Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Sunday, 7 February 2016

WAI ME YA SA 'YAN SHI'A MAZA SUKE SON AUREN MATA 'YA'YAN AHLUS SUNNA ('YAN DARIQU), BA SA TAKAITA A KAN NASU MATA DA 'YA'YAN?

BAYAN SUN SAN MATANSU 'YAN SHI'A SECOND HANDS NE SABODA MUTU'A, KUMA YANA DAGA CIKIN MANYAN ABIN DA YA SA SUKE SON AUREN 'YA'YAN AHLUS SUNNA ('YAN DARIQU) SABODA TA HAKA SUKE KARA YAWANSU, SUKE SHIGAR DA MATA CIKIN SHI'A. DON DUK WACCE TA AURI DAN SHI'A TO ITA MA KAI TSAYE TA ZAMA 'YAR SHI'A. KUMA ZA TA SHIGAR DA KAWAYENTA DA KANNENTA, DA 'YAN GIDANSU, MATUKAR IN JAHILAI NE, KO KUMA BA SU DAMU DA ADDINI BA. DON TUN TANA AMARCI, MIJIN ZAI KAWO MATA KASET NA WAKOKIN SHI'A, TANA SAWA. KOWA YA SAN A GIDAN AMARYA ANA SA KASET NA KIDE - KIDE DA WAKE - WAKE. TO SAI A YI TA SA IRIN WADANNAN WAKOKI NA SHI'ANCI, TA HAKA KAWAYEN AMARYA, DA KANNENTA ZA SU TA HADDACE WAKOKIN SHI'A, DAGA NAN KAWAI SAI WATA RANA KA GANSU A JERIN GWANON MAULIDIN FATIMA SUNA RAWA SUNA JUYI A KAN TITI.

HAKA YA FARU A WASU KASASHE NA LARABAWA, SUN SHI'ANTAR DA JAMA'AR AHLUS SUNNA MASU YAWA TA HANYAR AURATAYYA. KAMAR KASAR IRAQI, DA BAHRAIN, DA KUWAIT, DA MAKAMANTANSU. WANDA TUN ASALI, AHLUS SUNNA NE MAFI YAWA A WADANNAN KASASHE, AMMA A YAU 'YAN SHI'A SUNA DA RINJAYE A IRAQI, SUN YI YAWA A BAHRAIN, SUN FARA YIN YAWA A KUWAIT.

TO AHLUS SUNNA ('YAN DARIQU, DA 'YAN BA RUWANA), KU YI HATTARA WAJEN BA DA AUREN 'YA'YANKU WA MUTANE. IMMA KA CETO 'YARKA, KO KUMA KA HALAKAR DA ITA.

AMMA AHLUS SUNNA 'YAN SALAFIYYA KAM ('YAN IZALA), INSHA ALLAHU BABU HAUFI A LAMARIN AURATAYYARSU, DON BA SA BA DA AUREN 'YA'YANSU SAI WA MAI GANGARIYAR AQIDA TA SUNNA.

No comments:

Post a Comment