane, ya hadasu da Allah a game da Iyalan gidansa, a ciki har yake cewa:
من كنت مولاه فعلي مولاه

"Duk wanda na kasance masoyinsa ne, to Aliyu ma masoyinsa ne".

Kuma tun daga lokacin su Sahabban da suke kin nasa suke zarginsa suka canza, suka zama masu sonsa.

Sa'annan an samu Baffansa Abbas (ra) ya ce masa; "Makaryaci, Mai sa'bo, Mai warware alkawari, Maha'inci". Wannan duka zagi ne.
Wadanda suka yake shi kuwa, akwai A'isha (ra), da Dalha (ra) da Zubair (ra), da Mu'awiya (ra), da Amru bn Ass (ra) da sauran wadanda suke tare da su.

Kuma wannan dai shi ne dai abin da aka sani na fitinar da ta faru a tsakanin Sahabbai, wacce aka yi mana umurni da mu kame bakinmu a kanta. Saboda Annabi (saw) ya yi hani a kan zagin Sahabbansa da aibantasu a kan abin da ya faru na fitina a tsakaninsu. Saboda mutane ne da Allah ya gafarta musu, ya yi musu alkawarin Aljanna, duk da ya san za su yi wadannan fitunu a tsakaninsu. Alhali duk cikin wadannan babu wanda aka samu yana kin Abubakar (ra) da Umar (ra), balle ya zagesu, balle kuma ya yakesu, amma shi Aliyu (ra) an samu.

Masu kin Aliyu (ra) da zaginsa da yakarsa a cikin Tabi'ai kuwa Allah ne kawai ya san yawansu, cikin Khawarijawa da suke kafirta shi, da Nasibawa mutanen Sham da suke cewa; shi fasiki ne suka yake shi a cikin rundunar Mu'awiya (ra).

Wannan kawai shi ne abin da Ibnu Taimiyya yake nufi, kuma ya fadi hakan ne a muhalli na martini, ba tare da nufin aibantawa da muzantawa ba.

Na uku: wannan hadisi da mai wasika ya ce; Ibnu Taimiyya ya ruwaito shi, Hadisi ne na Wa'eedi (na alkawarin azaba), nassoshin Wa'eedi kuwa hukuncinsu yana iya faduwa saboda wani sababi, kamar yadda muka gabatar da sabuba da suke kawar da Ukuba a baya.
Saboda haka duk da wancan Hadisi da ya zo a game da Aliyu (ra), mun san cewa; Allah ya gafarta wa Sahabban da suka ki Aliyu (ra), saboda ya yi musu alkawarin gafara, da alkawarin Aljanna dukkansu. Allah ne ya ce:
{لَا يَسْتَوِي مِنْكُمْ مَنْ أَنْفَقَ مِنْ قَبْلِ الْفَتْحِ وَقَاتَلَ أُولَئِكَ أَعْظَمُ دَرَجَةً مِنَ الَّذِينَ أَنْفَقُوا مِنْ بَعْدُ وَقَاتَلُوا وَكُلًّا وَعَدَ اللَّهُ الْحُسْنَى وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ} [الحديد: 10]

Cewa da ya yi:
وكلا وعد الله الحسنى
"Duka bangarorin guda biyu, Allah ya yi musu alkawarin "alhusnaa".
Ma'anar "Al- Husnaa", Aljanna.
Wadannan bangarori guda biyu da Allah ya yi musu alkawarin Aljanna sun kunshi dukkan Sahabbai, don haka kenan wanda ya yi kiyayya wa Aliyu (ra) a cikinsu, ya fita daga cikin munafukai, saboda Allah ya gafarta masa.
4. Amma Hadisin da mai wasika ya ambata daga Mawatta ta Imam Malik ga nan Hadisin kamar haka:
وحدثني عن مالك، عن أبي النضر مولى عمر بن عبيد الله، أنه بلغه، أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: لشهداء أحد «هؤلاء أشهد عليهم»، فقال أبو بكر الصديق: ألسنا يا رسول الله بإخوانهم؟ أسلمنا كما أسلموا. وجاهدنا كما جاهدوا. فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «بلى ولكن لا أدري ما تحدثون بعدي؟» فبكى أبو بكر. ثم بكى. ثم قال: أئنا لكائنون بعدك
موطأ مالك ت عبد الباقي (2/ 461)

Wannan Hadisi bai inganta ba, saboda silsilarsa yankakkiya ce.
Ibnu AbdilBarr ya ce:
قال أبو عمر هذا حديث منقطع لم يختلف عن مالك في انقطاعه
الاستذكار (5/ 104)

A wani wajen kuma ya ce:
هذا الحديث مرسل هكذا منقطع عند جميع الرواة للموطأ
التمهيد (21/ 228)

Saboda haka tunda isnadinsa yankakke ne bai inganta ba, burin mai wasika bai cika ba.

Mai wasika ya ce:
"Wannan fa ita ce Aqidar Imam Malik da ka ce mazhabarsa ake yi a nan Nigeria".

Mai wasika yana nufin Imamu Malik ya zagi Abubakar (ra), tun da ya ruwaito wannan Hadisi a cikin littafinsa.

Sai mu ce: Wa ya gaya maka wannar ita ce Aqidar Malik?
To ga nan Aqidar Imamu Malik kamar haka daga Almajiransa Ibnul Qasim:
قال أبو عمر وقد روي عن مالك - رحمه الله - تقديم الشيخين أبو بكر وعمر - رضي الله عنهما - من رواية بن القاسم وغيره
الاستذكار (5/ 110)

"Abu Umar (Ibnu AbdilBarr) ya ce: kuma hakika an ruwaito daga Malik (r); (Aqidarsa ita ce): Gabatar da Dattawa guda biyu da fifitasu a kan sauran Sahabbai; Abubakar da Umar (ra). Daga riwayar Ibnul Qasim da waninsa".

Wannar ita ce Aqidar Imamuna Maliku, kuma a baya mun gabatar da maganar mai Risala, babban malamin Malikiyya.

5. Mai wasika ya yi ishara zuwa ga wani labari daga Littatafan Tarihi da na Adabi, -wai- Sahabi Abullahi bn Zubair (ra) yana tsananta kiyayya ga Banu Hashim, har ya kai ga ba ya ambaton Salati wa Annabi (saw) a bayyane a cikin Huduba tsawon kwana Arba'in, sai a boye.

Abin lura ga abin da mai wasika ya ambata:
(a) A cikin labarin ba a ambaci Aliyu (ra) ko Hassan (ra) ko Hussaini (ra) ba, amma shi mai wasika ya ambatosu, alhali zuwa wannan lokacin dukansu  sun rasu, babu ko daya da yake raye a cikinsu.
(b) Duk masu kawo labarin ba sa kawo shi da Isnadi, balle a tabbatar da gaskiyar labarin. Sai Balazariy ne kawai ya ambace shi da Isnadi, a cikin Isnadin kuwa akwai Haitham bn Adiyy, shi kuma makaryaci ne. Don haka labarin bai tabbata ba, ko kuma mu ce; labarin karya ne.
Duba "Mizanul I'itidaal" (4/ 324).

6. Misalai a kan zagin da 'Yan Shi'a suke yi wa Sahabbai suna da yawa, kuma za mu iya kasasu zuwa kashi biyu:
a- Wadanda malamansu magabata suka yi a cikin littatafansu.
b- Wadanda suke yi a wannan zamani, imma ta bakin malamansu a cikin lakcocinsu, da lokutan tarukansu, da kuma cikin rubuce – rubucensu da zantukansu. Duk mai bibiyar Yanar gizo, YouTube da Facebook da Tashoshin tauraron Dan Adam shaida ne a kan haka.
Ya isa misali kasancewar an samu wasu da suke yin taron murnar zagayowar ranar rasuwar Matar Annabi (saw) A'isha (ra) a kowace shekara. Da kuma bayyana soyayyarsu ga wanda ya kashe Sayyidina Umar (ra).

Misali guda daya kawai za mu kawo a nan don ya zama ishara ga tarin zage – zage da aibantawa da tsinuwa da nuna kiyayya ga Sahabbai da 'Yan Shi'a suke yi.

Mutane suna jin labarin "Addu'ar Gumakan Quraishawa guda biyu".
اللهم العن صنمي قريش وجبتيها وطاغوتيها وإفكيها، وابنتيهما الذين خالفا أمرك وأنكرا وحيك، وجحدا إنعامك، وعصيا رسولك، وقلبا دينك وحرفا كتابك.....

"Ya Allah ka tsine wa gumakan Quraishawa guda biyu, da Jibtun Quraishawa guda biyu, da Dagutun Quraishawa guda biyu, da Ifkinsu guda biyu, da 'Yanyansu mata guda biyu, wadanda suka saba Umurninka, suka yi inkarin wahayinka, suka musa ni'imominka, suka saba wa Manzonka, suka juya Addininka, suka canza Littafinka…".

Falalar wannar Addu'a, duk wanda ya karantata kamar wanda ya yi jifa ne da masu miliyon (1,000,000) a yakin Badar da Uhudu da Hunaini tare da Annabi (saw).
Duba Biharul Anwar (82/ 260), Mustadrakul Wasa'il (4/ 304).

To abin tambaya: su wanene gumakan Quraishawa guda biyu?
Ga amsa:
يعني باللات والعزى صنمي قريش أبا بكر وعمر.
بحار الأنوار (52 / 284)

"Yana nufin Lata da Uzza, gumakan Quraishawa, su ne Abubakar da Umar".

A cikin addu'ar an ce; har da 'ya'yansu mata guda biyu, wato kenan, addu'a ce ta tsinuwa da mummunan addu'a na bala'i da azaba ga Abubakar (ra) da Umar (ra) da A'isha (ra) da Hafsat (ra).

To wannan kawai misali ne, kuma sai ka karanta addu'ar za ka ga irin munanan maganganu a cikinta.

BANGARE NA BIYU: MA'ANAR AHLUL BAITI:

1) Mai wasika ya yi inkari kasancewar matan Annabi (saw) cikin Ahlul Baiti, inda ya nuna cewa; Hadisin Ummu Salama (ra) ya soke ayar cikin Suratul Ahzabi. Alhali abin da masu ilimi suke yi shi ne hada ayoyin da Hadisin suke yi su yi aiki da su gaba daya. Saboda iyakacin abin da za a fadi a game da Hadisin shi ne; Annabi (saw) bai sanya Ummu Salama tare da su a cikin mayafi ba, amma babu inda Hadisin yake nuna cewa; ita ba ta cikin Ahlul Baiti. Kamar yadda shi mai wasika yake rayawa.
Shi ya sa Malamai suke bayanin ma'anar Hadisin da cewa; Wadannan mutum hudu; Aliyu (ra), Fatima (ra), Hassan (ra) da Hussaini (ra) wadanda Annabi (saw) ya lullubesu da mayafi su suka fi cancantar shiga cikin Ahlul Baitinsa, su ne kebantattun Ahlul Baiti. Saboda dukkansu danginsa na jini, kuma a gidansa suke, a karkashin kulawarsa gaba dayansu. Don haka Matan Annabi (saw) su ma suna cikin Ahlul Baiti, da nassin Qur'ani da kuma Hadisin Salatin Annabi.

Kuma in an dauki maganar mai wasika, inda ya ce; wadannan guda hudu kawai su ne Ahlul Baiti, to yaya zai yi da su Aliyu Zainul Abideena, wadanda Allah bai haliccesu a wannan lokacin ba?
Kenan su ba Ahlul Baii ba ne?!
Ba na ganin mai wasika zai yarda da cewa; jikanun Nana Fatima (ra) ba sa cikin Ahlul Baiti, duk da ba sa cikin wadanda aka lullube da mayafi.

Saboda haka babu dalilin da zai sa ace; matan Annabi (saw) Ahlul Baiti ne a bisa ma'anar Luga, saboda ayoyi da Hadisai sun shigar da su cikin ma'ana ta Shari'a ta Ahlul baiti.
2) Mai wasika ya nuna cewa; Zainab (ra) da Rukayya (ra) da Ummu Kulthum (ra) ba 'ya'yan Annabi (saw) na haifuwa ba ne, 'ya'ya ne na reno a gidansa.

Wannar magana ta ci karo da Al- Qur'ani, saboda Allah ya ba mu labarin cewa; Annabi (saw) yana da 'ya'ya mata ba 'ya guda daya kawai ba.
Allah ya ce:
{يَاأَيُّهَا النَّبِيُّ قُلْ لِأَزْوَاجِكَ وَبَنَاتِكَ وَنِسَاءِ الْمُؤْمِنِينَ يُدْنِينَ عَلَيْهِنَّ مِنْ جَلَابِيبِهِنَّ ذَلِكَ أَدْنَى أَنْ يُعْرَفْنَ فَلَا يُؤْذَيْنَ } [الأحزاب: 59]

"Ya kai Annabi, ka ce wa matanka da 'ya'yanka mata, da matan muminai….".

Allah bai ce: وربيباتك 'ya'yan reno ba.

Kuma duka malaman Tarihi da Nasaba (ilimin sanin dangantaka) sun tabbatar da cewa; 'ya'yan Annabi (saw) mata su hudu ne; Zainab, Rukayya, Ummu Kulsum da Fatima (ra).
Don buga misali duba "Ansabul Ashraaf" na Balazariy (1/ 397, 401, 402), inda yake bayanin 'ya'yan da Khadija (ra) ta Haifa ma Annabi (saw).

'Yan Shi'a suna koresu daga cikin 'ya'yan Annabi (saw) don Sayyidina Usmanu (ra) ya fi Sayyidina Aliyu (ra) matsayi ta fiskar surukuntaka da Annabi (saw).

Don haka wannan inkari ba abin la'akari ba ne, kamar yadda ba za mu yi la'akari da ra'ayin 'Yan Shi'a Nusairiyya da suke cewa; -wai- Hassan da Hussaini ba 'ya'yan Aliyu (ra) da Fatima (ra) ba ne, -wai- 'ya'yan Salmanul Farisiy (ra) ne.

BANGARE NA UKU: BIN TAFARKIN AHLUS SUNNATI WAL JAMA'A:

a) Mai wasika ya yi kokarin nuna cewa; kuskure ne ace za abi abin da iyaye da kakanni suka tafi a kai, saboda ayoyi sun zo da zargin haka.

To lallai wannan kuskuren fahimta ne, saboda Allah ba ya zargi bin tafarkin iyaye da kakanni ne kai tsaye ba, a'a, ya zargi hakan ne saboda kasancewar iyaye da kakanni sun tafi ne a kan bata na kafirci da shirka. Amma in har iyaye da kakannin sun tafi ne a kan shiriya na Muslunci da Sunna da tafarkin Sahabbai da Tabi'ai, wannan ba abin zargi ba ne.
Allah ya ce:
{وَاتَّبَعْتُ مِلَّةَ آبَائِي إِبْرَاهِيمَ وَإِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ مَا كَانَ لَنَا أَنْ نُشْرِكَ بِاللَّهِ مِنْ شَيْءٍ ذَلِكَ مِنْ فَضْلِ اللَّهِ عَلَيْنَا وَعَلَى النَّاسِ وَلَكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَشْكُرُونَ } [يوسف: 38]
Kuma ya ce:
{وَجَاهِدُوا فِي اللَّهِ حَقَّ جِهَادِهِ هُوَ اجْتَبَاكُمْ وَمَا جَعَلَ عَلَيْكُمْ فِي الدِّينِ مِنْ حَرَجٍ مِلَّةَ أَبِيكُمْ إِبْرَاهِيمَ هُوَ سَمَّاكُمُ الْمُسْلِمِينَ مِنْ قَبْلُ } [الحج: 78]

Saboda haka bin abin da aka samu iyaye da kakanni a kansa ba abin zargi ba ne kai tsaye, akwai lokacin da yake zama abin zargi, shi ne idan iyayen sun tafi ne a kan kafirci da shirka da bidi'a da sabo. Akwai kuma lokacin da yake zama abin yabo, idan iyayen sun tafi ne a kan Muslunci da Imani da Tauhidi da Sunna da Da'a ma Allah, kamar yadda Annabi Yusuf (as) ya ce; ya bi tafarkin iyayensa. Haka Allah ya nuna mana Muslunci hanyar babanmu ne Annabi Ibrahim (as).

b) Mai wasika ya ambaci wasu abubuwa da ya dangantasu ga Littafin Bukhari, ga su kamar haka:
(A) Fitsari a tsaye.
(B) Shan nabiz.
(C) Lekowan Annabi (saw) zuwa ga matasa masu wasa ranar Eidi.
(D) Annabi (saw) ya mance aya a cikin Sallah har an yi masa tuni.
(E) Tsere da matarsa.
(F) Buga Duffi (bandiri) a gidan Annabi (saw).
Wadannan duka in har in ya tabbata Annabi (saw) ya yisu, ta hanyar Isnadi mai inganci to dole ne mu yarda Annabi (saw) ya yi su, in kuma ba su tabbata ba, saboda raunin Isnadi to ba za mu yarda cewa; Annabi (saw) ya yi su ba.
Don haka fadin mai wasika cewa; ba za su yarda da su ba, wannan ya yi kama da bin son zuciya, kamata ya yi ya kore mana tabbacinsu daga Annabi (saw) ta hanyar da ake bi wajen kore labarai. Ai ba zai yiwu muna kore abubuwa a bisa son rai ba. In son rai za abi, wani kuma yana ganin ya tabbata Annabi (saw) ya yi su, yana ganin hakan ya dace da son ransa.
Saboda haka son rai da son zuciya ba su ne za su zama ma'auni na tabbatar da abu ko korewa ba, da yarda ko kin yarda ba, saboda mutane sun banbanta wajen son ransu, ba dadai suke ba.

Saboda haka in duka wadannan ya tabbata sun faru da Annabi (saw) ta hanyoyi masu inganci a riwaya, to ba za a saurari mai korewa a bisa son zuciya ba. Saboda in an bi haka to kowa zai kore dukkan abin da ya saba ma son zuciyarsa. Kawai za mu saurari mai korewa ne ta hanyar da ake bi wajen kore tabbacin Hadisi, a bisa ka'idojin malaman Hadisi na kore labarai ko raunata riwaya. Saboda tabbatar da labari ko kore shi ba abu ne da ya dogara a kan hankali ba, balle ace mutum zai karbi duk abin da ya dace da son ransa, ya kore abin da ya saba ma son zuciyarsa.

c) Sa'annan kuma karya ne, a cikin tabbatatun Hadisai babu inda aka taba nuna cewa; Sahabi ya fi Annabi (saw) daraja, saboda dukkan Musulmi ya yi imanin cewa; matsayi da darajar Sahabitakar Annabi (saw) ba za ta kai matsayi da darajar Annabta ba, balle kuma ta Manzanci. Don haka kowa ya san cewa; Duk duniya babu wanda matsayinsa zai kai matsayin Annabi (saw) balle kuma ace; ya fi shi.

Saboda haka duk wanda ya fahimci cewa; Umar (ra) ya fi Annabi (saw) sanin gaskiya to ya tuhumi kwakwalwarsa, kada ya tuhumi Hadisin Annabi (saw), matsalar ta kwakwalwar ce ba ta Hadisin ba. Don haka ne ma duk wanda ya kudurta cewa; wani ya fi Annabi (saw) sanin gaskiya, ko sanin shiriya to ko shakka babu za a nemi ya tuba, in kuma ya k'i za a sare kansa, saboda ya yi ridda.

Don haka duk abin da ya tabbata Annabi (saw) ya fada a kan Umar (ra) gaskiya ne, kuma mun yarda da shi, a bisa yadda Manzon Allah (saw) yake nufi.

BANGARE NA HUDU: SABABIN BALA'I DA MASIFA:

Mai wasika ya nuna cewa; zagin Sahabbai ba shi ne sababin bala'in da muke ciki ba, -wai- saboda babu wani mai zagin sahabbai balle bala'in ya faru a kan haka. To wannan kokari ne na karyata waki'i, da abin da kowa yake gani a zahiri, kuma ya shaida. Kowa yana ji yana ganin 'Yan Shi'a suna zagin Sahabbai da Matan Annabi (saw) a zahiri, kuma kowa ya ga abin da ya faru da su a Zaria a farkon satin da ya gabata.
Sai kuma ya nuna cewa; sababin bala'in shi ne yin watsi da wasiyyar da Annabi (saw) ya yi ta yin biyayya ga littafin Allah da alayensa.
To wannar magana tana kunshe da karya da gaskiya. Ko shakka babu sababin bala'i shi ne sakaci wajen riko da Addinin da Annabi (saw) ya zo da shi daga wajen Allah, wanda ya rasu ya bar Sahabbansa a kansa, na bin Qur'ani da Sunnarsa. Lallai babu abin da zai gyara karshen wannar al'umma sai ta hanyar riko da bin abin da farkonta ya yi riko da shi.

Amma maganar wasiyya da bin iyalansa a kebance, wannan abu ne da yake bukatar dalili, kuma babu dalilin. Kawai abin da Annabi (saw) ya umurci al'umma da shi, shi ne riko da abin da yake kai shi da Sahabbansa, wato Qur'ani da Sunnarsa (saw).
Saboda haka, kasancewar iyalan gidan Annabi (saw); danginsa da matansa da zurriyarsa suna cikin Sahabbai, to suna cikin gamayyar Sahabbai da Annabi (saw) ya yi wasiyya da bin abin da suke kai, na bin Qur'ani da Sunna. Amma babu wani dalili da ya kebe bin iyalansa a kebe su kadai.
An tambayi Shugaban iyalan gidan Annabi (saw), Sayyidina Aliyu (ra); shin Annabi (saw) ya kebanceku da wani abu? Sai ya ce; a'a, bai kebancemu da wani abu da ya waremu daga gamayyar sauran mutane ba.

Daga karshe nake rokon Allah ya nuna mana gaskiya ya ba mu ikon binta, ya nuna mana karya ya bamu ikon guje mata, ya shiryar da mu hanya madaidaiciya.
Allah ya saka wa Mai Martaba Sarkin Kano Malam Sunusi Lamido Sunusi da Alheri, Allah ya yawaita mana irinsa a cikin Shugabanni da Sarakuna.
Allah ya fadakar da jagororin al'umma; Sarakuna da Shugabanni na siyasa zuwa ga sharrin munanan Aqidu, ya basu ikon kawar da su. Allah ya basu ikon taimakon Addininsa da Sunnar Manzonsa (saw).
Allah ya bamu zaman lafiya a kasarmu, tare da albarka da yalwar arziki.

Ammar AbuTurab
Litinin 21/12/2015

2 comments: