Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Sunday, 7 February 2016

SHUBUHOHIN 'YAN SHI'A A KAN MATSAYIN SAHABBAI (2)

NASIRU YA CE:
"WANNAN SHI AKE KIRA DA LABARIN SHIFCIN GIZO SARKIN KARYA".


AMMAR:
WANNAN DUKA DAMUWARKA CE, RASHIN GAYA MAKA WANDA AKA YI TATTAUNAWAR NAN DA SHI, KO WAJEN DA AKA YI TA, BA YA SA TA ZAMA K'ARYA. SA'ANNAN KUMA AI DA MA, MU A WAJENKU AI BA ZA MU TA'BA ZAMA MASU GASKIYA BA. ABU MAI MUHIMMANCI SHI NE SAK'ON DA ITA WANNAR TATTAUNAWA TSAKANIN 'DAN SHI'A DA NASIBI TAKE 'DAUKE DA SHI. MU DAI AN HASKA MANA MUNAFUKAI MAK'IYA SAHABBAI, KUMA MUN GANESU DUKA BANGARORIN GUDA 2.

NASIRU YA CE:
"WATO DUK INDA BAWAHABIYE YAKE SAI YA NUNA KANSA CEWA SHI KWARE WAJAN YIN KWANGE ACIKIN RIWAYA, MEYASA KAYI COJE KAYANKE YANDA RIWAYAR TAKE?"

AMMAR:
TO BARI MU GANI, TSAKANIN WAHABIYAWA DA 'YAN SHI'A SU WANE NE 'YAN KWANGE, 'YAN COGE, MASU ALGUS A CIKIN RIWAYA?
تفسير القمي - (13 / 12)
ابى عبدالله قال لما كان رسول الله صلى الله عليه وآله في الغار قال لفلان كانى انظر إلى سفينة جعفر في اصحابه يقوم في البحر وانظر إلى الانصار محتسبين في افنيتهم فقال فلان وتراهم يارسول الله قال نعم قال فارنيهم فمسح على عينيه فرآهم (فقال في نفسه الآن صدقت انك ساحر ط) فقال له رسول الله انت الصديق

WANNAR ITA CE RIWAYAR "AL- QUMMIY".
CUWA – CUWAR DA TAKE CIKIN WANNAR RIWAYAR GA TA NAN KAMAR HAKA:
1. AN GOGE SUNAN ABUBAKAR (RA), SAI ACE: "FULAAN":
لفلان، فلان.
2. DON ME YA SA AKA SA WANNAR JUMLAR A CIKIN BAKA 2 ( - ):
(فقال في نفسه الآن صدقت انك ساحر ط)
MA'ANA KENAN WANNAN DAGA BAYA NE WANI YA ZO YA CUSA WANNAR MUMMUNAR KALMAR.
3. ABIN DA ZAI NUNA MAKA CEWA HANUN DA YA YI WANNAN JAGWALGWALE A CIKIN WANNAR RIWAYA BA SHI DA BASIRA SHI NE; YA MANTA BAI GOGE KALMAR "SIDDIQ" BA:
انت الصديق
TUN DA WANNAR MAGANAR ANNABI (SAW) CE, TO ABIN TAMBAYA SHI NE; TA YAYA ANNABI (SAW) ZAI GASKATA SHI A KAN WACCAR MUMMUNAR MAGANA DA ABUBAKAR (RA) YA FA'DA A CIKIN ZUCIYARSA:
صدقت انك ساحر
-WAI- "NA GASKATA LALLAI KAI MATSAFI NE".
A NAN 'DAYAN UKU:
(a) IMMA ANNABI (SAW) YA SAN YA FA'DI WANNAR MAGANA TA KAFIRCI, AMMA YA GASKATA SHI A KAN HAKA, WANNAN AIBANTA ANNABI (SAW) NE, SABODA A MATSAYINSA NA MANZON ALLAH (SAW), AMMA YAKE GASKATA MUTANE A KAN KAFIRCI.
SA'ANNAN KUMA GASKATA SHI DA YA YI, YA NUNA CEWA; ANNABI (SAW) YA YARDA DA CEWA; ABIN DA YA ZO DA SHI SIHIRI NE TSAFI NE, SAI YA ZAMA ASHE, ANNABIN (SAW) BA SHI DA BANBANCI DA KAFIRAI DA SUKE SIFFANTA MANZANCINSA DA AL- QUR'ANI DA TSAFI, WANDA WANNAN KAFIRCI NE. DA WANNAN ZA KA FAHIMCI WANI MUNAFUKI ZINDIQI MAI SON SUKAN ANNABTA DA MANZANCIN ANNABI (SAW) NE YA YI WANNAN 'BARNA.
(b) IMMA KUMA ANNABI (SAW) BAI SAN ABUBAKAR (RA) YA FA'DI WANNAR MAGANA A CIKIN ZUCIYARSA BA, DON HAKA ASHE ANNABI (SAW) BAI SAN GAIBI BA, DON HAKA RAFIDHA 'YAN SHI'A SUN WARWARE KANSU, DA SUKE DA'AWAR SANIN GAIBI WA IMAMANSU, SABODA TUN DA ANNABI (SAW) BAI SAN GAIBI BA, TO TA YAYA WANI, -WAI- SHI IMAMI ZAI SAN GAIBI??!
TUN DA ANNABTA CE ASALIN IMAMAR DA AKE RAYAWA!
SUBHANALLAH, KA DUBA IRIN KAFIRCI DA TUFKA DA WARWARA DA WANNAR MAGANA TA 'YAN SHI'A TA JANYO MUSU.
AI NI DA MA NA RUFA MUKU ASIRI NE, DON MU TAK'AITA ABIN, AMMA SAI KA NEMI A TONA ASIRIN DA KE CIKIN WANNAN HADISI NAKU NA MA'ASUMAI.
TO IN DAI IRIN WANNAR MAGANA CE MAGANAR MA'ASUMAI, TO SAI MU CE: ALLAH WADAI DA MAGANGANUN IRIN WA'DANNAN MA'ASUMAN NAKU.
(c) IMMA KUMA YA ZAMA WANNAR JA'IRAR MAGANA:
(فقال في نفسه الآن صدقت انك ساحر ط)
-WAI- "YA CE A CIKIN RANSA: KA YI GASKIYA LALLAI KAI MATSAFI NE".
WANI MUNAFUKI ZINDIQI MARAS BASIRA NE YA ZO YA CUSATA, HAR YA JINGINATA GA MA'ASUMAI. WANDA NI A GANINA HAKA ABIN YAKE, SHI YA SA BAN WAIWAICETA TUN FARKO BA.
DON HAKA SAI MALAM NASIRU YA ZA'BI 'DAYA DAGA CIKIN WA'DANNAN FISKOKI GUDA UKU.
MUNA JIRANKA.
ABIN DA ZAI K'ARA TABBATAR MAKA CEWA; WANI ZINDIQI NE YA K'ARA WANNAR K'AZAMAR MAGANAR SHI NE; A WASU LITTATAFAN SAI AKA BAYYANA SUNAN ABUBAKAR (RA) A INDA A BAYA AKA CIRE SUNAN, SAI AKA CE: "FULANUN", DUBA WANNAR RIWAYAR, KAMAR YADDA AKA 'DAUKOTA DAGA "TAFSIRUL QUMMIY" KAFIN A CIRE SUNAN ABUBAKAR (RA):
بحار الأنوار - العلامة المجلسي - (19 / 53)، (31 / 589)
10 - فس: أبي، عن بعض رجاله، رفعه إلى أبي عبد الله عليه السلام قال: لما كان رسول
الله صلى الله عليه وآله في الغار قال لابي بكر: كأني أنظر إلى سفينة جعفر في
أصحابه (4) يعوم في البحر. وأنظر إلى الانصار محتبين في أفنيتهم، فقال أبو بكر:
وتراهم (5) يا رسول الله ؟ قال: نعم، قال: فأرنيهم، فمسح على عينيه فرآهم، فقال في
نفسه: الآن صدقت أنك ساحر، فقال له رسول الله صلى الله عليه وآله: أنت الصديق. (6)

DON ME YA SA A RIWAYAR FARKO AKA CIRE SUNAN ABUBAKAR
(RA), AMMA A NAN KUMA SAI GA SUNAN A FILI?!
ALLAH YA RABA MU DA IRIN WANNAN COGE, KAWAI DON A KAFIRTA SHUGABAN SIDDIQAI KUMA SHUGABAN WALIYYAI BAYAN ANNABAWA, WATO ABUBAKAR AL- SIDDIQ (RA), KAWAI SAI RESHE YA JUYE DA MUJIYA, SAI WANDA YA YI CUWACUWAR SAI SHI YA FA'DA CIKIN KAFIRCIN.

A TAK'AICE DAI, WANNAR RIWAYA TA 'YAN SHI'A TANA TABBATAR DA CEWA; ABUBAKAR (RA) SHI NE SIDDIQI, DON HAKA DAGA ANNABI (SAW) SAI SHI A FALALA DA DARAJA, DA IMAMANCI A CIKIN WANNAR AL'UMMA, SHI YA SA ALLAH YA SA YA ZAMA KHALIFANSA.


NASIRU YA CE:
"HABA AMMAR DAURE MANA KA KAWO MANA ISNADIN WANNAN KISSA DAKA KAWO DAGA NAN SAI KAGA IRIN RAGAR-GAZAKA DA ZAMUYI AKAN WANNAN KISSA DAKA KAWO.".


AMMAR:
AI KAI YA KAMATA KA BINCIKO DA KANKA IN HAR DA GASKE KA ISA KA YI RAGARGAZAR. KUMA AI KO KA RAGARGAJETA, DA MA A RAGARGAJE TAKE, SABODA KOWA YA SANI; KUSAN DUKKAN RIWAYOYINKU NA K'ARYA NE, SHI YA SA BA SU DA ISNADI. KA DUBA KUNDINKU "NAHJUL BALAGA" MANA KA GANI, DUK DA MATSAYINSA A WAJENKU?!
SA'ANNAN KUMA WATA K'A'IDA DA BA KA SANI BA ITA CE:
عدم الدليل المعين لا يستلزم عدم المدلول المعين

MA'ANA; TUN DA KA YARDA DA SAURAN RIWAYOYIN DA NA KAWO, WASU DAGA "NAHJUL BALAGA", A KAN FALALOLIN ABUBAKAR (RA) DA UMAR (RA) DA SAURAN SAHABBAI, AI BUK'ATA TA BIYA.
DON HAKA KO BA KA RAGARGAJI WANNAR RIWAYAR TAKU BA, DA MA KUSAN DUKKAN RIWAYOYINKU ABIN RAGARGAZA NE, SABODA DUKA NA K'ARYA NE.
TO TA INA KUKE 'DAUKAN ADDININKU NE???!
ADDININ DA AKA CE; 9 BISA 10 NA RIWAYOYINSA DUKA K'ARYA NE!!

NASIRU YA CE:
"ANNABI (S.A.W.) YAYI BAYANIN ABINDA YAKE NUFI DASHI WANNAN JI DA GANI DA KUMA ZUCIYA, MA'ANA SHINE ZA'A TAMBAYESU AGAME DA WASIYIN ANNABI SHINE IMAM ALI (A)".

AMMAR:
KA GA WANNAR FASSARA TAKU BABU MAI YARDA DA ITA SAI MARAS BASIRA. SABODA ASALIN MAGANAR ANA DANGANTATA DA WANNAR AYAR CE DA TAKE CIKIN SURATUL ISRA'I:
{وَلَا تَقْفُ مَا لَيْسَ لَكَ بِهِ عِلْمٌ إِنَّ السَّمْعَ وَالْبَصَرَ وَالْفُؤَادَ كُلُّ أُولَئِكَ كَانَ عَنْهُ مَسْئُولًا} [الإسراء: 36]
MA'ANAR AYAR ITA CE: "KAR KA BI MAGANAR DA BA KA DA ILMI A KANTA, LALLAI JI DA GANI DA ZUKATA KOWANE 'DAYA DAGA CIKIN WA'DANNAN YA KASANCE ABIN TAMBAYA NE GAME DA SHI".
TO DON HAKA, A KAN SU WA ZA AYI TAMBAYA A CIKIN WANNAR AYAR?
A KAN WA'DANNAN GA'BO'BI; "AL- SAM'U", "AL- BASARU", "AL- FU'ADU". ZA A TAMBAYI MUTUM A KAN WA'DANNAN GA'BO'BI NASA GUDA UKU (3).
MALAMAN TAFSIRIN SHI'A SUKA CE: WANNAN ISHARA:
أولئك
YANA KOMAWA NE KAN WA'DANCAN GA'BO'BI, KO AIYUKAN DA MUTUM YA AIKATA DA SU. AL- 'DABARASIY YA CE:
تفسير مجمع البيان - الطبرسي - (6 / 223)
فأولئك كما يكون إشارة إلى العقلاء يكون إشارة إلى غيرهم و قوله « كان عنه مسئولا » الهاء تعود إلى كل أي يسأل عن استعمال هذه الأشياء و إن شئت كان الهاء يعود إلى الإنسان أي يسأل عن الإنسان فيما استعمل هذه الأشياء و يكون في مسئولا ضمير يعود إلى كل و قدره أبو علي أن أفعال السمع و البصر و الفؤاد كل أفعال أولئك

A TAK'AICE DAI, MUTUM NE ABIN TAMBAYAN.
SA'ANNAN YA CE:
تفسير مجمع البيان - الطبرسي - (6 / 224)
« إن السمع و البصر و الفؤاد كل أولئك كان عنه مسئولا » معناه أن السمع يسأل عما سمع و البصر عما رأى و القلب عما عزم عليه ذكر سبحانه السمع و البصر و الفؤاد و المراد أن أصحابها هم المسئولون و لذلك قال « كل أولئك » و قيل بل المعنى كل أولئك الجوارح يسأل عما فعل بها قال الوالبي عن ابن عباس يسأل الله العباد فيما استعملوها و روى علي بن إبراهيم في تفسيره عن أبيه عن الحسن بن محبوب عن أبي حمزة الثمالي عن أبي جعفر (عليه السلام) قال قال رسول الله (صلى الله عليهوآلهوسلّم) لا يزول قدم عبد يوم القيامة بين يدي الله عز و جل حتى يسأله عن أربع خصال عمرك فيما أفنيته و جسدك فيما أبليته و مالك من أين كسبته و أين وضعته و عن حبنا أهل البيت

ZA A YI TAMBAYA NE A KAN WA'DANCAN GA'BO'BI GUDA 3, BA –WAI – SU ZA A TAMBAYA BA.
TO KA GA KENAN, IN KUNA SO RIWAYARKU TA DACE DA WANNAR AYAR, TO RIWAYAR TANA NUNI NE A KAN CEWA; ZA A TAMBAYI BAWA A KAN ABUBAKAR (RA) DA UMAR (RA) DA USMANU (RA) A LAHIRA, IN WANNAN YA TABBATA, TO KU 'YAN SHI'A KUN SHIGA UKU, DON A KAN WA'DANNAN SAHABBAI GUDA 3 WUTA ZA KU SHIGA.
DON HAKA, IMMA YA ZAMA ZA A YI TAMBAYA NE A KAN KHALIFOFIN ANNABI (SAW) GUDA UKU (3), AMMA SAI WANI HANU YA YI CANJE – CANJE A CIKIN RIWAYAR DON KAR TA NUNA FALALAR WA'DANNAN SAHABBAI GUDA 3, KO KUMA YA ZAMA AKWAI TUFKA DA WARWARA A CIKINSA, SABODA AYAR DA TA DACE DA "TASHBIHIN" DA ANNABI (SAW) TA SA'BA WA MAGANAR TAMBAYA A KAN WILAYA DA WANI YA K'ARA.
'YAN SHI'A SAI KU K'ARA MANA BAYANI!

A GASKIYA, RIWAYOYIN 'YAN SHI'A MARAS BASIRA NE YA K'IRK'IRESU, DAGA KA JISU ZA KA GA TUFKA DA WARWARA A CIKINSU.


NASIRU YA CE:
"AI IDAN KANA NEMAN MAKIYIN MUTANAN MADINA IDAN AKACE MU'AWIYA DA 'DANSA YAZIDU AN GAMA.".
KUMA YA CE:

" SHIKUWA 'DANSA YAZIDU BUKHARI YAKO RIWAYA ACIKIN LITTAFINSA NA BUKHARI ANNABI (S.A.W) YANA CEWA HALAKAR AL'UMATA ABISA HANNUN YARA KAN-KANA. WANNAN YASA ABU-HURAIRA YAKE ADDU'AR KADA ALLAH YAKAISHI SHEKARA TA SITTIN SABODA GADA WANNAN SHEKARAR HALAKAR ZATA SOMA, SAI GASHI MU'AWIYA YA NADA 'DANSA YAZIDU ACIKIN WANNAN SHEKARA.".

AMMAR:
AI DUK ABIN DA MU'AWIYA (RA) DA YAZIDU SUKA YI AN GAFARTA MUSU.
أم حرام: أنها سمعت النبي صلى الله عليه وسلم، يقول: «أول جيش من أمتي يغزون البحر قد أوجبوا»، قالت أم حرام: قلت: يا رسول الله أنا فيهم؟ قال: «أنت فيهم»، ثم قال النبي صلى الله عليه وسلم: «أول جيش من أمتي يغزون مدينة قيصر مغفور لهم»، فقلت: أنا فيهم يا رسول الله؟ قال: «لا»

SHI YA SA IBNU KASIR YA CE:
البداية والنهاية ط هجر (19/ 8 - 9)
فكان الأمر كذلك في سنة سبع وعشرين، مع معاوية في خلافة عثمان، حين استأذن عثمان في غزو قبرس، فأذن له فركب المسلمون المراكب إليها وفتحوها قسرا، وتوفيت أم حرام في هذه الغزوة، وكانت أم حرام مع زوجها عبادة بن الصامت، وكان مع معاوية في هذه الغزوة زوجته فاختة بنت قرظة. وأما غزوة البحر الثانية فكانت في سنة ثنتين وخمسين في أيام معاوية أيضا، غزاها ابنه يزيد ومعه الجنود فدخلوا إلى القسطنطينية، وكان معه في هذا الجيش جماعة من أعيان الصحابة، منهم أبو أيوب الأنصاري خالد بن زيد، رضي الله عنه، فمات هنالك وأوصى إلى يزيد بن معاوية، أن يدفنه تحت سنابك الخيل، وأن يوغل به إلى أقصى ما يمكن أن ينتهي به إلى نحو جهة العدو، ففعل ذلك.

DON HAKA WANNAN HADISIN YANA NUNA CEWA; MU'AWIYA (R) 'DAN ALJANNA NE, A DALILIN WANNAN YAK'I, SA'ANNAN KUMA YANA NUNI A KAN GAFARTA MA 'DANSA YAZIDU.
DON HAKA INA GANIN DUK ABIN DA ZA KA AMBATA NA LAIFIN MU'AWIYA (RA) KO 'DANSA YAZIDU, TO BA SHI DA WANI AMFANI, SABODA ALLAH YA YI MUSU ALKAWARIN ALJANNA DA GAFARA, ALHALI ALLAH BA YA KARYA ALKAWARINSA.
DON HAKA MU BA MU CE BA SU AIKATA LAIFUKA BA, AMMA DAI ALLAH YA YI MUSU ALKAWARIN GAFARA.

DON HAKA DAI, DUK 'DAN SHI'A MUNAFUKI NE, SABODA YANA K'IN AL- ANSAR, KAMAR YADDA NASIBI YAKE MUNAFUKI, SABODA YANA K'IN ALIYU (RA).
AMMA SHI AHLUS SUNNA, YANA SON DUKKAN SAHABBAI, KUMA DAGA CIKINSU AKWAI AL- ANSAR, DA KUMA ALIYU (RA), DUKA YANA SONSU, DON HAKA SHI MUMINI NE, SABODA WA'DANNAN HADISAI GUDA 2:
1- «آية الإيمان حب الأنصار، وآية النفاق بغض الأنصار»

"ALAMAR IMANI ITA CE SON ANSAR, ALAMAR MUNAFURCI ITA CE K'IN ANSAR".
2- NA BIYU:
والذي فلق الحبة، وبرأ النسمة، إنه لعهد النبي الأمي صلى الله عليه وسلم إلي: «أن لا يحبني إلا مؤمن، ولا يبغضني إلا منافق»

"ANNABI (SAW) YA CE MA ALIYU (RA): BABU MAI SONA SAI MUMINI, KUMA BABU MAI K'INA SAI MUNAFIKI".


NASIRU YA CE:
" HANKALI BAZAI TABA YARDA DACEWA MUTUM YAYI HIJIRA DAGA WANI GARI ZUWA GARIN MADINA AMMA WAI ACE YANA ZAGIN ANNABI (S.A.W)".


AMMAR:
IN HANKALIN 'DAN SHI'A BA ZAI 'DAUKA BA, BA ABIN MAMAKI BA NE, AMMA SHI KAM AHLUS SUNNA HANKALINSA ZAI IYA 'DAUKA, SABODA BABU "GILLU"; HASADA DA BAK'IN CIKI DA MUNGUN NUFI GAME DA SAHABBAN ANNABI (SAW) A CIKIN ZUCIYARSA.
ALLAH NE YA CE:
والذين جاءوا من بعدهم يقولون ربنا اغفر لنا ولإخواننا الذين سبقونا بالإيمان ولا تجعل في قلوبنا غلا للذين آمنوا ربنا إنك رءوف رحيم

SABODA ZAI IYA YIWUWA MUTUM YA MUSLUNTA AMMA YA ZAMA IMANI BAI SHIGA ZUCIYARSA BA, SABODA GIRMA DA DA'DEWA DA YA YI A KAN KAFIRCI, AMMA KUMA SAI DAGA BAYA IMANIN YA YI K'ARFI A CIKIN ZUCIYARSA.
ALLAH YA CE:
قالت الأعراب آمنا قل لم تؤمنوا ولكن قولوا أسلمنا ولما يدخل الإيمان في قلوبكم

DON HAKA MU HANKALINMU YA KAMA SOSAI, CEWA; HAKA ZAI IYA FARUWA DA ITA MAHAIFIYAR ABU HURAIRA (RA), SABODA RAUNIN MUSLUNCINTA A FARKO. SHI YA SA ABU HURAIRA (RA) YA NEMI ANNABI (SAW) DA YA YI MATA ADDU'A, SAI KUWA ALLAH YA AMSA ADDU'AR TASA, SABODA ALLAH MAI RAHAMA NE GA BAYINSA, KUMA YA AIKO ANNABI (SAW) A MATSAYIN RAHAMA GA DUKKAN HALITTU.

NASIRU YA CE:
" -3- WAI YAYA SUNAN ITA WANNA MAHAFIYA TASA YAUSHE KUMA TA MUTU INANE KABARINTA?".

AMMAR:
ZA MU BA KA AMSAR WANNAR TAMBAYA CE IDAN KA GINA WANI HUKUNCI A KANTA.

NASIRU YA CE:
" -4- YAYA AKAYI WANNAN MAHAIFIYAR ABU-HURAIRA TA MALLAKI GIDA KAMAR YANDA ABU-HURAIRA YAFADA AMMA SAI GASHI ABU-HURAIRA ANA KIDANYASHI DAGA CIKIN "AHLUS'SUFFAH" WATO MUTANAN DABASU MALLAKI KODA TUBALI BA?".
" -5- MEYASA WANNAN MAHAIFIYA TA ABU-HURAIRA BAZATA KARASHI KODA ASORAN GIDANTA YARIKA KWANA AMAIMAKON TAFIYA DAYAKEYI YANA KWANAN CIKIN MASALLACIN ANNABI (S.A.W.) SABODA RASHIN MUHALLI."
" -6- MEYASA ABU-HURAIRA YAKE RASA ABINCIN DAZAYACI WAKE BAIWA MAHAIFIYARSA ABINCIN DAZATACI?"

AMMAR:
WANNAR TAMBAYAR MA KAMAR TA BAYANTA TAKE.
IN KUMA INKARIN MALLAKAR GIDAN DA TAKE DA TA YI KAKE YI, ALHALI SHI ABU HURAIRA (RA) BAI MALLAKA BA, TO SAI MU CE; WANNAN INKARIN ABIN DA YA TABBATA A SHARI'A DA FITIRA DA HANKALI DA WAQI'I NE. SABODA SHARI'A TA TABBATAR MANA DA CEWA; RABA ARZIKI A TSAKANIN BAYI FALALA CE TA ALLAH, YANA BA DA DUKIYA NE GA WANDA YA GA DAMA A CIKIN BAYINSA, SAI YA BAI MA 'DA DUKIYA YA HANA UBA, KUMA "BIL AKS". WANNAN ABU NE TABBATACCE A SHARI'A DA FITIRA DA HANKALI DA WAQI'I. ALLAH YA CE:
{أهم يقسمون رحمة ربك نحن قسمنا بينهم معيشتهم في الحياة الدنيا ورفعنا بعضهم فوق بعض درجات ليتخذ بعضهم بعضا سخريا}
YA CE:
والله فضل بعضكم على بعض في الرزق

BABU MAI INKARIN WANNAN SAI MARAS HANKALI, MAI K'ARAMIN K'WAK'ALWA.


NASRU YA CE:
" AMMA SAI GASHI DAKANKA KA KAWO AYA WADDA TAKE NUNI DACEWA WADANDA SUKAYI IMANIN NE SUKAYI RIDDA HARMA ABUBAKAR YA YAKESU. KAGA ANAN KENAN BA DUKA SAHABBAI BANE SUKAYI IMANI BA, SABODA AN SAMI WADANDA SUKAYI RIDDA ACIKINSU ".


AMMAR:
TA YAYA ZA ACE; MUTUM YA YI RIDDA, ALHALI BAI YI IMANI BA?!
AI WANDA YA YI IMANI NE YAKE YIN RIDDA, BA WANDA DA MA CAN BAI YI IMANI BA.
ABIN DA KA KASA GANEWA SHI NE, SUNAN "SAHABI", YANA DA ALAK'A NE DA SIFA, DAGA ZARAR WANNAR SIFA TA GUSHE, TO SHI MA SUNAN YA GUSHE. DON HAKA AYAR TANA MAGANA NE A KAN WANDA YA TABBATA A KAN IMANINSA, WANNAN SHI NE SAHABI. AMMA DAGA ZARAR YA YI RIDDA, TO YA FITA DAGA CIKIN AYAR, SABODA YA FITA DAGA CIKIN SUNAN "SAHABI", KAMAR YADDA YA FITA DAGA CIKIN MUSLUNCI.
DON HAKA, IN YA HALATTA A KIRA WANDA YA YI RIDDA DA SUNAN MUSULMI, TO YA HALATTA A KIRA WANDA YA YI RIDDA DAGA CIKINSU DA SUNAN "SAHABI"!!

MISALI; IN A DA NA TA'BA YIN SHI'A, HAR ANA KIRANA 'DAN SHI'A, SHIN A YANZU ZA KA KIRANI DA 'DAN SHI'A?
KUMA SHIN HAR YANZU RIWAYOYIN DA SUKA ZO DAGA MA'ASUMAI NA FALALAR 'DAN SHI'A SUNA AIKI A KAINA, SHIN INA CIKINSU?
فما لهؤلاء القوم لا يكادون يفقهون حديثا؟!

NASIRU YA CE:
" LALLE KUWA ALLAH DA ANNABINSA BASA SON KAFIRAI DAGA CIKIN SAHABBAI".

AMMAR:
TUFKA DA WARWARA!!
AI WANNAR MAGANA TA BA DA DARIYA WA MASU HANKALI.
AI KOWA YA SAN BABU KAFIRI A CIKIN MUSULMAI, BARE KUMA A CIKIN SAHABBAI. SABODA KOWANE SAHABI MUSULMI NE, AMMA BA KOWANE MUSULMI NE YAKE SAHABI BA.
TO WANNE YA FI FA'DI?
TO SHI KAFIRI BAI SHIGA CIKIN DA'IRAR MUSLUNCI MAFI FA'DI BA, TA YAYA ZAI SHIGA CIKIN DA'IRAR "SAHIBANCI" DA'IRA TSUKAKKIYA?!
A TAK'AICE; MUTUM BA YA ZAMA SAHABI HAR SAI YA CIKA SHARU'DA GUDA 3:
(a) HA'DUWA DA ANNABI (SAW).
(b) IMANI DA SHI, (DON HAKA MUNAFUKAI BA SAHABBAI BA NE).
(c) MUTUWA A KAN IMANI, (DON HAKA WANDA YA YI RIDDA, HAR YA MUTU, TO SHI BA SAHABI BA NE).

NASIRU YA CE:
" SANNAN KUMA BUKHARI YAKAWO HADISI ARANAR LAHIRA ANNABI (S.A.W.) ZAICE AYI NESA DA SAHABBAN DASUKA FARAR DA WANI ABU ABAYNSA :

« فَأَقُولُ إِنَّهُمْ مِنِّى . فَيُقَالُ إِنَّكَ لاَ تَدْرِى مَا أَحْدَثُوا بَعْدَكَ . فَأَقُولُ سُحْقًا سُحْقًا لِمَنْ غَيَّرَ بَعْدِى »"

AMMAR:
A BISA BAYANIN SHARU'DA DA SUKA GABATA, WA'DANNAN BA SAHABBAI BA NE, WA'DANDA SUKA YI RIDDA NE, HAR SUKA MUTU A KAN RIDDA.

NASIRU YA CE:
SAI GA SAHABI DABAKINSA YANA BADA SHEDAR SUN FARAR ABAYAN ANNABI (S.A.W) :
لَقِيتُ الْبَرَاءَ بْنَ عَازِبٍ - رضى الله عنهما - فَقُلْتُ طُوبَى لَكَ صَحِبْتَ النَّبِىَّ - صلى الله عليه وسلم - وَبَايَعْتَهُ تَحْتَ الشَّجَرَةِ . فَقَالَ يَا ابْنَ أَخِى إِنَّكَ لاَ تَدْرِى مَا أَحْدَثْنَا بَعْدَهُ .

AMMAR:
MA'ANAR KALMAR "AHDATHUU" BA SHI NE A NAN BA, SABODA KALMAR "AHDATHA" TANA 'DAUKAR NAU'O'IN AIYUKA DABAN – DABAN, TA KAN ZO DA MA'ANAR RIDDA DA KAFIRCI, KUMA TA KAN ZO DA MA'ANAR BIDI'A, SA'ANNAN TA KAN ZO DA MA'ANAR AIKATA KABA'IRA. SABODA MA'ANAR KALAMAR "HADATH" SHI NE FARUWAN ABU. DAGA ZARAR KA AIKATA AIKI YA ZAMA "HADATH", SABODA KAFIN KA YI AIKIN BABU SHI.
1. DON HAKA HADISIN DA KA KAWO YANA MAGANA NE A KAN RIDDA, SHI YA SA YA ZO A WATA RIWAYAR KAMAR HAKA:
صحيح البخاري (4/ 139)
عن ابن عباس رضي الله عنهما، عن النبي صلى الله عليه وسلم، قال: " إنكم محشورون حفاة عراة غرلا، ثم قرأ: {كما بدأنا أول خلق نعيده وعدا علينا إنا كنا فاعلين} [الأنبياء: 104]، وأول من يكسى يوم القيامة إبراهيم، وإن أناسا من أصحابي يؤخذ بهم ذات الشمال، فأقول أصحابي أصحابي، فيقول: إنهم لم يزالوا مرتدين على أعقابهم منذ فارقتهم، فأقول كما قال العبد الصالح ": {وكنت عليهم شهيدا ما دمت فيهم فلما توفيتني} [المائدة: 117]- إلى قوله - {العزيز الحكيم} [البقرة: 129]

KA GA SAI YA CE:
إنهم لم يزالوا مرتدين...
"BA SU GUSHE BA SUNA MASU RIDDA…".
DON HAKA YA KAMATA KA SAN K'A'IDAR FAHIMTAR NASSI SHI NE KA HA'DA DUKKAN LAFUZANSA DA RIWAYOYINSA, SAI KA FAHIMCI MA'ANARSA.
2. SHI KUMA ATHARIN DA KA KAWO NA BARA'U (RA) SHI KUMA YANA NUFIN AIKATA KABA'IRA NE, SHI YA SA IBNU HAJAR (R) YA CE:
يشير إلى ما وقع لهم من الحروب وغيرها فخاف غائلة ذلك
YAKUKUWAN DA SUKA YI NE A TSAKANINSU, KUMA DUKKANSU TARE DA ALIYU (RA) AKA YI TA YI.
IN KO HAKA NE, TO KENAN ALIYU (RA) MA ZA A KORE SHI DAGA TAFKIN MANZON ALLAH (SAW) A RANAR LAHIRA.
3. "AHDATHA" YA KAN ZO DA MA'ANAR BIDI'A:
«من أحدث في أمرنا هذا ما ليس فيه، فهو رد»

DON HAKA YA KAMATA A RINK'A LURA DA KYAU.


NASIRU YA CE:
"AWAJAN BUKHARI DA MUSLIM SUN RAWAITO CEWA ALOKACINDA UMAR YACEWA ANNABI YAYI MASA IZINI DAYA SARE WUYAN WANNAN MUNAFUKI WATO IBN UBAYYIN, SAI ANNABI YACE KYALESHI KADA MUTANE SUCE MUHAMMADU YANA KASHE SAHABBANSA.".


AMMAR:
HABA MALAM NASIRU KA LURA MANA, CEWA AKA YI:
" KADA MUTANE SUCE".
WA'DANNE MUTANE KENAN?
MUMINAI AKE NUFI, KO JAHILAI, KO MUNAFUKAI, KO MUSHRIAKAI?
NI DAI NA YI IMANIN CEWA; MUMINAI BA ZA SU TA'BA CEWA KOMAI BA GA ABIN DA ANNABI (SAW) YA AIKATA, DON HAKA BA MUMINAI YAKE NUFI BA.
AMMA IN JAHILI YA CE; IBNU UBAYYI SAHABI NE, TO BABU MAMAKI. HAKA IN MUNAFUKAI DA KAFIRAI SUN FA'DA.
SHI YA SA HAR YAU, MUNAFUKAN ZAMANIN ANNABI (SAW) SAHABBAI NE A WAJEN JAHILAI DA MUNAFUKAI DA KAFIRAI NA WANNAN ZAMANI.
DON HAKA SAI KA BINCIKO MANA WASU MUTANE AKE NUFI?

NASIRU YA CE:
"KADAINA CEWA DUKAN SAHABBAI MASU IMANI NE ALHALI KUWAKUNCE ABUBAKAR YA YAKI SAHABBAN DASUKAYI RIDDA."

AMMAR:
TA YAYA ZAN DENA FA'DA, ALHALI NI BA JAHILI BA, KUMA BA MUNAFUKI BA, KUMA BA KAFIRI BA?!

NASIRU YA CE:
" TO GASHI ANAN HUZAIFA SHABI YAYIWA SAHABI 'DAN UWANSA SAHABI USMAN BN AFFAN TAQIYYA HAR DA RANTSUWA??? ANYI WALKIYA!!!".

AMMAR:
WA YA KIRA WANNAN DA SUNAN TAQIYYA??!

NASIRU YA CE:
" YAYA AKAYI MASHAYIN GIYA YASAMI WANNAN MUKAMI AMMA UMAR BAI SAMU BA?"

AMMAR:
ME UMAR (RA) YA RASA?
UMAR (RA) YA RASA BA DA TUTA NE, DA NA'DIN JAGORANCIN TAWAGAR YAK'I, AMMA RASHIN BA SHI TUTA BA YA LAZIMTA YA ZAMA BA YA SON ALLAH DA MANZONSA, SABODA GA SHI ANNABI (SAW) YA YI SHEDA DA HAKAN GA WANDA YA SHA GIYA, ALHALI A K'AIDA TA HANKALI, WANDA BAI SHA GIYA BA SHI YA FI CANCANTAR WANNAR SHEDAR, MATUK'AR BABU WANI ABU DA ZAI HANA SHI SAMUNTA. SHI YA SA ALLAH YA YI SHEDA GA KOWANE MUMINI:
والذين آمنوا أشد حبا لله

NASIRU YA CE:
" SANNAN KUMA BAM-BANCI DANA IMAM ALI (A) SHI ANNABI YACE DASHI ALLAH DA MANZONSA SHIMA SUNA SONSA SABANIN WANNAN MASHAYI CEWA AKAYI SHI YANA SON ALLAH DA MANZONSA."

AMMAR:
AI DUK WANI MUMINI MA ALLAH YANA SONSA, DON HAKA IN KA YARDA SAHABBAN DA MUKE MAGANA A KANSU MUMINAI NE SHI KENAN.
{إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ الْمُتَّقِينَ } [التوبة: 4]

KUMA KAMAR YADDA HADISAI SUKA ZO DA BAYANIN SON ANNABI (SAW) GA WASU DAGA CIKIN SAHABBAI A BISA 'DAI'DAIKU, FIYE DA SONSA GA ALIYU (RA).


NASIRU YA CE:
" SABODA HAKA KAI NAKE JIRA DAGA NAN HAR ABUSA KAHO KABADA HIMMA WAJAN KAWO IRIN WANNAN HADISI".


AMMAR:
AI WANNAN BA WANI ABU BA NE DA HAR ZA KA KURURUTA SHI, SABODA IN ANNABI (SAW) YA YI AMFANI DA WASU LAFUZA A KAN WANI SAHABI, BA DOLE SAI AN SAMU IRIN WA'DANNAN LAFUZA SU 'DINNAN BA WASU BA, WAJEN AMFANI DA SU A KAN WANI SAHABIN DABAN, SABODA ANNABI (SAW) YANA MAGANA NE GORGODON YANAYI DA HALI, DA LOKUTA DA SABUBA.
IN HAKA NE, TO SHI NASIBI ABOKIN HAMAYYARKA A KAN ALIYU (RA) IN YA KAWO WASU HADISAI DA SUKE BAYANIN FALALAR ABUBAKAR (RA) KO UMAR (RA), SAI YA CE: KAI KUMA KA KAWO MASA IRIN HADISAN, LAFUZANSU DADAI, BA BANBANCI, INA GANIN BA ZA KA IYA BA.
DON HAKA WANNAN BA WANI ABIN A KURURUTA SHI BA NE, SABODA KAI MA BA ZA KA IYA BA, IN AN NEMI KA YI HAKAN A KAN HADISAN FALALAR SAURAN SAHABBAI. SHI YA SA MU BA ZA MU YI MAKA IRIN WANNAN BA, SABODA YA SA'BA MA HANKALI, SABODA WANNAN JAYAYYA CE TA MATSORATA.

NASIRU YA CE:
" KOMA NA MENENE GADAI ABINDA KAYI DA'AWA AKANSA"
SAI YA KAWO K'ALU – BALEN DA NASIBI YA YI MA 'DAN SHI'A KAMAR HAKA:
" AN RUWAITO IRIN WA'DANNAN HADISAN GAME DA ABUBAKAR (RA) DA UMAR (RA) DA USMAN (RA) NINKIN NA ALIYU.".

AMMAR:
KA GA A NAN SAI NA FAHIMCI NASIRU BAI FAHIMCI KALU – BALEN DA AKA JEFA MA 'DAN SHI'AN BA, SHI KUMA BAI TAMBAYA BA. DON HAKA SAI NASIRU YA YI TAMBAYA, YA NEMI A KAWO MASA IRIN HADISAN DA ANNABI (SAW) YA FA'DA A KAN ALIYU (RA)!
YA KAMATA KA SAN CEWA; IN AN CE "IRIN ABU" A HAUSA YANA 'DAUKAR MA'ANA GUDA 2; TAMKAR ABU, BABU BANBANCI TA KOWACE FISKA, SAI KUMA MAKAMANCIN ABU, WANDA YA DAIDAITA DA SHI TA WASU FISKOKI BAN DA WASU. A LARABCI NA FARKON SHI NE:
مثل
NA BIYUN KUMA:
شبه
DON HAKA IN ANCE IRIN HADISAN FALALAR ALIYU (RA) BA ANA NUFIN IRINSU A KOMAI DA KOMAI BA NE, SABODA IN HAKA AKE NUFI, AI BAI ZAMA FALALAR DA ZA AYI ALFAHARI DA ITA GA KOWA BA, SABODA AN YI TARAYYA DA SHI A CIKINTA. DON HAKA MA'ANA TA BIYU AKE NUFI, WATO AKWAI HADISAI NA FALALAR WA'DANCAN SAHABBAI WA'DANDA SUKE NUNA SUNA DA K'OLOLUWAR FALALA NINKIN NA ALIYU (RA), MA'ANA SUN YI KAMA NE DA NA ALIYU (RA) TA FISKAR BAYANIN FALALARSA.
LA'ALLA SAK'ON YA ISA.
KAR KA YARDA NASIBIN CAN YA JIKA, IN YA JIKA TO SHI MA ZAI CE KA KAWO MASA HADISAI A KAN ALIYU (RA) IRIN HADISAN FALALOLIN ABUBAKAR (RA) DA UMAR (RA) DA USMAN (RA) (IRINSU TA KOWACE FISKA), KA GA KAI MA SAI KA HA'DU DA SHI WAJEN NEMA HAR DUNIYA TA TASHI, ALHALI BA ZA KA SAMU BA.

NASIRU YA CE:
" AMMA DUBA KAGA YANDA MALAMANKU SUKE CEWA SHI MAI TSANANIN RIKON SUNNAH NE."
" MEYASA WANNAN BAKHAWARIJAN YAZAMA AHLUS-SUNNAH?".

AMMAR:
AI SUNNA TAFARKI NE, WANDA YA KARKACE DAGA TAFARKIN SHI KENAN YA FITA A SUNNA, MATUK'AR WANNAN KARKACEWA TASA TA KAI GA KARKACEWA A ABIN DA AKE KIRA "USULUS SUNNA", KUMA NASIBANCI FITA DAGA TAFARKIN SUNNA NE A BABIN "USULUS SUNNA". DON HAKA MAGANAR WANI MALAMI BA YA ISA WAJEN SHIGAR DA MUTUM CIKIN AHLUS SUNNA.
IMAMU AHMAD (R) YA CE:
طبقات الحنابلة (1/ 313)
فمن وقف على عثمان ولم يربع بعلي فهو على غير السنة يا أبا جعفر.

AL- AJURRIY(R) YA CE:
الشريعة للآجري (5/ 2540)
باب ذكر هجرة أهل البدع والأهواء:
قال محمد بن الحسين رحمه الله: ينبغي لكل من تمسك بما رسمناه في كتابنا هذا وهو كتاب الشريعة أن يهجر جميع أهل الأهواء من الخوارج والقدرية والمرجئة والجهمية , وكل من ينسب إلى المعتزلة , وجميع الروافض , وجميع النواصب , وكل من نسبه أئمة المسلمين أنه مبتدع بدعة ضلالة

DUK DA IBNU HIBBAN YA CE: YANA DA TSANANI A KAN SUNNA, TO AMMA KUMA YANA DA BIDI'A TA NASIBANCI, ALHALI IMAMU AHMAD YA CE: DUKKAN WANDA BA YA GANIN ALIYU (RA) A MATSAYIN KHALIFA NA 4 TO SHI BA AHLUS SUNNA BA NE, BA YA KAN TAFARKIN SUNNA.
HAKA SHI AL- AJURRIY YA K'IRGA DUKKAN NASIBAWA A CIKIN 'YAN BIDI'A TARE DA RAFIDHA 'YAN SHI'A. DON HAKA KAMAR YADDA 'DAN SHI'A BA AHLUS SUNNA BA NE, HAKA NASIBI BA AHLUS SUNNA BA NE. SABODA MU AHLUS SUNNA MUNA SON ALIYU (RA), KUMA MUNA GANIN GIRMANSA, DON SHI NE MAI DARAJA TA 4 BAYAN MANZON ALLAH (SAW), SA'BANIN NASIBI DA YAKE KAFIRTA SHI, KO YAKE FASIQANTAR DA SHI.


NASIRU YA CE:
" WADAN NAN AYOYI DASUKA GABA WADANDA KA KAWO BASA ALAKANTA IMANIN SAHABBAI ATATTARE KO ADUNKULANSU,".


AMMAR:
A'A, SUNA ALAK'ANTA IMANIN SAHABBAI A TATTARANSU, DUKKAN SAHABBAI MUMINAI NE.

NASIRU YA CE:
"BAZAKA IYA CEWA IDAN DAYANSU YAYI RIDDABA TO SAURANMA SAI SUNYI RIDDA BA."

AMMAR:
EH, IDAN 'DAYANSU YA YI RIDDA BA ZA A CE SAURAN MA SUN YI RIDDA BA. SAURAN KAM SUNA NAN A KAN IMANINSU, SUNA CIKIN WADANNAN AYOYIN.

NASIRU YA CE:
" ZATA IYAYIWUWA WADANSU DAGA CIKIN SAHABBAI SU IYAYIN RIDDA WADANSU KUMA SU TABBATA AKAN IMANIN DASUKE AKANSA."

AMMAR:
EH, HAKA ABIN YAKE, KO SHAKKA BABU. AMMA WA'DANDA SUKA YI RIDDA, SUNANSU KAFIRAI BA SAHABBAI BA.

NASIRU YA CE:
" KUMA DABAKINKU AHLUS-SUNNAH KUNCE ABAYAN WAFATIN ANNABI WASU DAGA CIKIN SAHABBAI SUNYI RIDDA HARMA ABUBAKAR YA YAKESU DUK KUWA DA SAUKAR WADAN CAN AYOYI DASUKA GABATA AKANSU SAI GASHI KUMA KUNYARDA DACEWA WASU DAGA CIKINSU SUNYI RIDDAH".

AMMAR:
HAKA NE, WASU DAGA CIKIN SAHABBAI SUN YI RIDDA, DAGA NAN SAI SUKA TASHI DAGA CIKIN SUNAN SAHABBAI, KUMA SUKA FITA DAGA CIKIN AYOYIN DA SUKA SAUKA A KAN SAHABBAI. SABODA DALALAR AYOYIN DALALA CE TA "UMUMI":
دلالة العموم
HUKUNCINSA BA YA TABBATA A KAN 'DAI'DAIKU, DALALAR TANA TABBATA CE A KAN GAMAYYARSU, DAGA ZARAN MUTUM 'DAYA YA FITA DAGA CIKIN GAMAYYAR TO SHI KENAN YA FITA DAGA CIKIN DALALAR, KUMA BA YA KORE CEWA; AYOYIN SUN SAUK'A NE A KAN SAHABBAI GABA 'DAYANSU.

NASIRU YA CE:
" TO ANAN KENAN KUMA KUN YARDA ABUBAKAR DA UMAR DSS SUNYI RIDDA ATARE DA WADAN CAN SAHABBAI WADANDA SUKAYI RIDDAH KO???"

AMMAR:
A'A, BA MU YARDA BA. SABODA IN KA FA'DI HAKA, TO KENAN ALIYU (RA) MA YA YI RIDDA TARE DA SU KENAN, ALHALI BABU MAI FA'DIN WANNAN SAI MUNAFUKI DAGA CIKIN 'YAN SHI'A DA NASIBAWA.

No comments:

Post a Comment