A BAYA MUN YI BAYANI WA MUTANE CEWA; ALIYU GUDA BIYU NE, ALIYUN 'YAN SHI'A WANDA BABU SHI A DUNIYA, KWATA - KWATA ALLAH BAI HALICCE SHI BA, DA KUMA ALIYU NA HAKIKA (RA), WANDA SHI NE ALIYUN MUSULMAI, DAN UWAN ANNABI (SAW), DAN BAFFANSA ABU DALIB, MIJIN 'YARSA FATIMA (RA), KUMA KHALIFA NA HUDU (4), A BAYAN ABUBAKAR (RA) DA UMAR (RA) DA USMANU (RA), UBAN HASAN DA HUSAINI (RA).
KASANCEWAR ALIYUN 'YAN SHI'A ABU NE KAMAR DODO, ABIN DA AKE FA'DANSA AMMA BABU HAKIKANINSA, SHI YA SA ZA KA GA IN 'YAN SHI'AN ZA SU FADI FALALOLINSA SU YABE SHI, IN ZA SU TABBATAR DA WILAYARSA DA IMAMANCINSA BA SU DA ABIN DA ZAI TABBATAR DA HAKA SAI HADISAI NA K'ARYA KO RU'BA'B'BUN HADISAI, SABODA SHI ALIYUN NASU KWATA BABU SHI A DUNIYA, ALLAH BAI HALICCE SHI BA, SHI YA SA BABU YADDA ZA A YI A SAMU HADISI INGANTACCE WANDA YA FITO DAGA BAKIN ANNABI (SAW), BAKIN DA BA YA FURTA SON RAI, WANDA YA ZO YANA YABONSA, YANA BAYANIN FALALARSA, KO YANA BAYANIN IMAMANCINSA. SABODA BABU YADDA ZA A YI ANNABI (SAW) YA YABI ABUN DA BABU SHI, BA SHI DA HAKIKA, BARE YA TABBATAR MASA DA WILAYA DA IMAMA.
WANI MALAMIN SHI'A A FACEBOOK YANA YABON ALIYUNSU, YANA BAYYANA FALALAR WANDA YA YI IMANI DA IMAMANCINSA DA WILAYARSA, -WAI- SAI YA KAWO WANI HADISI INGANTACCE!!
ALIYUN SHI'AN NE ZA A SAMU HADISI INGANTACCE YANA YABON WANDA YA YI MASA WILAYA??!!!
GA NAN HADISIN KAMAR HAKA:
4642 - حدثنا بكر بن محمد الصيرفي، بمرو، ثنا إسحاق، ثنا القاسم بن أبي شيبة، ثنا يحيى بن يعلى الأسلمي، ثنا عمار بن رزيق، عن أبي إسحاق، عن زياد بن مطرف، عن زيد بن أرقم رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «من يريد أن يحيى حياتي، ويموت موتي، ويسكن جنة الخلد التي وعدني ربي، فليتول علي بن أبي طالب، فإنه لن يخرجكم من هدى، ولن يدخلكم في ضلالة» هذا حديث صحيح الإسناد، ولم يخرجاه "
المستدرك على الصحيحين للحاكم (3/ 139)
WANNAN HADISIN K'ARYA NE!!
MALAMIN SHI'AN YA CE:
"Kamar yadda yazo a cikin ingantattun Hadisai a wajen Sunna cewa:
Manzon Allah (S) yace:
"Wanda duk ya qayatar da shi yake son yayi rayuwa irin rayuwata, ya mutu irin mutuwata, kuma a sauke shi a aljannar da Ubangijina ne ya gina ta, to ya riqe Aliyyu Shugaba a bayana, kuma ya riqe wanda duk Aliy yace Shugaba ne a bayansa, kuma yayi riqo da Ahalin gidana a bayana, domin sune dangina waxanda aka haliccesu da jinina, kuma aka azurtasu da fahimtata da ilimina, to tavewa ga waxanda suke qaryata falalolinsu daga al'ummata, waxanda suke yanke dangantakata dasu, Ubangiji ba zai basu cetona ba".
WANNAN K'ARYA NE KAWAI DA JAHILCI.
ABIN DA YA KAI WANNAN MALAMI NA SHI'A GA WANNAN JAHILCIN SHI NE SABODA ALHAKIM YA CE:
هذا حديث صحيح الإسناد، ولم يخرجاه
KAR KA YI MAMAKI, A JIYA NA YI MUKU BAYANI CEWA; AL- HAKIM ABU ABDILLAH AL- NAISABURIY A CIKIN LITTAFINSA "AL- MUSTADRAK" AKWAI HADISAI RU'BA'B'BU HAR DA NA K'ARYA MASU YAWA A CIKINSA. ABIN DA YA FARU KUWA SHI NE; SHI AL- IMAMUL HAKIM YA YI NIYYAR FITAR DA HADISAI NE INGANTATTU DA SUKA KU'BUCE WA IMAMUL BUKHARI DA MUSLIM, TO SAI YA TARA HADISAN, A KAN DAGA BAYA ZAI ZO YA YI TANKADE DA RERAYA, TO YA FARA HAKAN, AMMA SAI MUTUWA TA RIGA SHI.
WASU MALAMAN KUMA SUNA GANIN DA MA 'DAN SHI'A NE, SHI YA SA YA SHIGAR DA HADISAN K'ARYA NA FALALAN ALIYU (RA) DA IMAMANCINSA A CIKIN LITTAFIN NASA.
DON HAKA, IN KA SAN WANNAN SHI ZAI SA BA ZA KA SHA MAMAKIN SAMUN HADISAI RAUNANA HAR DA RU'BA'B'BU DA NA KARYA MASU TARIN YAWA A CIKIN LITTAFIN NASA BA. WANNAN YA SA AL- IMAMU AL- ZAHABIY YA ZO YA BI LITTAFIN YA YI MASA TA'ALIK'I, YA BAYYANA IRIN WADANCAN HADISAI RAUNANA DA RA'BA'B'BU DA NA K'ARYAN.
GA NAN MAGANGANUN MALAMAI A KAN HADISAN DA AL- HAKIM YA INGANTA A CIKIN LITTAFINSA "AL- MUSTADRAK":
1. IBNU SALAH:
وهو واسع الخطو في شرط الصحيح، متساهل في القضاء به.
مقدمة ابن الصلاح = معرفة أنواع علوم الحديث - ت عتر (ص: 22)
2. AL- ZARKASHIY:
قال الخطيب أبو بكر أنكر الناس على الحاكم أبي عبد الله أحاديث جمعها وزعم أنها صحاح على شرط الشيخين
النكت على مقدمة ابن الصلاح للزركشي (1/ 214)
3. AL- ZAHABIY:
في (المستدرك) شيء كثير على شرطهما، وشيء كثير على شرط أحدهما، ولعل مجموع ذلك ثلث الكتاب بل أقل، فإن في كثير من ذلك أحاديث في الظاهر على شرط أحدهما أو كليهما، وفي الباطن لها علل خفية مؤثرة، وقطعة من الكتاب إسنادها صالح وحسن وجيد، وذلك نحو ربعه، وباقي الكتاب مناكير وعجائب، وفي غضون ذلك أحاديث نحو المائة يشهد القلب ببطلانها، كنت قد أفردت منها جزءا، وحديث الطير بالنسبة إليها سماء، وبكل حال فهو كتاب مفيد قد اختصرته، ويعوز عملا وتحريرا
سير أعلام النبلاء ط الرسالة (17/ 175 - 176)
4. AL- ZAHABIY:
قلت: ثم تغير رأي الحاكم وأخرج حديث الطير في مستدركه؛ ولا ريب أن في المستدرك أحاديث كثيرة ليست على شرط الصحة, بل فيه أحاديث موضوعة شان المستدرك بإخراجها فيه. وأما حديث الطير فله طرق كثيرة جدًّا قد أفردتها بمصنف ومجموعها هو يوجب أن يكون الحديث له أصل.
تذكرة الحفاظ = طبقات الحفاظ للذهبي (3/ 164)
5. IBNU HAJAR:
قيل في الأعتذار عنه أنه عند تصنيفه للمستدرك كان في أواخر عمره وذكر بعضهم أنه حصل له تغير وغفلة في آخر عمره ويدل على ذلك أنه ذكر جماعة في كتاب الضعفاء له وقطع بترك الرواية عنهم ومنع من الاحتجاج بهم ثم أخرج أحاديث بعضهم في مستدركه وصححها من ذلك أنه أخرج حديثا لعبد الرحمن بن زيد بن أسلم وكان قد ذكره في الضعفاء فقال: أنه روى عن أبيه أحاديث موضوعة لا تخفى على من تأملها من أهل الصنعة أن الحمل فيها عليه وقال في آخر الكتاب فهؤلاء الذين ذكرتهم في هذا الكتاب ثبت عندي صدقهم لأنني لا استحل الجرح إلا مبينا ولا أجيزه تقليدا والذي اختار لطالب العلم أن لا يكتب حديث هؤلاء أصلا.
لسان الميزان (5/ 233)
AL- HAKIM 'DAN SHI'A NE:
1. AL- KHADIBUL BAGDADIY:
فأما أبو عبد الله الحاكم فأخبرنا أبو منصور القزاز قال: أخبرنا أحمد بن على بن ثابت قال: كان ابن البيع الحاكم يميل إلى التشيع
تاريخ بغداد وذيوله ط العلمية (22/ 145)
2. AL- ZAHABIY:
إمام صدوق، لكنه يصحح في مستدركه أحاديث ساقطة، ويكثر من ذلك، فما أدرى هل خفيت عليه فما هو ممن يجهل ذلك، وإن علم فهذه خيانة عظيمة، ثم هو شيعي مشهور بذلك من غير تعرض للشيخين.
وقد قال ابن طاهر: سألت أبا إسماعيل عبد الله الأنصاري عن الحاكم أبي عبد الله، فقال: إمام في الحديث رافضي خبيث.
قلت: الله يحب الانصاف، ما الرجل برافضى، بل شيعي فقط.
ميزان الاعتدال (3/ 608)
3. AL- ZAHABIY:
أنبأني أحمد بن سلامة، عن محمد بن إسماعيل الطرسوسي، عن ابن طاهر: أنه سأل أبا إسماعيل عبد الله بن محمد الهروي، عن أبي عبد الله الحاكم فقال:
ثقة في الحديث رافضي خبيث (3) .
قلت: كلا ليس هو رافضيا، بلى يتشيع (4) .
قال ابن طاهر: كان شديد التعصب للشيعة في الباطن، وكان يظهر التسنن في التقديم والخلافة، وكان منحرفا غاليا، عن معاوية - رضي الله عنه - وعن أهل بيته، يتظاهر بذلك ولا يعتذر منه
سير أعلام النبلاء ط الرسالة (17/ 174 - 175)
A TAKAICE DAI IN AL- HAKIM YA INGANTA HADISI BAI ZAMA HUJJA BA, SABODA YANA DA SAKACI WAJEN INGANTA HADISI, HAR YANA INGANTA HADISAN K'ARYA, KUMA ANA TUHUMARSA DA SHI'ANCI.
TO SHI WANCAN HADISI NA FALALAR WANDA YA YI IMANI DA WILAYAR ALIYUN 'YAN SHI'A DA MALAMAN SHI'AR FACEBOOK SUKE TA RAWA SUNA JUYI SABODA SUN SAMU HADISI INGANTACCE NA FALALAR YIN WILAYA GA ALIYU DA WANDA YA YI IMANI DA WILAYAR TASA DA IMAMARSA, HADISIN KARYA NE, WANI RIK'AK'K'EN MAK'ARYACI 'DAN SHI'A NE YA TSUGUNA YA TAKARKARA YA SHIRGA K'ARYA YA K'IRK'IRE SHI.
AL- HAKIM YA CE:
هذا حديث صحيح الإسناد، ولم يخرجاه
SAI AL- ZAHABIY YA CE:
قلت: أنى له الصحة؛ فيه القاسم بن أبي شيبة متروك، وشيخه يحيى بن يعلى الأسلمي، وهو ضعيف، واللفظ ركيك؟ فهو إلى الوضع أقرب.
مختصر تلخيص الذهبي (3/ 1418)
DON HAKA WANNAN HADISIN K'ARYA NE. ALIYUN 'YAN SHI'A DA WILAYARSA DUKA K'ARYA NE, MAK'ARYATA ALMAJIRAN 'DAN SABA'I NE SUKA K'IRK'IRE SHI. A GABA ZAMU TONA ASIRIN WANNAN HADISI.
No comments:
Post a Comment