ALKALI YA CE:
IDAN KA FIFITA ABUBAKAR (RA) A KAN ALIYU (AS) TO HAK'IK'A KA K'ASK'ANTA ALIYU (AS).
'BARAWO YA CE:
DUK WANDA YA YI NUFIN K'ASK'ANTA ALIYU (RA) TO LALLAI YA 'BATA, AMMA FIFITA ABUBAKAR (RA) SHI NE BIN SUNNA.
KUMA IN AN BI RA'AYINKA TO DUKKAN WANDA YA FIFITA ALIYU (RA) A KAN FATIMA (RA) DA HASSAN DA HUSSAINI (RA) TO HAK'IK'A ZAI ZAMA WANDA YA K'ASK'ANTAR DA SU.
ALKALI YA CE:
TO AI ANNABI (SAW) YA 'DAUKI ALIYU (AS) A RANAR KARYA GUMAKA.
'BARAWO YA CE:
LALLAI WANNAN FALALA CE GA ALIYU (RA) KUMA BA MA MUSUNTA, AMMA KUMA AI YA 'DAUKI A'ISHA (RA) TANA K'ARAMA, KUMA YA 'DAUKI UMAMATU BNT ABIL ASW BN RABI'EE A KAFA'DANSA.
ALKALI YA CE:
AI ANNABI (SAW) YA CE:
«أنا من علي وعلي مني».
"NI DAGA ALIYU NAKE, ALIYU MA DAGA NI YAKE".
'BARAWO YA CE:
WANNAN MA BA MA KORE SHI, AMMA KUMA AI YA FA'DI HAKA WA ABBAS (RA) MA YA CE:
«أنا من العباس والعباس مني»
"NI DAGA ABBAS NAKE, ABBAS MA DAGA NI YAKE".
SABODA HAKA WACE FALALA ALIYU (RA) YAKE DA SHI A KAN ABBAS (RA) A NAN?
ALKALI YA CE:
AI YA CE WA ALIYU (AS): KAI 'DAN UWANA NE.
'BARAWO YA CE:
YA FA'DI HAKA SAU DA YAWA, AMMA SAI DAI YA FA'DA NE A BISA NUNA MATSAYINSA KO A BISA HAK'IK'A YA FA'DA?
ALKALI YA CE:
YA FA'DA NE A BISA "MAJAZ" (BA HAK'IK'A BA).
'BARAWO YA CE:
TO AI MU DA KU DUKA MUNA RUWAITOWA DAGA ANNABI (SAW) YA CE:
«واشوقاه إلى أخواني الذين يؤمنون بنبوتي ولم يلحقوني ويتمسكون بشريعتي ويصدقوني»
"INA SHAUQIN HA'DUWA DA 'YAN UWANA, WA'DANDA SUKE YIN IMANI DA ANNABTATA ALHALI BA SU HA'DU DA NI BA, KUMA SUNA RIK'O DA SHARI'ATA KUMA SUNA GASKATANI".
KUMA YA CE MA ABUBAKAR (RA):
«أنت أخي ورفيقي وصديقي»
"KAI 'DAN UWANA NE, WANDA YAKE TARE DA NI, KUMA ABOKINA".
SABODA HAKA BA NA GANIN KUNA DA WATA FALALA TA ALIYU (RA) DA ZA KU KAWO MANA FACE MUNA DA IRINTA, HAKA BABU WANI MATSAYI NASA DA ZA KU BAYYANA FACE MUNA DA MAKAMANCINSA, HAKA IDAN KUN CE ALIYU (RA) YA FI KOWA FALALA NE SABODA WA'DANNAN HADISAI SAI MU CE: ANNABI (SAW) YA CE:
«لو كان نبي لكان عمر»
"DA WANI ANNABI ZAI ZO DA UMAR NE".
IN KUMA KUN CE: YA SAMU FALALA CE SABODA JARUMTAKA, TO SAI MU CE: ANNABI (SAW) YA YI SHAIDA WA ZUBAIR (RA) DA ITA.
KUMA YA CE WA HAMZA (RA):
«أسد من أسد الله»
"ZAKI DAGA CIKIN ZAKUNAN ALLAH".
YA CE MA KHALID (RA):
«سيف الله»
"TAKOBIN ALLAH".
A NAN MUKA ZO K'ARSHEN WANNAR TATTAUNAWA, INDA MUKA GA SHI WANNAN ALKALI 'DAN SHI'A SHI YA FI DACEWA YA ZAMA 'BARAWO, SHI KUMA 'BARAWO SHI YA FI DACEWA YA ZAMA ALKALI.
A TAK'AICE WANNAN SHI YAKE TABBATAR MANA DA CEWA; ABUBAKAR (RA) YA FI KOWA FALALA A CIKIN WANNAR AL'UMMA BAN DA MANZONTA (SAW), SABODA K'A'IDAR NAN WACCE TAKE KAMAR HAKA:
إن التفضيل إذا ثبت للفاضل من الخصائص ما لا يوجد مثله للمفضول فإذا استويا وانفرد أحدهما بخصائص كان أفضل وأما الأمور المشتركة فلا توجب تفضيله على غيره.
"ANA FIFITA MUTUM A KAN WANI MUTAM NE IDAN YANA DA WASU MATSAYI DA YA KE'BANTA DA SU WA'DANDA BABU SU A WAJEN 'DAYA MUTUMIN, AMMA IDAN SUKA DAIDAITA A WASU FALALOLI, SAI KUMA 'DAYA DAGA CIKINSU YA KE'BANTA DA WASU MATSAYI TO YA ZAMA SHI NE MAFI FALALA, AMMA MATSAYIN DA YA YI TARAYYA DA WANI KO WASU A CIKINSU BA SU SA A FIFITA SHI A KAN WANINSA".
SABODA HAKA NE MUKE CEWA; ABUBAKAR (RA) YA FI ALIYU (RA) FALALA, SABODA FALALOLIN ABUBAKAR (RA) DA YA YI FICE DA SU, BABU WANDA YA YI TARAYYA DA SHI A CIKINSU, DUKA SUN KE'BANTA NE DA SHI KAWAI, AMMA SHI ALIYU (RA) DUKKAN FALALOLINSA DA YA YI FICE DA SU, WANI YI YI TARAYYA DA SHI A CIKINSU, BAI KA'DAITA DA SU BA, BA SU KE'BANTA DA SHI KA'DAI KAWAI BA, KAMAR YADDA HAKAN YA BAYYANA MANA A CIKIN WANNAR TATTAUNAWAR.
No comments:
Post a Comment