ASSALAMU ALAIKUM 'YAN UWANA DA ABOKAI, BARKANKU DA SHAN RUWA, DA FATAN AN SHA RUWA LAFIYA. ALLAH YA KARBA MANA, YA BA MU KARFIN GUIWA A KAN KOKARIN YAWAITA AIYUKAN IBADA A WANNAN WATA MAI ALBARKA, IBADU NA AZUMI, SALLAR DARE (TARAWIHI), KARATUN AL- QUR'ANI, SADAKA DA CIYARWA, DA ADDU'O'I DA NEMAN GAFARAN ZUNUBAI, DA SADA ZUMUNCI DA KUMA ZUWA AIKIN UMRA GA WANDA YA SAMU IKO.
A YAU TAMBAYA NAKE DA ITA ZUWA GA 'YAN UWANA DA ABOKAINA NA WANNAN DANDALI A MUNASABAR SHIGOWAN WANNAN WATA NA YAWAITA IBADU DA AIYUKAN ALHERI, WATO WATAN RAMADHANA.
TAMBAYAR ITA CE:
* ME KA SANI GAME DA ABUBUWAN DA MABIYA ADDININ SHI'A, WATO RAFIADHA 'YAN SHI'A SUKE AIKATAWA NA ABIN SUKA SA'BA WA SAURAN MUSULMAI A KANSA A WANNAN WATA, NA IBADU, TUN DAGA KAN HANYAR TABBATAR DA SHIGOWAN WATAN HAR ZUWA IBADU DA AKE YI A CIKINSA NA SALON AZUMI DA SAURAN AIYUKAN IBADA, HAR ZUWA KARSHENSA?
* KAWAI KA AMBATA MANA ABIN DA KA SANI NA ABIN DA 'YAN SHI'A SUKA SA'BA WA SAURAN MUSULMAI A KANSA A GAME DA WATAN RAMADHANA DA IBADU DA AKE YI A CIKINSA.
MANUFAR WANNAR TAMBAYA ITA CE; MUNA SO NE MU AUNA TAZARA DA RATA (GAP) DA YAKE TSAKANIN 'YAN SHI'A DA SAURAN MUSULMAI A CIKIN RUKUNIN AZUMI WANDA YAKE 'DAYA NE DAGA CIKIN RUKUNNAN MUSLUNCI GUDA BIYAR.
No comments:
Post a Comment