BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
IBNUL K'AYYIM (R) YA CE:
وليست حاجة الأرواح قط إلى شيء أعظم منها إلى معرفة باريها وفاطرها ومحبته وذكره والابتهاج به، وطلب الوسيلة إليه والزلفى عنده، ولا سبيل إلى هذا إلا بمعرفة أوصافه وأسمائه، فكلما كان العبد بها أعلم كان بالله أعرف وله أطلب وإليه أقرب، وكلما كان لها أنكر كان بالله أجهل واليه أكره ومنه أبعد
ALLAH MA'DAUKAKIN SARKI YANA SAMAN DUKKAN HALITTUNSA.
AN RUWAITO TARIN MAGANGANUN MAGABATA; SAHABBAI DA TABI'AI DA SUKE NUNA IMANINSU DA CEWA; ALLAH YANA SAMAN DUKKAN HALITTUNSA.
MAGANGANUN SAHABBAI:
(1) ABUBAKAR AL- SIDDEK' (RA):
A LAKACIN DA ANNABI (SAW) YA RASU SAI ABUBAKAR (RA) YA CE:
"من كان يعبد محمدًا فإنه قد مات، ومن كان يعبد الذي في السماء فإنه حي لا يموت".
DUK WANDA YA KASANCE YANA BAUTA WA MUHAMMADU NE, TO SHI FA YA MUTU. DUK KUMA WANDA YAKE BAUTA MA WANDA YAKE SAMA NE, TO SHI RAYAYYE NE BA ZAI MUTU BA.
AL- ZAHBIY YA CE:
أخرجه هكذا الدارمي بإسناد صحيح
DUBA KITABUL ARSHI NA ZAHABIY 2/ 125.
(2) UMARU BINUL KHA'D'DAB (RA):
عن عمر أنه مر بعجوز فاستو قفته فوقف يحدثها فقال له رجل: "يا أمير المؤمنين حبست الناس على هذه العجوز" فقال: "ويلك أتدري ما هي؟، هذه امرأة سمع الله شكواها من فوق سبع سموات، هذه خولة التي أنزل الله فيها {قد سمع الله قول التي تجادلك في زوجها}".
AN RUWAITO DAGA UMAR (RA); YA WUCE WATA TSOHUWA SAI TA TSAYAR DA SHI, SAI YA TSAYA YANA MATA MAGANA. SAI WANI MUTUM YA CE: YA AMIRUL MUMININA, KA TSAYAR DA MUTANE SABODA WANNAR TSOHUWAR. SAI YA CE: KAITONKA! SHIN KA SAN WACECE ITA? WANNAR ITA CE MATAR DA ALLAH YA JI KOKAWANTA TUN DAGA SAMAN SAMMAI BAKWAI (7). WANNAR ITA CE KHAULATU, WACCE ALLAH YA SAUK'AR DA AYA GAME DA ITA:
{قد سمع الله قول التي تجادلك في زوجها}
DUBA KITABUL ARSH NA ZAHABIY 2/ 128.
(3) ALIYU BIN ABI 'DALIB (RA):
A CIKIN HU'DUBAR ALIYU (RA) TA K'ARSHE YA CE:
الحمد لله الذي دنا في علوه وناء في دنوه لا يبلغ شيء مكانه ولا يمتنع عليه شيء أراده
GODIYA TA TABBATA GA ALLAH WANDA YAKE KUSA A CIKIN 'DAUKAKARSA, KUMA YA YI NISA A CIKIN KUSACINSA. BABU WANI ABU DA ZAI ISA WAJENSA, KUMA BABU WANI ABU DA ZAI HANA ABIN DA YA YI NUFINSA.
DUBA AL- RADDU ALAL JAHAMIYYA NA DARIMIY, 48.
(4) IBNU MAS'UD (RA) YA CE:
"ما بين السماء القصوى والكرسي خمسمائة عام، وبين الكرسي والماء كذلك، والعرش فوق الماء والله فوق العرش، ولا يخفى عليه شيء من أعمالكم".
TSAKANIN SAMA MAFI NISA (TA 7) DA ALKURSIYYI TAFIYAN SHEKARA 500 NE. TSAKANIN ALKURSIYYI DA RUWA MA HAKA NE. AL'ARSHI KUMA YANA SAMAN RUWAN. ALLAH KUMA YANA SAMAN AL'ARSHIN, AMMA BABU WANI ABU NA AIYUKANKU DA YAKE 'BUYA MASA.
DUBA KITABUL ARSH NA ZAHABIY 2/ 129. KUMA YA CE:
رواه اللالكائي، والبيهقي، بإسناد صحيح عنه.
(5) IBNU ABBAS (RA):
YA SHIGA WAJEN A'ISHA (RA) A LOKACIN RASUWARTA. SAI YA CE:
كنت أحب نساء رسول الله إلى رسول الله ولم يكن رسول الله يحب إلا طيبا وانزل الله براءتك من فوق سبع سموات جاء بها الروح الأمين فأصبح ليس مسجد من مساجد الله تعالى يذكر فيه الله إلا وهي تتلى فيه آناء الليل والنهار
KIN KASANCE MAFI SOYUWAN MATAN MANZON ALLAH (SAW) A GARE SHI, KUMA MANZON ALLAH (SAW) BA YA SON WANI ABU SAI KYAKKYAWA. KUMA ALLAH YA SAUK'AR DA KU'BUTANKI DAGA ALFASHA DAGA SAMAN SAMMAI BAKWAI (7), MALA'IKA JIBRILU AMINTACCE (AS) NE YA ZO DA ITA. SAI AKA WAYI GARI, BABU WANI MASALLACI DAGA CIKIN MASALLATAN ALLAH DA AKE AMBATONSA A CIKINSA FACE ANA KARANTA AYOYIN A CIKINSA DARE DA RANA.
DUBA AL- RADDU ALAL JAHAMIYYA NA DARIMIY, 47.
(6) ABDULLAHI BIN RAWAHA (RA) YA CE:
شهدت بأن وعد الله حق ... وأن النار مثوى الكافرينا
وأن العرش فوق الماء طاف ... وفوق العرش رب العالمينا
وتحمله ملائكة كرام ... ملآئكة الإله مسومينا
A CIKI YA CE:
وفوق العرش رب العالمينا
A SAMAN AL'ARSHI AKWAI UBANGIJIN HALITTU.
(7) ZAINAB MATAR ANNABI (SAW):
ANAS (RA) YA CE:
قال فكانت زينب تفخر على أزواج النبي صلى الله عليه وسلم تقول زوجكن أهاليكن وزوجني الله تعالى من فوق سبع سموات
ZAINAB TA KASANCE TANA ALFAHARI WA MATAN ANNABI (SAW), TAKE CEWA; IYAYENKU NE SUKA AURAD DA KU, NI KUMA ALLAH NE YA AURAD DA NI TUN DAGA SAMAN SAMMAI BAKWAI (7).
BUKHARI NE YA RUWAITO SHI.
WA'DANNAN MAGANGANU SUNA TABBATAR DA CEWA; SAHABBAN ANNABI (SAW) SUN YI IMANIN CEWA; ALLAH YANA SAMAN AL'ARSHINSA NE.
No comments:
Post a Comment