Featured post

FALALOLIN SAHABBAI

Sunday, 7 February 2016

LAFAZIN "MAULA" DA YA ZO CIKIN WASU INGANTATTUN RIWAYOYIN HADISIN "GHADEER KHUM" MA'ANARSA "MASOYI" NE BA SHUGABA BA

YA TABBATA A GHADEER KHUM ANNABI (SAW) YA CE:
"من كنت مولاه فعليُّ مولاه".

LAFAZIN "MAULA" MA'ANARSA; MASOYI.
MA'ANAR HADISIN SHI NE: ANNABI (SAW) YA CE: "DUK WANDA NA ZAMA ABIN SO GARE SHI, TO ALIYU MA ABIN SONSA NE".

* AMMA SAI 'YAN SHI'A SUKE CANZA MA'ANAR, DON HADISIN YA DACE DA SON RANSU, SAI SUKE CEWA; -WAI- LAFAZIN "MAULA" A CIKIN HADISIN, MA'ANARSA ITA CE: SHUGABA.

ALHALI, CIGABAN HADISIN YANA K'ARYATA 'YAN SHI'AN A KAN WANNAN FASSARA TASU TA CUWA - CUWA.
YA ZO A CIKIN WASU RIWAYOYIN HADISIN - DUK DA CEWA; BAI TABBATA BA - KARIN ADDU'A KAMAR HAKA:
"فمن كنت مولاه فعليُّ مولاه، اللهم وال منِ والاه، وعاد من عاداه".

WANNAR RIWAYAR BA TA INGANTA BA. FARKON NE KAWAI YA TABBATA, WATO FADINSA: " من كنت مولاه فعليُّ مولاه." SABODA WASU RIWAYOYIN DA SUKA ZO DA HAKAN WADANDA SUKA HADU HAR SUKA INGANTA.
AMMA WANNAN K'ARIN "اللهم وال منِ والاه، وعاد من عاداه". SAM BAI TABBATA BA A WAJEN MALAMAN HADISI. AMMA A WAJEN SU 'YAN SHI'A KAM YA TABBATA.

* TO, TUN DA WANNAN K'ARI NA ADDU'AN YA TABBATA A WAJENKU, SAI MU CE MUKU:
WANNAN K'ARIN ADDU'AR TANA WARWARE FASSARARKU GA HADISIN, YANA KUMA KARYATAKU A AQIDARKU TA IMAMA (WILAYAR ALI (RA) DA 'YA'YANSA), YANA KUMA K'ARA TABBATAR DA MA'ANAR DA AHLUS SUNNA SUKA FASSARA HADISIN DA ITA.
SABODA MA'ANAR ADDU'AR ITA CE:
"اللهم وال منِ والاه، وعاد من عاداه".

"YA ALLAH KA SO WANDA YA SO SHI, KA K'I (ADAWA, DA K'IYAYYA) GA WANDA YA K'I SHI".

*** KOWA YA SAN CEWA; KISHIYAR K'IYAYYA ITA CE SOYAYYA BA SHUGABANCI BA. DON HAKA ASHE DA MA HADISIN YANA MAGANA NE A KAN SOYAYYA GA ALIYU (RA) BA NA'DA SHI A MATSAYIN SHUGABA BA, KAMAR YADDA 'YAN SHI'A SUKE RAYAWA.

YA ALLAH KA YI MANA TSARI DA SHAFEWAR BASIRA, DA BIN SON RAI.

BARKANKU DA JUMA'A.

No comments:

Post a Comment