Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Thursday, 25 February 2016

YAYE SHUBUHOHI A KAN SULHUN HASSAN (RA) (10)

(16) NASIRU YA CE:
TO ASHE KENAN SULHUNDA ANNABI YAYI DA MUSHRIKAI ASANDA SUKACE SHIBA ANNABIN ALLAH BANE BA, SANNAN KUMA SUKACE DOLE AGOGE SUNANSA NA RASULULLAHI, HAKA KUMA YAYARD AKAYI, WANNAN YANUNA KENAN CEWA BAWAJIBI BANE RUBUTA SUNAN RASULULLAHI ADUK CIKIN WURARENDA SUKAZO ACIKIN ALKUR'ANI DAWANIN HAKA. SULHUN DAYAYI AKAN YARDA DAGOGE SUNANSA YANUNA BA WAJIBI BANE ARIKA RUBUTA SUNANSA.

AMMAR:
AKWAI JAHILCI MAI YAWA A CIKIN WANNAR MAGANAR:
(A) DAIDAITA SULHUL HUDAIBIYYA DA SULHUN HASAN BN ALI (RA). WANNAN JAHILCI NE.

(B) CEWA; " SANNAN KUMA SUKACE DOLE AGOGE SUNANSA NA RASULULLAHI, HAKA KUMA YAYARD AKAYI, WANNAN YANUNA KENAN CEWA BAWAJIBI BANE RUBUTA SUNAN RASULULLAHI ADUK CIKIN WURARENDA SUKAZO ACIKIN ALKUR'ANI DAWANIN HAKA."
WANNAR MAGANAR TSANTSAN JAHILCI NE, KUMA MAGANA CE MARAS KAN GADO.
ASALI MA MENENE ALAK'ARTA DA MAGANARMU??!
MUNA MAGANA NE FA A KAN MATSAYIN AURE DA IMAMA SAI KA SHIGA WANNAN KAME - KAMEN!!

(C) MENENE ALAK'A TSAKANIN TAKARDAR DA AKA RUBUTA A WAJEN SULHUL HUDAIBIYYA DA AL- QUR'ANI??!

(D) ALQUR'ANI LITTAFIN ALLAH NE, AMMA ITA WANNAR TAKARDAR WA KAFIRAI FA ZA A KAITA.

(E) AL- QUR'ANI MAGANAR ALLAH NE, WANNAR TAKARDA KUWA MAGANAN MUTANE NE A CIKINTA.

(F) NASIRU YA CE: " SULHUN DAYAYI AKAN YARDA DAGOGE SUNANSA YANUNA BA WAJIBI BANE ARIKA RUBUTA SUNANSA."
DUK WANNAN SHIRIRITA NE KAWAI DA SHIRME.

** BAI KAMATA RASHIN HUJJA YA MAI DA MUTUM MAHAUKACI BA, HAR YA KAI GA BAI SAN ABIN DA YAKE FA'DA KO YAKE RUBUTAWA BA!!

(17) NASIRU YA CE:
ANAN IDAN KOWA YADUBA YASAN KANAYIN MAGANA NE AKAN ABINDA AKE CEWA DASHI WAJIBI, TOSHINE NAKE CEWA DAKAI :

AMMAR:
A'A, NI INA MAGANA NE A KAN ABIN DA YA FI WAJIBI A WAJENKU, WATO ITA CE; IMAMA. TUN DA IMAMA RUKUNIN ADDINI CE A SHI'A, SAI DAI IN KAI KA JAHILCI SHI'AR. KUMA NA KAWO MAKA NASSOSHI DAGA IMAMANKU, AMMA SABODA HUJJA NE A KANKA, BA KA IYA CEWA; KOMAI A KANSU.
DON HAKA, IN BA JAHILTAR SHI'A BA, BABU WANDA ZAI DADAITA WAJABCIN IMAMA DA WAJABCIN AURE. DUK 'DAN SHI'A NA ASALI YA SAN CEWA; WAJABCIN IMAMA, WAJABCI NE NA FARILLA NA RUKUNI A CIKIN ADDINI.

(18) NASIRU YA CE:
HABA AMMAR KO KAMANTA CEWA SUHAIL YACEWA ANNABI DAMUN YARDA CEWA KAI MANZON ALLAH NE DABAMU YAKEBA SANNAN KUMA SUKACE DASHI DOLENE AGOGE SUNANSA NA RASULULLAHI. SHIN WANNAN ZANCE NASU BAYA NUNA CEWA SUN SAUKE SHI DAGA KAN ANNABTAR SABANE, DUKA WANNAN ZANCEDA MUSHRIKAI SUKE FADA SUN FADANE AGABAN ANNABI SANNAN KUMA AGABAN SAHABBANSA. AMMA SAIYA KARBI YIN SULHU DASU AKAN HAKA, AMAI MAKON YAYAKESU.

AMMAR:
ALLAH SARKI RU'DU!!
IN BAN DA RU'DU IRIN NAKA BA, TUN KAFIN WANNAN LOKACIN BA SU YI IMANI DA MANZON ALLAH (SAW) BA. TUN KAFIN WANNAN LOKACIN SU KAFIRAI NE, TUN KAFIN WANNAN LOKACIN ANNABI (SAW) YA YAK'ESU A BADR, UHUD, AHZAB, DA SAURANSU.
DON HAKA A RANAR HUDAIBIYYA IN SUN CE; KAR A RUBUTA "MANZON ALLAH" A KAN TAKARDAR SULHU, SABODA BA SU YARDA DA MANZANCIN ANNABI (SAW) BA, BA SU ZO DA WANI SABON ABU BA. SABODA TUN DA SU KAFIRAI NE, KUMA BA SU YI IMANI DA MANZON ALLAH BA.
DON HAKA MENENE WANI ABU SABO A CIKIN ABIN DA SUKA YI A HUDAIBIYYA??!

(19) NASIRU YA CE:
SHIN WANNAN ZANCE NASU BAYA NUNA CEWA SUN SAUKE SHI DAGA KAN ANNABTAR SABANE,

AMMAR:
MTSWWWW!!
KA GA WANNAR MAGANAR, WALLAHI BA MAI FA'DANTA SAI CIKAKKEN JAHILI.
SUN SAUK'E SHI A KAN ANNABTARSA, TA YAYA??!
DA MA SUN YARDA SHI ANNABI NE, BARE ACE A RANAR HUDAIBIYYA SUN SAUK'E SHI??!
WANNAN AI JAHILCI NE A FILI, DA KUMA 'DIMAUCEWA NA RASHIN HUJJA!!

(20) NASIRU YA CE:
AMSA : TO KUNGA SUHAIL BN AMR DASHI DA MUTANENSA SUNYI INKARIN ANNABTAR MANZON ALLAH ALOKACINDA AKE RUBUTA SULHUN HUDAIBIYYA. WANNAN ABU YASA SUNZAMA KAFIRAI ABISA ABINDA SUKA FADAWA ANNABI, MEYASA ANNABI BAI YAKE SUBA? SANNAN KUMA KENAN YIN INKARIN ANNABTARSA BA KAFIRCI BANE HAKANE AMMAR?

AMMAR:
MU FA MUNA MAGANA NE A KAN SULHUN DA HASAN (RA) YA YI, BA A KAN SULHUL HUDAIBIYYA BA. KUMA SULHUN HASAN (RA) BA TA DA WATA ALAK'A DA SULHUL HUDAIBIYYA TA KOWACE FISKA, SAI DA A SUNA KAWAI.
SULHUN HASAN (RA) YA KASANCE NE A TSAKANIN 'BANGARORIN MUSULMAI GUDA 2. AMMA ITA SULHUL HUDAIBIYYA TA KASANCE NE TSAKANIN 'BANGAREN MUSULMAI DA NA KAFIRAI. DON HAKA BA SU YI KAMA BA, BARE KA DOGARA A KANSA.
AMMA KU KUMA IMAMANKU SUN CE; INKARIN IMAMANCINSU KAFIRCI NE, AMMA SAI GA NAN MU'AWIYA (RA) DA MUTANENSA SUN YI INKARIN IMAMAR HASAN (RA) AMMA KUMA HASAN (RA) BAI KAFIRTASU BA, KUMA YA JANYE DAGA MATSAYINSA NA IMAMANCI YA YI MUBAYA'A WA MU'AWIYA (RA).
TO YAYA KENAN, SHIN INKARIN IMAMAR BA KAFIRCI BA NE KENAN??

No comments:

Post a Comment