Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Thursday, 25 February 2016

YAYE SHUBUHA A KAN QISSAR GADEER

Shiatu Ali, GA JAWABAI A KAN AMSOSHINKA DA KA BAYAR.

(1) AMSA: SABANIN ZATON KA, LABARIN BAYA NUNI DA CEWA ANNABI (SAWA) YAKI BIN UMARNIN ALLAH, QISSAR TANA NUNI NE DA SAMUWAN MASU YIWA AHLUL BAYT (AS) HASSADA DAGA CIKIN SAHABBAI .....

AMMAR:
WANNAN YA NUNA BA KA FAHIMCI ABIN DA MUKA YI NUNI GARE SHI BA KENAN. TO GA NAN ABIN DA YAKE NUNA CEWA; QISSAR TANA HUKUNTA CEWA; ANNABI (SAW) YA SA'BA UMURNIN ALLAH (T):
KASANCEWAR MAI BA DA LABARIN YA NUNA CEWA; MALA'IKA JIBRILU (AS) YA ZO WA ANNABI (SAW) YANA UMURTANSA DA YA ISAR DA WANNAN SAK'O NA WILAYAR ALI (RA) SAU DA DAMA, AMMA ANNABI (SAW) YA K'I, HAR YA NEMI A 'DAUKE MASA WANNAN ISAR DA SAK'ON, SA'ANNAN DAGA K'ARSHE SAI DA YA SHAR'DANTA WA ALLAH SAI YA BA SHI KARIYA DAGA MUTANE KAFIN YA ISAR DA WANNAN SAK'O. TO KO SHAKKA BABU LALLAI AKWAI YI MA ALLAH TAURIN KAI A CIKIN WANNAN YANAYI. DA K'IN KAR'BAN UMURNINSA KAI TSAYE. WANDA HAR MA SAI DA AKA TSAWATAR MASA, KAFIN NAN YA KAR'BI SAK'ON.:
ان جبرئيل " عليه السلام "
هبط الي مرارا ثلاثا يأمرنى عن السلام ربى وهو السلام ان اقوم في هذا المشهد

KAI KA CE YA YI JINKIRI NE, ALHALI KUMA YADDA YA ZO A CIKIN QISSAR SHI NE KAMAR HAKA:
وسألت جبرئيل " عليه السلام " ان يستعفى لى من تبليغ ذلك اليكم أيها الناس لعلمى بقلة المتقين وكثرة المنافقين ، وادغال الآثمين
وختل المستهزئين
GA SHI AN CE; ANNABI (SAW) YA ROK'I MALA'IKA JIBRILU (AS) DA A YAFE MASA ISAR DA WANNAN SAK'O!!
TA YAYA WANNAN ZAI SA MU 'DAUKI NAKA TAWILIN, NA CEWA; KAWAI JINKIRI YA YI??
KAI, ANNABI (SAW) BAI ISAR DA WANNAN SAK'O BA, HAR SAI DA MALA'IKA JIBRILU (AS) YA ZO DA GARGA'DI DA TSAWATARWA:
اتاه جبرئيل " عليه السلام " على خمس ساعات مضت من النهار بالزجر والانتهار والعصمة من الناس

*** SAI DA AKA TSAWATAR MASA, SA'ANNAN TUKUNA YA YARDA ZAI ISAR DA SAK'ON ALLAH???!!

SA'ANNAN KA CE:
"MU MUNYI IMANI ANNABI (SAWA) MA’ASUMI NE TA KOWACE FUSKA"

LALLAI ABIN DA NA GABATAR NA WANNAR QISSAR, YANA K'ARYATA WANNAN ZANCE NAKA.

(2) AMSA: BA YANA JIN TSORON KADA SU CUTAR DASHI BANE, A’A YANA TSORON NE IDAN SUKA FITINU DA JIN DAUKAKAN DA ALLAH (SWT) YAYIWA IMAM ALI DA AHLUL BAYTI (A.S) ZASU IYA HADDASA FITINA A CIKIN MUSULUNCI....)

AMMAR:
GAFATTA MALAM, WANNAN BAYANI NAKA YANA NUNA MANA CEWA; BA KA TARE DA MU, MU FA QISSAR MUKA 'DAUKO MAKA, A RUBUCE DA LARABCI. KO DAI BA KA KARANTATA DA KYAU BA NE??!
GA NAN ABIN DA AKA CE ANNABI (SAW) YA CE:
وسئل جبرئيل " عليه السلام " أن يسأل ربه العصمة من الناس . و انتظر أن يأتيه جبرئيل بالعصمة من الناس من الله عزوجل . فأخر ذلك إلى ان بلغ مسجد الخيف

SHIN ITA WANNAR ISMA (KARIYA) DA ANNABI (SAW) YAKE NEMA WAJEN ISAR DA WILAYAR ALI (RA), MA KANSA YAKE NEMA NE, KO KUMA WA SAHABBANSA YAKE NEMA, DON KAR SU FITINU, SU HADDASA FITINA A CIKIN MUSLUNCI??
AMMA KAI KA CE: "BA YANA JIN TSORON KADA SU CUTAR DASHI BANE"
ABIN TAMBAYA; SHIN KARIYAR DA YAKE NEMA MA KANSA NE, KO KUMA WA SAHABBANSA??
ALHALI AN CE:
اتاه جبرئيل " عليه السلام " على خمس ساعات مضت من النهار بالزجر والانتهار والعصمة من الناس فقال يا محمد ان الله عزوجل يقرأك السلام ويقول لك : ( يا أيها الرسول بلغ ما انزل اليك من ربك - في علي - وان لم تفعل فما بلغت رسالته والله يعصمك من الناس )
SAI DA AKA TSAWATAR MASA, KUMA AKA KARE SHI DAGA MUTANE...
IN BA MUTANE YAKE TSORON KAR SU CUTAR DA SHI BA, ME YA SA YA NEMI KARIYA DAGA GARESU??

** SA'ANNAN MATSAYIN WILAYAR ALI (RA) A WAJENKU, TA WUCE KOMAI A ADDINI, AMMA DUK DA WANNAN MATSAYI NATA, DA MUHIMMANCI, AMMA A HAKAN UMAR (RA) YA HANA MANZON ALLAH (SAW) RUBUTATA???!
YA KAMATA ACE; MATSAYIN WILAYAR ALI (RA) TA WUCE WANI YA HANA A RUBUTATA!!

(3) AMSA: TO, KA FADA MANA WANI SAKO NE ZAI ISAR WANDA BAI ISAR BA HAR SAI DA YA RAGE SAURA WATANNI UKKU YAYI WAFATI? ......

AMMAR:
WANNAN QISSA TAKU TA NUNA CEWA; ANNABI (SAW) BAI ISAR DA WILAYAR ALI BA, HAR SAI DA YA RAGE WATANNI 3 DA WAFATINSA, SHI YA SA AKA SA SHI DOLE YA ISAR DA WANNAN SAK'O A GHADEER KHUM A RANAR 18 GA ZUL HIJJA, DUK DA CEWA; YANA JIN TSORON ISARWA.
AMMA MUHIMMANCIN WANNAN SAK'O KAM, AI KA FINI SANI.
AMMA TAMBAYARKA TA GABA, WACCE TAKE KAMAR HAKA:
"ME YASA YAKE BUKATAN KARIYA A WANNAN LOKACIN ALHALI TUN FARKO YAYI DA’AWA A CIKIN MUSHRIKAN MAKKA HAR YACE DA ZASU SANYA RANA DA WATA A TAFUKAN HANNAYENSA BA ZAI DAINA BA?"
LALLAI KAI ZAN TAMBAYA, DON HAKA SAI KA BA NI AMSA!!

(4) AMSA: AI A WANNAN RANAR KAFURAI SUN RIGA SUN YAKE KAUNA DA GANIN BAYAN MUSULUNCI .....

AMMAR:
AYAR DA KA KAWO ITA CE TAKE YI MAKA RADDI, TAKE WARWARE MAGANAR DA KA FA'DA. SABODA MUNAFUKAI MA KAFIRAI NE A BISA HAK'IK'A. SA'ANNAN KUMA YAWANSU A CIKIN MUSULMAI BAI KAI SU CI GALBA A KAN MUSULMAI BA, HAR ANNABI (SAW) YA JI TSORON MUNAFUKAI ZA JANYO FITINAR DA ZA TA SA DUKKAN AL'UMMA SU HA'DU A KAN K'IN BIN UMURNIN ALLAH DA MANZONSA. SABODA KUN RUWAITO CEWA; AL'UMMA BA ZA SU HA'DU A KAN 'BATA BA.
إن الله تعالى لا يجمع امتي على ضلالة، ويد الله تعالى مع الجماعة، من شذ شذ إلى النار
DON HAKA HAR YANZU BA KA KAWO MANA DALILIN DA ZAI SA ANNABI (SAW) YA JI TSORON MUTANE BA, YA K'I ISAR DA SAK'ON ALLAH, HAR SAI AN TSAWATAR MASA, HAR SAI AN BA SHI KARIYA BA.

(5) AMSA: DA MUNAFUKAN DA BA’A SANIBA DA MASU RAUNIN IMANI DUK SUNA CIKIN SAHABBAI, AMMA BASA CIKIN MAFI ALKHAIRIN AL’UMMA......

AMMAR:
AI A CIKIN QISSAR BA MUNAFUKAI KAWAI AKA AMBATA CEWA; ANNABI (SAW) YANA JIN TSORO BA, HAR DA MUTANENSA, DAGA BAYA SAI YA AMBACI MUNAFUKAN.
فخشى رسول الله ( صلى الله عليه وآله ) قومه وأهل النفاق والشقاق أن يتفرقوا . ويرجعوا جاهلية لما عرف من عداوتهم وما يبطنون عليه انفسهم لعلي " عليه السلام " من البغضاء .
TO SU WAYE MUTANEN NASA??
DON HAKA WANNAR MAGANA TA K'UNSHI DUKKAN AL'UMMA KENAN. ANA GANIN ZA SU YI RIDDA!!
LALLAI WA'DANNAN AYOYIN SUNA K'ARYATA WANNAN LABARI.
ALLAH YA CE:
كنتم خير أمة أخرجت للناس تأمرون بالمعروف وتنهون عن المنكر وتؤمنون بالله
YA CE:
وكذلك جعلناكم أمة وسطا لتكونوا شهداء على الناس ويكون الرسول عليكم شهيدا

SA'ANNAN GA CAN HADISIN DA GABATAR MAKA:
إن الله تعالى لا يجمع امتي على ضلالة، ويد الله تعالى مع الجماعة، من شذ شذ إلى النار
DUBA MIZANUL HIKMA, DA BIHARUL ANWAR.

(6) AMSA: YA NADA IMAM ALI (A.S) KAMAR YADDA BAYANI YA GABATA, KUMA BAI SANYA ABUBAKAR YA BADA SALLAH BA .......

AMMAR:
1. TUN DA KA CE; ANNABI (SAW) BAI SANYA ABUBAKAR (RA) YA BA DA SALLA BA, TO SAI KA GAYA MANA WANDA YA YI SALLA WA MUTANE A RASHIN LAFIYAN ANNABI (SAW) NA AJALI??
2. A INA NE INDA AKA CE; ANNABI (SAW) YA UMURCI ABUBAKAR (RA) YA KASANCE A CIKIN RUNDUNAR USAMATU BN ZAID (RA)??

(7) AMSA: TIRMIZI YA RUWAITO UMAR YANA TAYA IMAM ALI MURNA AKAN HAKA, DON HAKA SHI YASAN ABIN DA AKE NUFI YA WUCE MASOYI.....

AMMAR:
TO SAI KA KAWO MANA RUWAYAR TIRMIZIY 'DIN SAI MU YI NAZARINTA. SA'ANNAN KUMA KO DA HAKAN YA TABBATA, LALLAI YIN MURNA A KAN HAKA BA YA HUKUNTA CEWA; MA'ANAR KALMAR "MAULA" TA WUCE SOYAYYA. SABODA A CIKINSA AKWAI SHAIDA A KAN CIKAN IMANIN ALIYU (RA). WANNAN KUWA BABBAN ABIN MURNA NE WA MUTUM.

No comments:

Post a Comment