DUK WANDA YA YI AUREN MUTU'A A YANZU, YA ZAMA CIKAKKEN MAZINACI!!
AUREN MUTU'A AKWAI SA'BANI AKANSA A ZAMANIN FARKO, AMMA DAGA BAYA DUKKAN AL'UMMA SUN YI IJMA'I AKAN HARAMCINSA HAR ZUWA RANAR K'IYAMA. BABU WANDA YA SA'BA WANNAN IJMA'IN, SAI MUTANEN DA BA A LA'AKARI DA SA'BANINSU, WATO SUNE RAFIDA 'YAN BIDI'A!!!!!!!
AL- KHA'D'DABIY (R) YA CE:
قال الشيخ: تحريم نكاح المتعة كالإجماع بين المسلمين, وقد كان ذلك مباحاً في صدر الإسلام ثم حرمه في حجة الوداع, وذلك في آخر أيام رسول الله صلى الله عليه وسلم , فلم يبق اليوم فيه خلاف بين الأئمة إلاّ شيئا ذهب إليه بعض الروافض.
DUBA MA'ALIMUS SUNAN 3/ 190.
IBNU ABDILBARR (R) YA CE:
وأجمعوا على أن المتعة نكاح لا إشهاد فيه ولا ولي, وأنه نكاح إلى أجل, تقع فيه الفرقة بلا طلاق ولا ميراث بينهما. وهذا ليس حكم الزوجات في كتاب الله ولا سنة رسوله صلى الله عليه وسلم.
DUBA AL- TAMHEED 10/ 116.
IMAMUL MAZIRIY (R) YA CE:
ثبت أن نكاح المتعة كان جائزا فى أول الإسلام ، ثم ثبت أنه نسخ بما ذكر من الأحاديث فى هذا الكتاب وفى غيره ، وتقرر الإجماع على منعه، ولم يخالف فيه إلا طائفة من المبتدعة، وتعلقوا بالأحاديث الواردة فى ذلك ، وقد ذكرنا أنها منسوخة .
DUBA AL- MU'ULIM BI FAWA'IDI SAHIHI MUSLIM 2/ 130.
AL- K'ADIY IYAAD (R) YA CE:
ولا خلاف بين العلماء أن هذه المتعة كانت نكاحا إلى أجل لا ميراث فيه، وفراقها بانقضاء الأجل من غير طلاق، ووقع الاجماع على تحريمها بعد من جميع العلماء إلا الروافض. واتفق السلف على تحريمها آخرا إلا ما روى عن ابن عباس من إجازتها، وقد روى عنه أنه رجع عن ذلك، وأجمعوا على أنه متى وقع نكاح المتعة الآن أنه يفسخ أبدا قبل الدخول وبعده، إلا ما تقدم عن زفر.
DUBA IKMALUL MU'ULIM 4/ 537.
ABUL ABBAS AL- K'UR'DUBIY (R) YA CE:
وأجمع السلف والخلف على تحريمها، إلا ما روي عن ابن عباس، وروي عنه: أنه رجع عنه، وإلا الرافضة، ولا يلتفت لخلافهم ؛ إذ ليسوا على طريقة المسلمين.
DUBA AL-MUFHIM NA 4/ 93.
* DUK WANDA YA YI AUREN MUTU'A A YANZU, YA ZAMA CIKAKKEN MAZINACI!!
AUREN MUTU'A HARAMUN NE HAR ZUWA RANAR K'IYAMA!!!
BAYANI AKAN K'ARYAR DA AKA YI WA MALAMAN SUNNA GAME DA MUTU'A.
GA HAK'IK'ANIN MAGANGANUNSU AKAN MUTU'AR, SA'BANIN ABIN DA MAI RUBUTU DA YA GABATA YA NUNA; IN DA YA NUNA CEWA; - WAI – WA'DANNAN MALAMAI; DA ZAN AMBACESU, SUN K'ARAFAFA FASSARA WANNAR AYA TA SURATUN NISA'I AKAN AUREN MUTU'A, KO KUMA – WAI – SUN NUNA AYAR TA SAUK'A NE AKAN MUTU'AR. TO WALLAHI K'ARYA NE, KAMAR YADDA MAI KARATU ZAI GANI, KUMA SAI YA KOMA YA SAKE KARANTAWA DAGA CIKN LITTATAFAN KAI TSAYE, DON YA GA IRIN K'ARYA DA TADLISI DA AKA YI MUSU.
ALLAH (SWT) YA CE:
فما استمتعتم به منهن فآتوهن أجورهن فريضة ولا جناح عليكم فيما تراضيتم به من بعد الفريضة إن الله كان عليما حكيما.
1- WANNAR AYA ITA CE HUJJAR RAFIDA WAJEN HALASTA MUTU'A. TO A WAJEN TAFSIRINTA 'DABARIY YA AMBACI FASSARA GUDA 2;
1- AYAR TANA MAGANA NE AKAN AUREN HALAL.
2- AYAR TANA MAGANA NE AKAN AURE MUTU'A.
DUKANSU 'DABARIY YA AMBACESU A WAJEN TAFSIRIN AYAR.
TO WANNE DADAI??
SAI AL-'DABARIY (R) YA CE:
قال أبو جعفر: وأولى التأويلين في ذلك بالصواب، تأويل من تأوله: فما نكحتموه منهن فجامعتموه، فآتوهن أجورهن = لقيام الحجة بتحريم الله متعة النساء على غير وجه النكاح الصحيح أو الملك الصحيح على لسان رسوله صلى الله عليه وسلم.
MA'ANA: YA CE: FASSARA MAFI DACEWA DA DADAI, ITA CE FASSARAR WANDA YA FASSARA DA CEWA; ABIN DA KUKA AURA NA MATA SA'ANNAN KUKA SADU DA SU, TO KU BA SU SADAK'INSU. SABODA HUJJA TA TSAYA DAGA BAKIN MANZON ALLAH (SAW) BISA HARAMCIN YIN MUTU'A DA MATA, BA TA FISKAR INGANTACCEN AURE BA, KO INGANTACCEN MALLAKAR BAIWA.
DAGA NAN SAI YA RUWAITO HADISI DA YAKE NUNA CEWA; MA'ANAR FA'DIN ALLAH:
''فماستمتعتم''
NA CIKIN AYAR INGANTACCEN AURE YA KE NUFI, BA AUREN MUTU'A BA.
الربيع بن سبرة الجهني، عن أبيه: أن النبي صلى الله عليه وسلم قال: استمتعوا من هذه النساء = والاستمتاع عندنا يومئذ التزويج.
DAGA RABE'U BIN SABURAH AL-JUHANIY DAGA BABANSA; LALLAI MANZON ALLAH (SAW) YA CE: KU JI DA'DI DA WA'DANNAN MATAN. JIN DA'DI DA MATA A WAJENMU A WANNAN LOKACI SHI NE; AURE.
MAGANAR CEWA WASU DAGA CIKIN SAHABBAI SUN KARANTA AYAR DA K'ARIN;
الى اجل مسمى.
LALLAI SHI 'DABARIY YA YI RADDINTA, YA CE:
وأما ما روي عن أبي بن كعب وابن عباس من قراءتهما:( فما استمتعتم به منهن إلى أجل مسمى ) ، فقراءة بخلاف ما جاءت به مصاحف المسلمين. وغير جائز لأحد أن يلحق في كتاب الله تعالى شيئا لم يأت به الخبر القاطع العذر عمن لا يجوز خلافه.
MA'ANA; AMMA ABIN DA AKA RUWAITO DAGA UBAYYI 'DAN KA'AB DA IBNI ABBAS CEWA; SUNA KARANTAWA; ZUWA LOKACI AMBATACCE (SANANNE), KARATU NE DA YA SA'BA MA ABIN DA YA ZO CIKIN LITTAFIN K'UR'ANIN MUSULMAI. BA YA HALATTA GA WANI YA KAWO WANI ABU YA HA'DA DA AYA A CIKIN LITTAFIN ALLAH, WANDA BABU HADISI TABBATACCE MAI YANKE UZURI, DAGA ABIN DA BA HALATTA A SA'BA MASA BA.
TO JAMA'A KUN GA DAI YADDA 'DABARIY YA YI RADDIN WANNAN K'IRA'A SHAZZA TA SU UBAYYI DA IBNU ABBAS (RA). DON HAKA DUK WANDA YA CE: 'DABARY YA K'ARFAFA CEWA; AYAR TA SAUKA NE AKAN AUREN MUTU'A, TO YA YI K'ARYA.
AL- ZAMAKHSHARIY DUK DA CEWA MU'UTAZILI NE, GA MAGANARSA A WAJEN TAFSIRIN AYAR:
(فما استمتعتم به منهن) فما استمتعتم به من المنكوحات من جماع أو خلوة صحيحة أو عقد عليهن.
MA'ANA; ABIN DA KUKA JI DA'DI DA SHI NA ABIN AURE, NA JIMA'I, KO INGANTACCE KE'BEWA, KO 'DAURIN AURE.
SAI KUMA YA AMBACI 'DAYA FASSARAR;:
وقيل نزلت في المتعة التى كانت ثلاثة أيام حين فتح الله مكة على رسوله عليه الصلاة والسلام ثم نسخت كان الرجل ينكح المراة وقتا معلوما ليلة أو ليلتين أو أسبوعا بثوب أو غير ذلك ويقضي منها وطره ثم يسرحها سميت متعة لاستمتاعه بها أو لتمتيعه لها بما يعطيها
وعن عمر لا اوتى برجل تزوج امرأة إلى اجل الا رجمتهما بالحجارة
وعن النبي ( صلى الله عليه وسلم ) أنه أباحها ثم أصبح يقول
268 ( يا ايها الناس إني كنت أمرتكم بالاستمتاع من هذه النساء الا ان الله حرم ذلك إلى يوم القيامة )
وقيل أبيح مرتين وحرم مرتين
وعن ابن عباس هي محكمة يعني لم تنسخ وكان يقرأ ( فما استمتعتم به منهن إلى اجل مسمى ) ويروى انه رجع عن ذلك عند موته وقال اللهم إني أتوب اليك من قولي بالمتعة وقولي في الصرف
النساء
YA CE; KUMA AN CE; WAI AYAR TA SAUKA NE AKAN MUTU'AR DA TA KASANCE TSAWON KWANA 3, A LOKACIN FATHU MAKKA, SA'ANNAN SAI AKA SHAFE MUTU'AR. …
SA'ANNAN SAI YA KAWO CEWA; UMAR (RA) YA YI GARGA'DI AKAI. SAI YA KAWO HADISI; MANZON ALLAH (SAW) YA HALATTA MUTU'A, SA'ANNAN SAI YA CE: YA KU MUTANE, NA UMURCEKU DA JIN DA'DI DA WA'DANNAN MATAN, SAI DAI ALLAH YA HARAMTA HAR ZUWA RANAR K'IYAMA''.
TO KA GA KENAN BABU MAI CEWA; UMAR (RA) NE YA HARAMTA SAI JAHILI KO MAI SON RAI.
SA'ANNAN SAI YA CE; AN RUWAITO DAGA IBNU ABBAS (RA) CEWA; HUKUNCIN AYAR YANA NAN, KUMA HAR YANA KARANTAWA DA:
الى اجل مسمى.
SAI DAI ANA RUWAITOWA DAGA GARE SHI CEWA; YA DAWO DAGA WANNAR FAHIMTA LOKACIN MUTUWARSA, YA CE: YA ALLAH INA TUBA GAREKA GAME DA RA'AYINA NA MUTU'A, DA NA SARF.
TO KA GA ZAMAKHSHARIY KO KA'DAN BAI 'DAURE WA MUTU'A GINDI BA. BA WANDA ZAI FAHIMCI HAKA SAI MAI SON RAI. KUMA YA BAYYANA CEWA IBNU ABBAS YA DAWO YA BAR K'IRA'ARSA YA TUBA MA ALLAH.
AL- RAZIY YA AMBACI HUJJOJIN MASU HALASTA MUTU'A KUMA YA YI MUSU RADDI 'DAYA BAYAN 'DAYA.
GA MAGANAR DA AKA CE NAWAWI YA YIN, WANDA ASALINTA MAGANAR AL- MAZIRIY CE:
وتعلقوا بقوله تعالى فما استمتعتم به منهن فآتوهن أجورهن وفي قراءة بن مسعود فما استمتعتم به منهن إلى أجل وقراءة بن مسعود هذه شاذة لا يحتج بها قرآنا ولا خبرا ولا يلزم العمل بها.
MA'ANA; RAFIDA SUN RIK'E WANNAR AYAR AKAN MUTU'A. YA ZO A K'IRA'AR IBNU MAS'UD (RA);
الى اجل.
WANNAR K'IRA'AR SHAZZA CE. BABU MAI KAFA HUJJA DA ITA A MATSAYIN K'UR'ANI KO HADISI, KUMA BA A AIKI DA ITA.
CEWA IMAMU AHAMAD YA K'ARFAFA FASSARA AYAR DA AUREN MUTU'A A CIKIN MUSNAD NASA, WANNAR MAGANA CE DUNK'ULALLIYA, IMMA YA ZAMA YA RUWAITO DAGA WASU SAHABBAI NE, KO KUMA YA FA'DA NE DA KANSA. IN RUWAITOWA YA YI WANNAN BA YA NUNA CEWA RA'AYINSA NE KO YA K'ARFAFA, IN KUMA DA KANSA YA FA'DA TO A KAWO MANA MAGARTASA A RUBUCE TARE DA INDA TAKE???!!!
MU DAI GA ABIN DA MUKA SANI DAGA IMAMU AHMAD GAME DA AUREN MUTU'A; YA CE A RISALARSA ZUWA GA MUSADDD BIN MUSARHAD:
ولا نكاح إلا بولي وخاطب وشاهدي عدل والمتعة حرام إلى يوم القيامة.
YA CE: BABU AURE SAI DA WALIYYI DA MAI NEMA DA SHAIDU 2 ADILAI, KUMA MUTU'A HARAMUN NE HAR ZUWA RANAR K'IYAMA.
DUBA 'DABAK'ATUL HANABILA
AMMA SHI AL- JASSAS CEWA YA YI:
وأما احتجاج من احتج فيها بقوله تعالى فما استمتعتم به منهن فآتوهن أجورهن وأن في قراءة أبي إلى أجل مسمى فإنه لا يجوز إثبات الأجل في التلاوة عند أحد من المسلمين فالأجل إذا غير ثابت في القرآن ولو كان فيه ذكر الأجل لما دل أيضا على متعة النساء لأن الأجل يجوز أن يكون داخلا على المهر فيكون تقديره فما دخلتم به منهن بمهر إلى أجل مسمى فآتوهن مهورهن عند حلول الأجل
YA CE: AMMA WANDA YA KAFA HUJJA DA WANNAR AYAR, SABODA A K'IRA'AR UBAYYI (RA) AKWAI;
الى اجل مسمى.
LALLAI TABBATAR DA AJALIN A CIKIN K'IRA'AR BAI HALATTA A WAJEN WANI DAGA CIKIN MUSULMI. K'ARI ''AJALIN'' NAN BA TABBATACCE BA NE A CIKIN K'UR'ANI. KUMA DA AKWAI K'ARIN ''AJALIN'' DA BA YA NUNI AKAN MUTU'A, DOMIN AJALIN ZAI IYA ZAMA NA BA DA SADAKI NE, SAI A K'ADDARA SHI KAMAR HAKA; IDAN KUN SHIGA MUSU DA SADAKIN DA AN JINKIRTA SHI ZUWA SANANNEN AJALI, TO KU BA SU SADAKIN NASU IDAN WANNAN AJALIN (LOKACI) YA ZO.
KUMA DU YA CE:
وفي فحوى الآية من الدلالة على أن المراد النكاح دون المتعة ثلاثة أوجه.
A CIKIN MA'ANAR AYAR, AKWAI DALILI AKAN CEWA; ANA NUFIN AURE NE BA MUTU'A BA, TA FISKOKI GUDA 3:
SAI YA AMBACESU.
KUMA DU YA CE:
ولما كانت هذه المعاني موجودة في المتعة كانت في معنى الزنا ويشبه أن يكون من سماها سفاحا ذهب إلى هذا المعنى.
YA CE: SABODA SAMUN WA'DANNAN MA'ANONI A CIKIN MUTU'A, TO TA KASANCE KAMAR ZINA NE. TA YIWU SABODA WANNAN MA'ANA NE, WANDA YA KIRA MUTU'A DA SUNAN KARUWANCI, YA KIRATA DA HAKAN.
KUMA DU YA CE:
وقد روي عن جماعة من السلف أنها زنا
YA CE: HAK'IK'A AN RUWAITO DAGA MAGABATA MASU YAWA, SUNA CEWA; MUTU'A ZINA CE.
DON HAKA JAMA'A A INA AL-JASSAS YA K'ARFAFA FASSARA WANNAR AYA DA AUREN MUTU'A???!!!
BABU MAI FA'DIN HAKAN SAI WANDA BA YA FAHIMTAR MAGANGANUN MALAMAI A CIKIN LITTATAFANSU KO MAI SON ZUCIYA.
AMMA SHI BAIHAK'IY: AMMA SHI AL-BAIHAK'IY GA DUKKAN MAGANGANUN DA YA YI A BABIN MUTU'A. SAI A NUNA MANA INDA YA K'ARFAFA MAGANAR MUTU'AR:
قال الشافعى ذكر ابن مسعود الإرخاص فى نكاح المتعة ولم يوقت شيئا يدل أهو قبل خيبر أو بعدها وأشبه حديث على بن أبى طالب رضى الله عنه فى نهى النبى -صلى الله عليه وسلم- عن المتعة أن يكون والله أعلم ناسخا له.
YA CE: IMAMU SHAFI'IY YA CE: IBNU MAS'UD (RA) YA AMBACI RANGWAME GAME DA MUTU'A, AMMA BAI FA'DI WANI LOKACI DA ZAI NUNA CEWA; SHIN KAFIN YAK'IN KHAIBARA NE KO BAYANSA. AMMA TA YIWU HADISIN ALIYU (RA) NA HANIN ANNABI (SAW) AKAN MUTU'A YA KASANCE YA SHAFE RANGWAME AKAN MUTU'A DAKE CIKIN HADISIN IBNU MAS'UD (RA).
KUMA DU YA CE:
قال الشيخ رحمه الله : وهذا الذى قاله سفيان محتمل فلولا معرفة على بن أبى طالب رضى الله عنه بنسخ نكاح المتعة وأن النهى عنه كان البتة بعد الرخصة لما أنكر به على ابن عباس رضى الله عنهما والله أعلم وروى عن ابن عمر تحريمها يوم خيبر.
YA CE: ABIN DA SUFYANU('DAN UYAINA) YA FA'DA ANAN ABIN DUBAWA NE. SABODA BA DON ALIYU (RA) YA SAN AN SHAFE HALASCIN MUTU'A BA, KUMA HANI AKAI YA KASANCE NE BAYAN RANGWAME BA, DA BAI YI INKARI WA IBNU ABBAS (RA) BA. KUMA AN RUWAITO HADISIN HARAMCIN MUTU'AR A RANAR YAK'IN KHAIBARA DAGA ABDULLAHI 'DAN UMAR (RA).
KUMA DU YA CE:
قال الشيخ ثم إن رسول الله -صلى الله عليه وسلم- أذن فى نكاح المتعة زمن الفتح فتح مكة ثم حرمها إلى يوم القيامة وذلك بين فيما أخبرنا أبو طاهر الفقيه
YA CE: SA'ANNAN MANZON ALLAH (SAW) YA YI IZNIN MUTU'A A LOKACIN FATHU MAKKA, SA'ANNAN YA HARAMTATA HAR ZUWA RANAR K'IYAMA.
KUMA DU YA CE:
فقد نقل نهيه عنها بعد الإذن فيها ولم يثبت الإذن فيها بعد غزوة أوطاس فبقى تحريمها إلى الأبد والله أعلم
YA CE: HAK'IK'A AN RUWAITO HANI AKAN MUTU'A BAYAN AN YI IZNI AKANTA, IZNI AKAN MUTU'A BAI TABBATA BA BAYAN YAK'IN AU'DAAS, DON HAKA SAI HARAMCIN YA TABBATA HAR ABADA.
KUMA DU YA CE:
قال الشيخ : ونحن لا نشك فى كونهما على عهد رسول الله -صلى الله عليه وسلم- لكنا وجدناه نهى عن نكاح المتعة عام الفتح بعد الإذن فيه ثم لم نجده أذن فيه بعد النهى عنه حتى مضى لسبيله -صلى الله عليه وسلم- فكان نهى عمر بن الخطاب رضى الله عنه عن نكاح المتعة موافقا لسنة رسول الله -صلى الله عليه وسلم- فأخذنا به
YA CE: BA MA SHAKKA CEWA; MUTU'A 2, NA MATA DA NA HAJJI, SUN KASANCE A ZAMANIN MANZON ALLAH (SAW), SAI DAI MUN SAMU YA YI HANI AKAN MUTU'AR MATA A SHEKARAR FATHU MAKKA BAYAN YA YI IZNI AKAI, SA'ANNAN BA MU SAMU YA YI IZNI AKAI BA BAYAN YA YI HANIN, HAR UMAR (RA) YA BI TAFARKINSA . HANIN UMAR (RA) GAME DA MUTU'A YA DACE DA SUNNAR MANZON ALLAH (SAW), SAI MUKA YI RIK'O DA SHI.
AL- BAIDAWIY:
وقيل نزلت الآية في المتعة التي كانت ثلاثة أيام حين فتحت مكة ثم نسخت لما روي أنه ( صلى الله عليه وسلم ) أباحها ثم أصبح يقول يا أيها الناس إني كنت أمرتكم بالاستمتاع من هذه النساء ألا أن الله حرم ذلك إلى يوم القيامة وهي النكاح المؤقت بوقت معلوم سمي بها إذ الغرض منه مجرد الاستمتاع بالمرأة أو تمتيعها بما تعطي وجوزها ابن عباس رضي الله عنهما ثم رجع عنه
YA CE: AN CE; WAI WANNAR AYAR TA SAUKA NE AKAN MUTU'A DA TA KASANCE TA KWANA 3, LOKACIN FATHU MAKKA, SA'ANNAN SAI AKA SHAFE HALASCINTA, SABODA ABIN DA AKA RUWAITO; MANZON ALLAH (SAW) YA HALASTA, SAI YA WAYI GARI YANA CEWA: YA KU MUTANE; LALLAI NA UMURCEKU DA JIN DA'DI DA WA'DANNAN MATAN, KU SAURARA KU JI!! LALLAI ALLAH YA HARAMTA HAKAN HAR ZUWA RANAR K'IYAMA''.
SHI NE; AUREN 'DAN LOKACI SANANNE. AN KIRA SHI DA WANNAN SUNA NE (MUTU'A) DON MANUFARSA KAWAI; JIN DA'DIN MACE, KO KUMA DA'DA'DA MATA DA ABIN DA ZA A BATA. IBNU ABBAS (RA) YA HALASTA SA'ANNAN YA DAWO DAGA HALASCIN.
IBNU KASEER:
وقد استدل بعموم هذه الآية على نكاح المتعة، ولا شك أنه كان مشروعا في ابتداء الإسلام، ثم نسخ بعد ذلك.
YA CE: WASU SUN KAFA HUJJA DA GAMAYYAR WANNAR AYAR AKAN HALASCIN MUTU'A, AMMA BABU SHAKKA YA KASANCE AN SHAR'ANTA SHI A FARKON MUSLUNCI, SA'ANNAN SAI AKA SHAFE HALASCIN DAGA BAYA.
AL- SHAUKANIY:
وقد قال بجوازها جماعة من الروافض ولا اعتبار بأقوالهم وقد أتعب نفسه بعض المتأخرين بتكثير الكلام على هذه المسألة وتقوية ما قاله المجوزون لها وليس هذا المقام مقام بيان بطلان كلامه
وقد طولنا البحث ودفعنا الشبه الباطلة التي تمسك بها المجوزون لها في شرحنا للمنتقى
YA CE: WASU MUTANE RAFIDA SUN CE MUTU'A HALAL NE, AMMA BA A DAMUWA DA MAGANGANUNSU. HAK'IK'A WANI DAGA CIKIN 'YAN BAYA YA WAHALAR DA KANSA WAJEN YAWAITA MAGANA AKAN WANNAR MAS'ALAR DA K'ARFAFA RA'AYIN MASU HALASTAWA, AMMA NAN BA WAJEN YI MASA RADDI BA NE. HAK'IK'A MUN TSAWAITA BAHASI, MUN YI RADDIN DUKKAN 'BATATTUN SHUBUHOHIN MASU HALASTAWA A CIKIN SHARHIN ''AL-MUNTAK'A'' WATO ''NAILUL AU'DAAR''.
AL- ALUSIY:
والقول بأنها نزلت في المتعة غلط وتفسير البعض لها بذلك غير مقبول لأن نظم القرآن الكريم يأباه
YA CE: RA'AYIN CEWA; AYAR NAN TA SAUKA NE AKAN MUTU'A MUMMUNAN KUSKURE NE, KUMA FASSARAR DA WASU SUKE YI MA AYAR DA MUTU'A, SAM BA KAR'BA'B'BE BA NE, DON SIYAK'IN K'UR'ANIN BA ZAI KAR'BE SHI BA.
KUMA DU YA CE:
قوله عز من قائل : فإذا استمتعتم وهو يدل على أن المراد بالاستمتاع هو الوطء والدخول لا الاستمتاع بمعنى المتعة التي يقول بها الشيعة والقراءة التي ينقلونها عمن تقدم من الصحابة شاذة
YA CE; FA'DIN ALLAH MABUWAYI, IDAN KUN JI DA'DI, YANA NUNI NE AKAN ABIN DA AKE NUFI DA JIN DA'DIN SHI NE SADUWA TA AURE DA SHIGA DA MATA BAYAN AURE. BA YANA NUFIN JIN DA'DI NA MUTU'A BA NE, WANDA 'YAN SHI'A SUKE FA'DI, KUMA K'IRA'AR DA SUKE RUWAITOWA DAGA SAHABBAI SHAZZIYA CE. (MA'ANA; TA SA'BA MA INGANTACCIYAR K'IRA'A)
RASHEED RIDA:
وذهبت الشيعة إلى أن المراد بالآية " نكاح المتعة " : وهو نكاح المرأة إلى أجل معين كيوم أو أسبوع أو شهر مثلا ، واستدلوا على ذلك بقراءة شاذة رويت عن أبي ، وابن مسعود ، وابن عباس رضي الله عنهم وبالأخبار والآثار التي رويت في المتعة ، فأما القراءة فهي شاذة لم تثبت قرآنا ، وقد تقدم أن ما صحت فيه الرواية من مثل هذا آحادا ، فالزيادة فيه من قبيل التفسير ، وهو فهم لصاحبه ، وفهم الصحابي ليس حجة في الدين ، لا سيما إذا كان النظم والأسلوب يأباه كما هنا ، فإن المتمتع بالنكاح الموقت لا يقصد الإحصان دون المسافحة ، بل يكون قصده الأول المسافحة.
YA CE: 'YAN SHI SUN TAFI AKAN CEWA; MA'ANAR AYAR ''AUREN MUTU'A'' NE, …. KUMA SUN KAFA HUJJA NE DA K'IRA'A SHAZZIYA (MA'ANA; TA SA'BA MA INGANTACCIYAR K'IRA'A) WACCE AKA RUWAITO DAGA UBAYYI, IBNU MAS'UD, IBNU ABBAS (RA), DA KUMA HADISAI DA ATHAR DA AKA RUWAITO AKAN MUTU'A. AMMA ITA K'IRA'A SHAZZIYA CE, BA TA TABBATA K'UR'ANI BA. IRIN WANNAN IN TA TABBATA TO RUWAYA CE KA'DAITACCIYA, (WACCE BA TA TA'BA ZAMA K'UR'ANI, SABODA SHI DOLE SAI RUWAYA TA ZAMA MUTAWATIRA), KAWAI IN AN SAMU K'ARIN TAFSEERI CE, KUMA FAHIMTAR SAHABI SHI KA'DAI (WANDA YA SA'BA MA SAURAN SAHABBAI) BA YA ZAMA HUJJA A ADDINI. MUSAMMAN MA IN SIYAK'IN K'UR'ANI DA USLUBINSA BAI DACE DA SHI BA. LALLAI MAI YIN MUTU'A BA YANA NUFIN KARE KANSA NE BA, KAWAI YANA NUFIN KARUWANCI NE, KAI ASALI MA TUN FARKO MANUFARSA ITA CE; KARUWANCI.
KUMA DU YA CE:
والحاصل أن القرآن بعيد من هذا القول ، ولا دليل في هذه الآية ولا شبه دليل عليه ألبتة .
YA CE: SAKAMAKON BAYANIN NAN; LALLAI K'UR'ANI YA YI NESA DA WANNAN RA'AYI (FASSARA AYAR DA MUTU'A), BABU WANI DALILI A CIKIN AYAR KAI KO KAMA DA DALILI AKAN RA'AYIN BABU, KWATA – KWATA.
KUMA DU YA CE:
ويرى أهل السنة أن الرخصة في المتعة مرة أو مرتين يقرب من التدريج في منع الزنا منعا باتا كما وقع التدريج في تحريم الخمر ، وكلتا الفاحشتين كانت فاشية في الجاهلية
YA CE: RA'AYIN AHLUS SUNNA SHI NE; RANGWAMEN DA AKA YI AKAN MUTU'A SAU 1, KO SAU 2, YA YI KAMA DA MATAKAI WAJEN HANA ZINA HANAWA NA GABA 'DAYA, KAMAR YADDA HAKAN YA FARU WAJEN HARAMTA GIYA, SABODA DUKKAN ALFASHA GUDA 2, SUN WATSU A ZAMANIN JAHILIYYA.
SUYU'DIY KUMA A CIKIN DURRUL MANTHUR, RUWAYOYI YA TARA KAWAI BA SHI RA'AYI KO 'DAYA CIKIN LITTAFIN SHI YASA YAKE CIKE DA HADISAI MASU RAUNI, HAR DA NA K'ARYA. SHI YA SA RAFIDA SUKA YAWAITA KWASO KOWANE IRIN HADISI DAGA CIKINSA.
TO, JAMA'A KUN GANI A BAYA WANI RAFIDI YA NUNA CEWA; WA'DANNAN MALAMAN SUN K'ARFAFA FASSARAR AYAR SURATUN NISA'I DA AUREN MUTU'A, TO JAMA'A K'ARYA YAKE YI. SHI YA SA NA KAWO WA'DANNAN MAGANGANUN NA WA'DANNAN MALAMAI, SABODA K'ARYAR DA AKA MUSU CEWA SUNA FASSARA WANNAR AYA DA HALASCIN AUREN MUTU'A, KO KUMA –WAI- AYAR TA SAUKA NE AKAN HALASCIN MUTU'AR. GA SHI DAI MUN GA YADDA KOWANNE DAGA CIKINSU YA YI KACA-KACA DA AUREN MUTU'A. KUMA DUKKANSU SUN NUNA CEWA; BA DADAI BA NE FASSARA AYAR DA AUREN MUTU'A, KUMA BA DON AUREN MUTU'A AKA SAUKAR DA ITA BA, KUMA K'IRA'AR SU IBNU ABBAS (RA) SHAZZIYA CE TA SA'BA MA K'IRA'A MUTAWATIRA, DON HAKA KO KA'DAN BABU HUJJA A CIKINTA.
DON HAKA LALLAI WANNAR AYAR BABU DALILI GA WANDA YA HALATTA MUTU'A A CIKINTA.
DA MA SHI AUREN MUTU'A YA TABBATA NE A HADISI BA A K'UR'ANI BA. SABODA A FARKON MUSLUNCI BUK'ATA TA SA MANZON ALLAH (SAW) YA HALALTA MUSU MUTU'A, AMMA DAGA BAYA YA HANA YIN MUTU'AR YA HARAMTA TA HAR ZUWA RANAR K'IYAMA, DON HAKA SAYYIDINA UMAR (RA) MA A ZAMANINSA YA K'ARFAFA HARAMCIN DA MANZON ALLAH (SAW) YA YI.
JAMA'A MUN DAI FAHIMCI CEWA RAFIDA BA SU DA WANI DALILI NA ALK'UR'ANI AKAN MUTU'A, SAI K'IRA'A SHAZZA (MA'ANA; TA SA'BA MA INGANTACCIYAR K'IRA'A). SABODA HAKA DUK WANDA YA CE; AKWAI DALILI A CIKIN K'UR'ANI AKAN MUTU'A, YA ZAMA CIKAKKEN MAK'ARYACI, SABODA JAHILCI, KO SON ZUCIYA DA SON RAI.
WA YA HARAMTA AUREN MUTU'A????
1- على بن أبى طالب رضى الله عنه : أن رسول الله -صلى الله عليه وسلم- نهى عن متعة النساء يوم خيبر وعن أكل لحوم الحمر الإنسية.
AN RUWAITO DAGA ALIYU (RA); LALLAI MANZON ALLAH (SAW) YA YI HANI AKAN MUTU'A DA MATA A RANAR YAK'IN KHAIBARA, DA CIN NAMAN JAKUNAN GIDA.
BUKHARI DA MUSLIM.
2- عن الحسن وعبد الله ابنى محمد بن على عن أبيهما : أن عليا رضى الله عنه قيل له إن ابن عباس رضى الله عنهما لا يرى بمتعة النساء بأسا. فقال : إن رسول الله -صلى الله عليه وسلم- نهى عنها يوم خيبر وعن لحوم الحمر الإنسية.
AN RUWAITO DAGA HASSAN DA ABDULLAHI 'YA'YAN MUH'D 'DAN ALIYU DAGA BABANSU YA CE; LALLAI ALIYU (RA) AN CE MASA; GA IBNU ABBAS (RA) YANA GANIN BABU LAIFI AKAN MUTU'A DA MATA. SAI YA CE: LALLAI MANZON ALLAH (SAW) YA YI HANI AKANTA (MUTU'A DA MATA) A RANAR YAK'IN KHAIBARA, DA CIN NAMAN JAKUNAN GIDA.
BUKHARI DA MUSLIM.
3- سالم بن عبد الله : أن رجلا سأل عبد الله بن عمر رضى الله عنهما عن المتعة فقال : حرام قال فإن فلانا يقول فيها فقال : والله لقد علم أن رسول الله -صلى الله عليه وسلم- حرمها يوم خيبر وما كنا مسافحين.
AN RUWAITO DAGA SALIM 'DAN ABDILLAHI; WANI MUTUM YA TAMBAYI ABDALLAHI 'DAN UMAR (RA) GAME DA MUTU'A, SAI YA CE: HARAMUN NE. SAI YA CE: AI WANE YANA FA'DIN HALACCINTA. SAI YA CE: NA RANTSE DA ALLAH YA SANI CEWA; MANZON ALLAH (SAW) YA HARAMTATA A RANAR YAK'IN KHAIBARA, DON HAKA MU BA MASU HARKA DA DADURO BA NE (KARUWAI).
DUBA SUNANUL KUBARA NA AL-BAIHAK'IY , A BABIN AUREN MUTU'A.
4- عن الربيع بن سبرة الجهنى عن أبيه سبرة رضى الله عنه أنه قال : أذن رسول الله -صلى الله عليه وسلم- بالمتعة فانطلقت أنا ورجل إلى امرأة من بنى عامر كأنها بكرة عيطاء فعرضنا عليها أنفسنا فقالت : ما تعطينى فقلت : ردائى وقال صاحبى : ردائى وكان رداء صاحبى أجود من ردائى وكنت أشب منه فإذا نظرت إلى رداء صاحبى أعجبها وإذا نظرت إلى أعجبتها ثم قالت : أنت ورداؤك تكفينى فكنت معها ثلاثا ثم إن رسول الله -صلى الله عليه وسلم- قال :« من كان عنده شىء من هذه النساء التى يتمتع بهن فليخل سبيلها ».
AN RUWAITO DAGA RABE'U 'DAN SABURA AL-JUHANIY DAGA BABANSA SABURA (RA) YA CE; MANZON ALLAH (SAW) YA YI IZNIN MUTU'A, SAI NA TAFI NI DA WANI MUTUM ZUWA WAJEN WATA MATA DAGA BANI AMIR, KAI KA CE DAK'WALWAR BUDURWA CE, SAI MUKA NUNA MATA KANMU, SAI TA CE; ME ZAKU BANI, SAI NA CE: MAYAFINA, SAI ABOKINA YA CE: MAYAFINA. AMMA MAYAFIN ABOKIN NAWA YA FI NAWA KYAU, AMMA NI NA FI SHI SAMARTAKA. TO IDAN TA DUBA MAYAFIN ABOKINA SAI YA BIRGETA, IDAN KUMA TA DUBENI SAI IN BIRGETA, SAI TA CE MINI: KAI DA MAYAFINKA KUN ISHENI, SAI NA ZAUNA TARE DA ITA TSAWON KWANA 3. SA'ANNAN SAI MANZON ALLAH YA CE: DUK WANDA AKWAI IRIN WA'DANNAN MATA DA YAKE MUTU'A DASU, TO YA RABU DA ITA.
MUSLIM.
5- الربيع بن سبرة عن أبيه عن جده قال : أمرنا رسول الله -صلى الله عليه وسلم- بالمتعة عام الفتح حين دخلنا مكة ثم لم نخرج منها حتى نهانا عنه.
DAGA SABURA (RA) YA CE: MANZON ALLAH (SAW) YA UMURCEMU DA MUTU'A A SHEKARAR FATHU MAKKA A LOKACIN DA MUKA SHIGA MAKKAN, SA'ANNAN BA MU FITA DAGA MAKKAN BA HAR SAI DA YA HANAMU GAME DA MUTU'AN.
DUBA SUNANUL KUBURA NA AL-BAIHAK'IY , A BABIN AUREN MUTU'A.
6- الربيع بن سبرة عن أبيه : أن رسول الله -صلى الله عليه وسلم- نهى عن المتعة وقال :« إنها حرام من يومكم هذا إلى يوم القيامة ومن كان أعطى شيئا فلا يأخذه ».
DAGA SABURA (RA); LALLAI MANZON ALLAH (SAW) YA HANAMU MUTU'A, KUMA YA CE: TA HARAMTA DAGA YAU HAR RANAR K'IYAMA. DUK WANDA YA BA DA WANI ABU TO KAR YA KAR'BA.
MUSLIM
7- الربيع بن سبرة عن أبيه رضى الله عنه قال : رأيت رسول الله -صلى الله عليه وسلم- قائما بين الركن والباب وهو يقول :« يا أيها الناس إنى كنت أذنت لكم فى الاستمتاع ألا وإن الله حرمها إلى يوم القيامة فمن كان عنده منهن شىء فليخل سبيلها ولا تأخذوا مما آتيتموهن شيئا ».
DAGA SABURA (RA) YA CE: NA GA MANZON ALLAH (SAW) YANA TSAYE A TSAKANIN RUKUNI (HAJARUL ASWAD) DA KOFAN KA'ABA, YANA CEWA: YA KU MUTANE! LALLAI NA YI MUKU IZNIN MUTU'A, TO KU SAURARA KU JI; LALLAI ALLAH YA HARAMTATA HAR ZUWA RANAR K'IYAMA, TO DUK WANDA YAKE TARE DA WATA MACE TA MUTU'A, TO YA RABU DA ITA, KUMA KAR KU KAR'BI WANI ABU DA KUKA BASU.
MUSLIM.
8- عن إياس بن سلمة بن الأكوع عن أبيه رضى الله عنه قال : رخص رسول الله -صلى الله عليه وسلم- فى متعة النساء عام أوطاس ثلاثة أيام ثم نهى عنها بعد.
DAGA IYAS BIN SALAMA BIN AL-AKWA'A, DAGA BABANSA (RA) YA CE: MANZON ALLAH (SAW) YA YI RANGWAME GAME DA MUTU'AR MATA A SHEKARAR YAK'IN AU'DAS, TSAWON KWANA 3, SA'ANNAN YA YI HANI AKAI DAGA BAYA.
MUSLIM.
9- عن أبى جمرة قال سمعت ابن عباس وسئل عن متعة النساء فرخص فيها فقال له مولى له : إنما كان ذاك وفى النساء قلة والحال شديد ، فقال ابن عباس : نعم.
DAGA ABU JAMRA YA CE: NA JI IBNU ABBAS AN TAMBAYE SHI GAME DA MUTU'AR MATA, SAI YA YI RANGWAME AKAI, SAI WANI MAULANSA YA CE MASA: AN YI RANGWAME AKAN HAKAN NE A LOKACIN MATA 'YAN KA'DAN NE, KUMA ANA YANAYI NA TSANANI. SAI IBNU YA CE: EH, HAKA NE.
BUKHARI.
10- عن أبى ذر قال : إنما أحلت لنا أصحاب رسول الله -صلى الله عليه وسلم- متعة النساء ثلاثة أيام ثم نهى عنها رسول الله -صلى الله عليه وسلم-.
AN RUWAITO DAGA ABU ZARR (RA) YA CE: MU SAHABBAN MANZON ALLAH (SAW) KAWAI AN HALASTA MANA MUTU'A DA MATA NE, TSAWON KWANA 3, SA'ANNAN SAI MANZON ALLAH (SAW) YA YI HANI AKANTA.
DUBA SUNANUL KUBURA NA AL-BAIHAK'IY , A BABIN AUREN MUTU'A.
JAMA'A GA SHI K'ARARA MANZON ALLAH (SAW) SHI NE YA HARAMTA MUTU'A, BAYAN YA YI MUSU RANGWAME AKANTA HAR SAU 2, NA FARKO YA HALATTA KAFIN YAK'IN KHAIBARA, SAI HARAMTA A RANAR KHAIBARAN. SA'ANNAN SABODA BUK'ATA, YA SAKE HALATTAWA A RANAR FATHU MAKKA, SA'ANNAN BAYAN KWANA 3, SAI YA HARAMTA, TUN DAGA RANAR HAR TASHIN K'IYAMA. KUMA WANNAN SHEKARA TA FATHU MAKKA ITA CE; SHEKARAR DA AKA YI YAK'IN AU'DAAS. DON HAKA MUTU'A AN HALATTA SAU 2, AN KUMA HANA SAU 2.
KUMA DUKA A WAJEN YAK'UK'UWA NE, BA A GARIN MADINA BA. ABIN DA YAKE NUNA CEWA RANGWAME YAYI MUSU SABODA BUK'ATA, SA'ANNAN DAGA K'ARSHE KUMA YA HARAMTA HAR RANAR K'IYAMA.
DON HAKA HAR K'IYAMA TA TSAYA MUTU'A HARAMUN NE.
TO SAI A ZAMANIN KHALIFA UMAR (RA) AKA SAMU WASU DA BA SU SAN AN YI WANNAN HANIN BA, SAI KHALIFA UMAR (RA) YA SAKE JADDADA HANIN DA MANZON ALLAH (SAW) YA YI. KUMA DUKKAN SAHABBAI BABU WANI DA YA FITO YA SA'BA MASA. TUN DAGA NAN KOWA CIKIN AL'UMMAR MUSULMAI SUKA SAN HARAMCIN MUTU'A.
WA'DANDA KUMA AKA RUWAITO HALASCINTA DAGA GARESU, AN SAMU SUN DAWO SUN BAR WANNAN RA'AYIN NASU.
DON HAKA, SA'BANI AKAN HALASCIN MUTU'A YA KASANCE NE A FARKON WANNAN AL'UMMA, WASU SUN YI TARAJU'I DAGA BAYA KAMAR SU IBNU ABBAS (RA). AMMA DAGA NAN DUKKAN AL'UMMA SUKA YI IJMA'I AKAN HARAMCIN MUTU'A, BABU WANDA YA SA'BA SAI RAFIDA 'YAN SHI'A WA'DANDA BA A DAMUWA DA SA'BANINSU. SABODA IN KA DUBA HUJJOJINSU ZAKA SAMUSU KAMAR HAKA:
1- K'IRA'A SHAZZIYA, WACCE TA SA'BA MA K'IRA'A MUTAWATIRA, BA A KAFA HUJJA DA ITA AKAN ABIN DA DALILINSA YA TABBATA A FILI.
2- HADISAN K'ARYA.
3- HADISAI MASU RAUNI.
4- RUWAYOYI MASU RAUNI KO SHAZZAI DAGA MAGABATA.
5- RIWAYOYI NA RA'AYOYIN MAGABATA KAFIN SU DAWO SU BAR RA'AYIN.
6- SAI KUMA MAGANGANUN MALAMAI DA BA SU FAHIMCE SU BA, KAMAR YADDA MUKA GA WANNAN RAFIDI MAI RUBUTUN DA YA GABATA, YA KAFA HUJJA DA MAGANGANUN MALAMAI, ALHALI MAGANGANUNSU SUN YI HANUN RIGA DA RA'AYINSA, SABODA SHI BAI FAHIMCI MAGANGANUN BA, KO KUMA A WANI LITTAFI NA WANI JAHILIN YA SAMU BAYANAI, SHI KUMA BA TARE DA YA KOMA CIKIN LITTATAFAN YA TABBATAR BA YA ZO YA KAWO MANA SU, SAI GA SHI ABIN DA YAKE FA'DA DABAN, ABIN DA MAGANGANUN MALAMAN KUMA SUKE NUFI DABAN.
DON HAKA DUK ABIN DA SUKE KAWOWA RU'DU NE, DA K'ARERAYI DA HAYANIYA, DA NUFIN SU KAWO SHAKKA WA AL'UMMAR MUSULMI A CIKIN AL'AMARIN ADDININSU.
GA MAGANGANUN MALAMAI DA KE TABBATAR DA IJMA'IN WANNAN AL'UMMA TA ANNABI MUH'D (SAW) AKAN HARAMCIN MUTU'A.
AUREN MUTU'A AKWAI SA'BANI AKANSA A ZAMANIN FARKO, AMMA DAGA BAYA DUKKAN AL'UMMA SUN YI IJMA'I AKAN HARAMCINSA HAR ZUWA RANAR K'IYAMA. BABU WANDA YA SA'BA WANNAN IJMA'IN, SAI MUTANEN DA BA A LA'AKARI DA SA'BANINSU, WATO SUNE RAFIDA 'YAN BIDI'A!!!!!!!
AL- KHA'D'DABIY (R) YA CE:
قال الشيخ: تحريم نكاح المتعة كالإجماع بين المسلمين, وقد كان ذلك مباحاً في صدر الإسلام ثم حرمه في حجة الوداع, وذلك في آخر أيام رسول الله صلى الله عليه وسلم , فلم يبق اليوم فيه خلاف بين الأئمة إلاّ شيئا ذهب إليه بعض الروافض.
DUBA MA'ALIMUS SUNAN 3/ 190.
IBNU ABDILBARR (R) YA CE:
وأجمعوا على أن المتعة نكاح لا إشهاد فيه ولا ولي, وأنه نكاح إلى أجل, تقع فيه الفرقة بلا طلاق ولا ميراث بينهما. وهذا ليس حكم الزوجات في كتاب الله ولا سنة رسوله صلى الله عليه وسلم.
DUBA AL- TAMHEED 10/ 116.
IMAMUL MAZIRIY (R) YA CE:
ثبت أن نكاح المتعة كان جائزا فى أول الإسلام ، ثم ثبت أنه نسخ بما ذكر من الأحاديث فى هذا الكتاب وفى غيره ، وتقرر الإجماع على منعه، ولم يخالف فيه إلا طائفة من المبتدعة، وتعلقوا بالأحاديث الواردة فى ذلك ، وقد ذكرنا أنها منسوخة .
DUBA AL- MU'ULIM BI FAWA'IDI SAHIHI MUSLIM 2/ 130.
AL- K'ADIY IYAAD (R) YA CE:
ولا خلاف بين العلماء أن هذه المتعة كانت نكاحا إلى أجل لا ميراث فيه، وفراقها بانقضاء الأجل من غير طلاق، ووقع الاجماع على تحريمها بعد من جميع العلماء إلا الروافض. واتفق السلف على تحريمها آخرا إلا ما روى عن ابن عباس من إجازتها، وقد روى عنه أنه رجع عن ذلك، وأجمعوا على أنه متى وقع نكاح المتعة الآن أنه يفسخ أبدا قبل الدخول وبعده، إلا ما تقدم عن زفر.
DUBA IKMALUL MU'ULIM 4/ 537.
ABUL ABBAS AL- K'UR'DUBIY (R) YA CE:
وأجمع السلف والخلف على تحريمها، إلا ما روي عن ابن عباس، وروي عنه: أنه رجع عنه، وإلا الرافضة، ولا يلتفت لخلافهم ؛ إذ ليسوا على طريقة المسلمين.
DUBA AL-MUFHIM NA 4/ 93.
* DUK WANDA YA YI AUREN MUTU'A A YANZU, YA ZAMA CIKAKKEN MAZINACI!!
No comments:
Post a Comment